Editor

9513 Posts
Ya kamata gwamnatoci su kafa masana’antun koya sana’o’i a gidajen yari – Doguwa

Ya kamata gwamnatoci su kafa masana’antun koya sana’o’i a gidajen yari – Doguwa

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Muƙaddashin Kwanturola na gidan gyara jalin da ke Bauchi, Musa Dauda Doguwa ya buƙaci gwamnatocin lardin arewacin ƙasar nan da su kafa ma’aikatu na koya wa matasa sana’o’i da zummar rage gararambar su. Doguwa ya bayyana cewar, ya yi ayyuka a gidajen gyara hali daban-daban da ke sassan ƙasar nan, waɗanda suka haɗa da na Kano, Jigawa, Neja, Kaduna, Katsina, da sauransu. Amma bai taɓa iske gidan maza da yake da tarin matasa kamar na Bauchi ba. Doguwa ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan da kwamitin da ke…
Read More
Kamfanin ‘Google’ zai zuba Dala biliyan guda don bunƙasa fasahar zamani a Nijeriya

Kamfanin ‘Google’ zai zuba Dala biliyan guda don bunƙasa fasahar zamani a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin Google ya bayyana cewa, zai ƙara zuba jarin Dalar Amurka har biliyan guda domin ganin an bunkasa fasahar zamani ta yanar gizo a Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka. Kamfanin ya bayyana cewa, wannan yunƙurin nasa na zuba jari zai sa a samu rangwamen farashin yanar gizo da kaso 21. Sannan zai ninka ƙarfin yanar gizo sau biyar a ƙasar Nijeriya. Wannan bayani ya fito daga bakin Manajan Daraktan Google na Afirka, Nitin Gajria. A lokacin taron Google na Afirka na farko wanda aka gudanar a Larabar nan da ta wuce. A cewar sa, Kamfanin Google a…
Read More
Waye ba ya busa wiwi?

Waye ba ya busa wiwi?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ba mamaki wannan tambaya ta ‘waye ba ya zuƙar tabar wiwi?’ ta zama bambaraƙwai don masu sha sun san kansu, haka nan kuma waɗanda ba sa busawa za su ce ina ruwan biri da gada. Kazalika ba na nufin jam'in cewa duk mutane su na zuƙar wiwi ko akasarin jama'a na hulɗa da ita ba, a'a taken ALKIBLAR wannan makon ne da ya shafi mutane da yawan gaske. Tun ban fara rubuce-rubuce ba na ke cin a na cewa wane ya cake ko wane sai da kori aljanu kafin ya fito idanun sa wuri-wuri ya yi…
Read More
Batun Naira biliyan 13.3 da aka ware don aikin ‘yan sandan al’umma

Batun Naira biliyan 13.3 da aka ware don aikin ‘yan sandan al’umma

Sanarwar da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kan cewa, ya amince da ware Naira biliyan 13.3, don fara aikin 'yan sanda na al'umma a cikin jihohi 36 na ƙasar da Babban Birnin Tarayya Abuja yana nuna jajircewar shugaban wajen tabbatar da cewa, ya yi duk abin da ya yi alƙawarin zai aiwatar kafin ya bar gadon mulki. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a wani taron bita na kwanaki biyu na duba ayyukan Ministoci wanda aka shirya don tantance ci gaban da aka samu don cimma muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba,…
Read More
Aikin MC ilimi ne mai zaman kansa a aikin jarida – MC Bahaushe

Aikin MC ilimi ne mai zaman kansa a aikin jarida – MC Bahaushe

Daga UMAR GARBA, a Katsina Kabir Sa'idu Bahaushe matashi ne da ya yi fice a fannoni daban daban, kama daga mai shiryawa da gabatar da shirye shirye a gidan radiyo, da kuma yin sharhi da rubuce-rubuce a jaridu da mujallu. Haka nan ma Kabir Sa'idu Bahaushe ya yi fice a harkar gabatar da tarurruka a gidan biki ko taron ƙungiyoyi ko kuma taron marubuta ko na mawaƙa gami da taron siyasa. Manhaja ta tattauna da Bahaushe a kan batutuwan da su ka shafi aikin shi na gabatar da tarurruka watau MC da alaƙarsa da marubuta da ƙungiyoyi har ma da…
Read More
Rashin sha’awar iyali da dalilansu (4)

Rashin sha’awar iyali da dalilansu (4)

Daga BILKISU YUSUF ALI Daga makon da ya gabata mu na tattaunawa ne kan sha’awa tsakanin ma’aurata da abin da yake ɗauke ta ko ya sa ta yi rauni. Daga yanda mutane suke bibiya tare da yin tambayoyi wannan ya nuna rashin sha’awa wata gagarumar matsala ce da ta addabi al’ummarmu. Kamar yadda muka fa]a a baya yau za mu kawo hanyoyin magance wannan matsalar a mataki na farko kafin mataki na gaba na shan magani. Sakewa:Yana da kyau yayin kusantar juna ma’aurata su sake da junansu sakewar gaske. Ya kasance sun mallakawa junansu kawunansu tsakaninsu ba tsoro ko shayi…
Read More
A karon farko za a fara gasar daddalla mari a Nijeriya

A karon farko za a fara gasar daddalla mari a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Masu shirya wata sabuwar gasa da za a fara a karon farko a Nijeriya, sun ce a fito a fafata domin za a fara gasar mare-mare cikin watan Oktoba a Nijeriya. Babban Daraktan kamfanin tsara wasannin na TKK Sports, Abdulrahman Orosanya ne ya bayyana haka, ranar Juma’a a Legas. Ya ƙara da cewa, ba a dai sa ranar da za a fara ba, amma dai cikin watan Oktoba za a fara, kuma a cikin Disamba za a yi wasannin ƙarshe na cin kofuka. Orosanya ya ce, an ƙirƙiro wannan wasan daddalla mari a ƙasar Rasha, amma…
Read More
Hidimar da Charles Henry Robinson ya yi wa harshen Hausa

Hidimar da Charles Henry Robinson ya yi wa harshen Hausa

Duk ƙasar da ta ke son mallakar ƙwaryar Afrika, dole sai ta mallaki Bahaushe – Mista Johnson Daga JAAFAR JAAFAR  Shekaru 130 da su ka gabata, a ranar Juma’a, 26 ga Yuni, 1891, John Alfred Robinson, wani Bature malami a Christ’s College ta Cambridge, ya mutu a garin Lokoja. Wannan Bature, wanda ya fahimci Hausa daidai gwargwado, ya na cikin mutanen da su ka fara fahimtar amfanin nazarin harshen Hausa. Watanni kaɗan bayan rasuwar wannan Bature, sai wasu Turawa su ka haɗu a wani otal da ya ke a Birnin London mai suna Charing Cross Hotel don tattauna yadda za…
Read More
Masarautar Katsina da Katsinawa

Masarautar Katsina da Katsinawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Katsina babbar masarauta ce kuma mai daɗaɗɗen tarihi a Ƙasar Hausa. Ta na ɗaya daga cikin asalin garuruwan yankin qasar ta Hausa. Kafin zamowarta wannan babban birni da a yau ya zama helikwatar Jihar Katsina sannan kuma fadar masarautar Katsina, ta taɓa zama a wani gari da yake da tazarar kimanin kilomita 32 daga Katsinan yau. Sunan wannan gari shi ne ‘Durɓi ta Kusheyi’. Wannan gari shi ne asalin fadar mulkin daular Katsina. Wannan masarauta cike take da ababen tarihi, a cikin wancan garin na Durɓi, akwai wannan kuka tana nan, akwai wani Dutse da su…
Read More
Ruwan jiki (2)

Ruwan jiki (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilimintu, kuma ku san yadda jikinku ke aiki. Bayani ya zo a satin da ya gabata game da ruwan jikin ɗan Adam. Na faɗi guraren da ake samun ruwan jiki, da gwargwadon yawan ruwan jiki da ake samu a jikin ɗan Adam. Na faɗa cewa akwai ruwa a cikin ƙwayoyin halitta, wato kowacce ƙwayar halitta ta jikin ɗan Adam. Amma…
Read More