Babaji

5684 Posts

Kofin Duniya: Belgium ta yi waje da Amurka a zagayen ‘yan 16

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasa Folarin Balogun ya koma cikin tawagar 'yan wasan Amurka bayan Shugaba Donald Trump ya tsoma baki akan al'amarinsa na wasan da ya gabata. Saidai Balogun ya gaza taimaka wa ƙasar kai wa zagayen wasan dab da na kusa da na ƙarshe a karon farko tun a 2002 a gasar Kofin Duniyar da ke gudana a Nahiyar Amurka bayan da Belgium ta lallasa ta da ci 4 da 1. Tawagar Amurka ta fara gasar ne cike da ƙwarin-gwiwar kasancewarta a gida inda ta samu tikitin hayewa zagaye na gaba kai-tsaye daga na rukunin-rukuni.…
Read More

Mafarkin Ronaldo na lashe Kofin Duniya ya zo ƙarshe bayan Sifaniya ta doke Portugal a zagayen ‘yan 16

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasa Mikel Merino da aka sako daga baya ya yi nasarar zura ƙwallo a raga ana gab da kammala wasa inda aka tashi Sifaniya ta doke Portugal ta su Cristiano Ronaldo da ci 1 da 0 a gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka. Wannan al'amari ya kawo ƙarshen fatan zakaran ɗan ƙwallon duniya, Ronaldo zuwa ƙarshe bayan gumurzu da ƙasarsa a gasar har sau shida a tarihinsa. Haka kuma nasarar da Sifaniya ta samu dama ce ta cigaba da aiki tuƙuru wajen ganin ta lashe kofin a matsayinta…
Read More

PFIPC ba ta da asusu a CBN – Akanta Janar ya ci karo da Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A daiadai lokacin da 'yan Nijeriya ke cigaba da tsokaci akan badaƙalar hukumar bogi ta PFIPC, Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OACF) ya ce hukumar ba ta da asusun aiki a Babban Bankin Nijeriya (CBN), don haka ba a taɓa tura mata ko sisi daga kuɗaɗen gwamnati ba. Daraktan hulɗa da jama'a na ofishin a wata sanarwa, Bawa Mokwa, ya bayana cewa an dai fara yunƙurin buɗe asusun ne, amma ba a kai ga kammala shi ba saboda ba a cika wasu sharuɗɗa da ake buƙata ba. Ya ƙara da cewa, Adeniyi Adeyemi ya…
Read More

Badaƙalar PFIPC: AYCF ta nesanta kanta da kalaman goyon bayan Gbajabiamila

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Mashawartan Arewa na Matasa AYCF, ta nesanta kanta daga saƙon da aka wallafa da ke zargin ta fitar da wata sanarwa mai ƙunshe da goyon ga Shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila akan al'amarin hukumar bogi ta PFIPC. A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta, Alhaji Yerima Shettima a ranar Lahadi, AYCF ta musanta hannu a fitar da kowane saƙo akan al'amarin. A cewar sanarwar, wasiƙar da ake yaɗawa ba daga AYCF yake ba don haka al'umma su ƙaurace mata tare da saƙon da ke ciki. Sanarwar ta bayyana…
Read More

Kaduna: Hare-haren ‘yan bindiga sun yi ajalin manoma 9 da garkuwa da mutane da dama

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar ne 'yan bindiga sun halaka kimanin manoma guda tara da kuma yin awon-gaba da wasu da dama a wasu hare-haren gonaki da ke a bayan garin ƙauyen Kakangi a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna. Rahotanni sun bayyana maharan sun buɗe wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta a lokacin da suka riske su suna bakin aiki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara, kafin daga bisani suka tafi da wasu da ba a tantance adadinsu ba. Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3 na yamma…
Read More

Sabbin bayanai sun alaƙanta ofishin sakataren gwamnati da daraktan hukumar bogi yayin da Majalisar Dattawa za ta yi zama akan kasafin biliyan N1.3

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu sababbin bayanai sun bjiro da ke nuna Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ya amince da Daraktan Hukumar Shugaban Ƙasa ta Ciyar da Lamuran Harkokin Waje Gaba (PFIPC) ta bogi, Mista Adeniyi Adeyemi, ya halarci Taron Canada-Africa Fintech (CAFS) a watan Agustan 2025. Wannan al'amari na zuwa ne a daidai lokacin da ake cece-kuce ciki har da allah-wadai daga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma neman a bayyana haƙiƙanin gaskiyar al'amarin daga ɓangaren Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Adalci akan Albarkatun Ƙasa (SERAP) akan ware Naira biliyan 1.3 ga hukumar bogin…
Read More

Idan Tinubu ya lashe zaɓen 2027 sai na halaka ɗansa Seyi, inji DJ Chicken

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen mai nishaɗantarwa a Soshiyal Mediya da ake kira da DJ Chicken ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta sakamakon furta wasu kalamai masu hatsari akan sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a karo na biyu. DJ'n ya yi haka ne a wani bidiyo ta shafinsa na Instagram duk da cewa daga bisani an goge shi, inda ya yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ba zai lashe zaɓen da ke tafe ba. Sannan, ya kuma yi barazana mai tayar da hankali akan ɗan Shugaban Ƙasar, Seyi Tinubu, inda aka ga yadda ɗan mediyar ya yi shiga…
Read More

Kofin Duniya: Bellingham ya zura biyu yayin da ‘yan Ingila 10 suka doke Mexico

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Ingila ta sha da ƙyar a hannun Mexico a zagayen 'yan 16 na gasar Kofin Duniya na 2026 yayin da aka kammala wasan tsakaninsu da 3 da 2, lamarin da ya ba ta damar zuwa zagayen wasan dab da na kusa da na ƙarshe. Ɗan wasan Real Madrid, Jude Bellingham ne ya zura ƙwallo biyu, wanda hakan ya ba ƙasar damar jan ragamar wasan, kana daga bisani Julian Quinones na Mexico ya goge ɗaya. Bayan an sallami Jarell Quansah daga wasan ne sai Ingila ta samu damar ƙara ta uku a bugun daga…
Read More

Kofin Duniya: Norway ta kai wasan dab da na kusa da na ƙarshe a karon farko bayan doke Brazil

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Norway ta shiga sahun ƙasashen da suka kafa tarihi a harkar wasan ƙwallon ƙafa na zamani bayan doke Brazil da ci 2 da 1 a wasan zagayen 'yan 16 na gasar Kofin Duniya na 2026. Wannan shi ne karo na farko da Norway ta kai zagayen wasan dab da na kusa da na ƙarshe a gasar, kamar yadda ita ma Brazil wannan shi ne karon farko da aka cire ta zagayen tun a 1990. Da fari, ɗan wasa Bruno Gumarães ne ya zubar da bugun fenarati bayan dogon lokaci da sashen binciken VAR…
Read More

‘Ku nuna mana hujjar’: Gwamnatin Tinubu ta yi watsi da iƙirarin kashe tiriliyan N8 da ba su cikin wajen kasafin kuɗi

Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa ta kashe sama da Naira tiriliyan 8 a wajen kasafin kuɗin shekarar 2026, tana mai cewa babu wata hujja da ke tabbatar da hakan. Ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce an yi wa kalaman wakilin Asusun Lamuni na Duniya (IMF) a Najeriya, Christian Ebeke, mummunar fassara. Oyedele ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da abin da ake kira “kasafin kuɗi na ɓoye”, yana mai jaddada cewa duk kuɗaɗen gwamnati ana kashe su ne bisa dokokin kasafin kuɗi da majalisar tarayya ta amince da su.…
Read More