02
Jul
Daga JAMIL GULMA a Kebbi Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba motoci guda 110 na taki da kuma ton ɗari na irin zamani ga manoma 120,000 don noman damina na wannan shekara. Wannan yana daga cikin kudurran gwamna Malam Nasir Idris na haɓaka harkokin noma da kuma sauƙaƙa wa al'umma rage tsadar rayuwa musamman abinci a jihar. Gwamna Malam Nasir Idris ya bayyana cewa sanin kowa ne kashi tamanin na al'ummar jihar Kebbi sun dogara ne da noma saboda haka sun fi buƙatar tallafi a wannan ɓangaren, an kuma yi tsarin rabon takin da irin ta yadda zai isa ga ainihin…
