25
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu tagwayen girgizar ƙasa sun yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 80 da jikkata 700 da ɗoriya a Venezuela, kamar yadda shugabar riƙo ta ƙasar ta bayyana a ranar Alhamis, lamarin da ya jefa jama’ar yankin cikin firgici. Akan haka ne jami'an hukumomi da sauran al'ummar ƙasar suka riƙa hawa abubuwa masu tsawo da nufin neman tsira daga iftila'in, lamarin da ya sa jagoran, Delcy Rodriguez ta ayyana dokar ta-ɓaci. Girgizar ƙasar masu faɗin murabba'i 7.2 da 7.5 sun auku ne a waje guda na Venezuela a ranar Laraba, kamar ya yadda hukumomi suka…
