Babaji

5684 Posts

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta dakatar da soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da aiwatar da hukuncin Mai Shari'a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ya umarci a soke rajistar Jam'iyyar ADC da wasu jam’iyyu guda huɗu. A cikin taƙaitaccen hukunci da ta yanke, kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana matakin a matsayin “babban raini ga tsarin shari’a,” tana mai cewa alkalin kotun ya yi watsi da umarnin da kotun ɗaukaka ƙarar ta bayar tun da farko. Sauran jam’iyyun da hukuncin ya shafa sune Action People's Party (APP), Action Alliance (AA), Zenith Labour Party (ZLP) da Accord Party (AP). Kotun ta ce,…
Read More

‘Yan sanda sun tarwatsa mafakar ‘yan bindiga, sun kama mai ciki da ke musu girki a Abuja

Rundunar 'Yan Sanda a Abuja, ta kama wata mata mai juna biyu, Hauwa Shafi'u da wasu mutum uku da ake zargi da alaƙa da masu garkuwa da mutane a yankin Byazhin da ke kusa da birnin tarayyar. Kwamishinan 'Yan Sandan Birnin Tarayya, Ahmed Sanusi, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani samame da jami'an tsaro suka kai a maɓoyar 'yan bindiga a ranar 11 ga watan Yuni, inda aka kashe wasu daga cikin masu laifin tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su. A cewarsa, Hauwa Shafiu na samar wa ƙungiyar kayan masarufi tare da…
Read More

An zargi sojojin sama da lakaɗa wa direba dukan da ya yi ajalinsa bisa ɓata motarsu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani direban motar kasuwa ƙirar bus mai suna Joseph Okpe ya rasu bayan zargin jami'an sojin sama da casa shi akan wani rikici yayin ƙaramin cinkoson ababen hawa da ya haɗa da motarsu a hanyar Oshodi zuwa Apapa da ke Jihar Legas. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Mayu, 2026 kamar yadda bayanan ƙorafin da aka yi a Babbar Kotun Abuja suka bayyana, inda aka zargi cewa marigayin mai shekaru 43 ya daku ne bayan tsama akan damejin wata mota ta jami'an sojojin. A cewar takardar ƙorafin…
Read More

Za a gurfanar da Sadiya Farouk a ranar 2 ga Yuli yayin da kotu ta ƙi amince wa soke izinin kama ta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da buƙatar tsohuwar Ministar Harkokin Jin-ƙai, Sadiya Umar Farouq, na soke izinin kamu da kotun ta bayar a kanta. Kotun ƙarƙashin Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie, ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2026, bayan lauyan tsohuwar ministar ya nemi a soke umarnin kama ta da kotun ta bayar tun farko. Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati ta EFCC na tuhumar Sadiya Farouq tare da wasu mutum biyu, Bashir Nura Alkali da Sani Nafiu Mohammed kan zargin haɗa baki wajen aikata laifi, amfani da ofis…
Read More

‘Yan sanda sun ƙaddamar da kama motoci masu rufaffun allunan lambobi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda ta fara gudanar da atisayen kama motoci masu ɗauke da allunan lambobi da aka rufe da waɗanda suka ƙoƙe da marasa rajista. Hukumar ta ɗauki matakin ne domin inganta lamuran tsaro da tabbatar da rajistar ababen hawa da kuma shafe ayyukan ta'addanci a sassan Nijeriya. Hakan na zuwa ne bisa umarnin Sufeto Janar na rundunar, Tunji Disu da nufin ƙarfafa tsaon al'umma da kuma hana miyagu amfani da ababen hawa da ba su da rajista ko asali. Tuni dai rassan rundunar na jihohi suka fara aiwatar da umarnin, inda suka gargaɗi…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da adaidaita sahu masu amfani da lantarki 10,000 a Agusta, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta shirya ƙaddamar da adaidaita sahu masu amfani da lantarki guda 10,000 a matsayin wani shiri na sauƙaƙe lamuran sufuri a Nijeriya da kuma bunƙasa harkokin fannin. Hukumar kula da Ci-gaban Shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC) ne za ta jagoranci raba adaidaitan a watan Agustan 2026 domin amfanin al'umma a shiyyar da ma wasu sassa. Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya bayyana haka yayin wani zama da Ƙungiyar 'Yan Sufuri masu goyon bayan Tinubu/Shettima a 2027 a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce shugaban ƙasar ya amince da maimaita irin shirin a…
Read More

Hukuncin soke rijistar ADC barazana ce ga dimukraɗiyya, inji jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar ADC ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja bisa hukuncin umarnin soke rijistarta, tana mai bayyana hukuncin a matsayin wata babbar barazana ga dimukraɗiyya da zaman lafiyar siyasa a ƙasar nan. Haka kuma, ADC Jam’iyyar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na cire ta daga cikin jam’iyyun da za su shiga zaɓe zai iya haifar da mummunan rikicin siyasa. Jam'iyyar ta bayyana haka ne ta bakin Sakataren Yaɗa Labaranta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi a wata takarda, inda ta ce wannan hukunci ya ƙara tabbatar da yadda jam’iyya…
Read More

An benca Lamin Yamal a wasan Sifaniya na farko a gasar Kofin Duniya na 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ake cigaba da fafatawa tsakanin ƙasashe daban-daban a Gasar Kofin Duniya na 2026 a satin farkon, ƙasar Sifaniya da ake ganin ka iya lashe kofin, za ta kara da Cape Verde ba tare da ɗan wasa Lamin Yamal ba a sahun farko. Wannan shi ne karo na farko da Cape Verde ta samu damar shiga gasar tun bayan zama mambar Hukumar Ƙwallon ta Duniya (FIFA) a shekarar 1985. Kasar ita ce ƙaramar ƙasa ta uku da taɓa nasarar hayewa zagayen shiga gasar ta fuskar yawan jama'a, inda Curacao da Iceland ne sauran…
Read More

Basaraken Kwara ya rasu a hannun ‘yan bindiga bayan neman fansar miliyan N21

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An tabbatar da rasuwar Mai Garin ƙauyen Olayinka da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara, Oba Salman Olatunji Aweda bayan waɗanda suka sace shi sun nemi a biya fansar Naira miliyan 21, sabbin babura guda biyu da jarkan fetur a matsayin sharuɗɗan sako shi. A cewar jaridar ShaharaReporters, an tabbatar da labarin ne a wani saƙon faifan murya daga wani mamban kwamitin da aka samar don ƙoƙarin ceton marigayin sarkin. A saƙon, mamban ya sanar da abin alhinin ne ga 'yan garin Olayinka, ina ya bayyana rashin basaraken a matsayin "ikon Allah" duk…
Read More

Kotu ta sake ɗage shari’ar zargin rashawa akan El-Rufa’i

Babbar Kotun Tarayya a Kaduna, ta sake ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i zuwa ranar 28 ga watan Yuni, 2026. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) na tuhumar El-Rufai da laifukan amfani da ofis ba daidai ba, damfara da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati a lokacin da yake gwamnan jihar. A zaman kotun da aka gudanar ranar Litinin kamar yadda rahotanni suka bayyanar, El-Rufai ya halarta tare da jami’an ICPC, DSS da kuma ’yan sanda. Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa an fitar da wasu kuɗaɗen gwamnati domin aiwatar da ayyuka da ba a…
Read More