20
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Tsofaffin ɗalibai mata ta Makarantar St. Louis (SLOGA) reshen Abuja, tare da tsofaffin ɗalibai, iyaye da masu ruwa da tsaki na St Louis da ke Kano, ta nemi a gudanar da cikakken bincike akan ainihin abin da ya sabbaba mutuwar ɗaliba Maimuna Salisu Yaro mai shekaru 14, wadda aka fi sani ida Nihal. A wata sanarwa da SLOGA ta aike wa NewsPointNigeria a yau Asabar, ƙungiyar ta ce ta samu labarin mutuwar ɗaliban cikin alhini bayan ababen da suka faru a makarantar a ranar 13 ga watan Yuni, 2026. Ƙungiyar ta bayyana ɗalibar…
