Babaji

4788 Posts

Kwanan nan ‘yan jarida za su fara raka sojoji fagen fama, inji Ministan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar gabatar da wani sabon shiri da zai ba 'yan jarida damar raka jami'an tsaro yayin ƙaddamar da wasu atisaye a matsayin wani ɓangare na inganta lamuran tsaro a Nijeriya. Za a yi haka ne da nufin bunƙasa fahimtar yanayin ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta ga 'yan ƙasa da kuma tabbatar da tsare gaskiya da adalci akan harkokin sojoji. Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa ya bayyana a a ranar Alhamis yayin babban taron tsaron ƙasa da Ƙungiyar 'Yan jaridar ta Ƙasa (NUJ) ta shirya a Abuja. Ministan, wanda mai…
Read More

Ku daina ba ‘yan ta’adda satar amsa – Ministan Labarai ga gidajen jaridun Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al'umma, Mohammed Idris ya yi kira ga gidajen jaridun Nijeriya da su daina buɗe sirri ga 'yan ta'adda da wasu ɓarayi, yana mai cewa cigaba da yawaita yaɗa ayyukansu dama ce ga masu son watsa fargaba da rashin zaman lafiya acikin al'umma. Mohammed Idris ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin babban taro akan tsaro da Ƙungiyar 'Yan jarida ta Ƙasa (NUJ) ta shirya da haɗin-gwiwar Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), inda ya ce wajibi ne 'yan jarida su samar da daidaito akan 'yancin yaɗa…
Read More

Ana sa ran farashin fetur ya faɗi yayin da ɗanyen mai ya koma ƙasa da Dala 75

Farashin ɗanyen mai ya ragu ƙasa da Dala 75 a ranar Alhamis, karo na farko tun watan Maris, 2026, wato mafi ƙanƙantarsa tun lokacin da aka fara yaƙin Iran, bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Amurka da Iran ta ƙara hasashen samun wadataccen mai a kasuwannin duniya. Farashin man Brent ya sauka da dala 1.59, wato kashi 2%, zuwa dala 77.96 kan kowace ganga, yayin da man West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya ragu da dala 1.83, wato kashi 2.38%, zuwa dala 74.96 kan kowace ganga. Faduwar farashin ya biyo bayan yarjejeniyar mai matakai 14 da Amurka da Iran…
Read More

‘Yan sanda sun kama mai yi wa ‘yan bindiga safarar kayan shayi a Kwara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Kwara, ta kam wani da zargi da yi wa 'yan bindiga safara kayan aiki a Ilorin, inda ta ƙwato wasu ababe da ake zargin yana kai wa ƙungiyoyin ta'addanci da ke ayyukasu a dazuka da wasu yankuna a jihar. An yi nasarar haka ne bayan yaɗa wata jita-jitar kai harin 'yan bindiga, lamarin da ya tilasta wa ɗaruruwan iyaye zuwa ɗauko 'ya'yansu a makarantu. A wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar a ranar Alhamis, ya ce sashen yaƙi da miyagun laifuka (VCRU) ne ya yi…
Read More

2027: NDC ta ɗaga wa Obi da Kwankwaso ƙafa kan rantsuwar fita daga jam’iyyar

Jam’iyyar adawa ta NDC, ta ƙara fayyace sabuwar dokar da ta ƙaddamar kan hana ‘yan takararta sauya sheƙa bayan sun ci zaɓe, inda ta tabbatar cewa ba za ta tilasta wa ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sanya hannu kan rantsuwar ba. Tun farko dai jam’iyyar ta bayyana cewa duk mai neman takara a ƙarƙashinta dole ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar kin sauya sheka, wadda za ta iya sa a ƙwace kujerar duk wanda ya fice daga jam’iyyar bayan samun nasara a zaɓe. Sai dai a sabon bayani da Sakataren jam’iyyar na ƙasa,…
Read More

Kano: Masu ruwa da tsaki sun yi zama kan allura rigakafi a Bichi

Kwamitin Masu Ruwa da Tsaki na Ƙaramar Hukumar Bichi sun ƙaddamar da wani muhimmin zama domin nemo mafita kan giɓin da aka samu game da allurar rigakafin yara daga shekarar 2019 zuwa yau, wanda aka yi wa shirin laƙabi da BCU; BIG CATCH-UP. Kansilan Mazaɓar Fagolo kuma shugaban Majalisar Kansiloli kuma Ciyaman na Kwamitin Kula da Cigaban da aka Samu a mazaɓu dake Jihar Kano na yankin, Alhaji Habibu Musa Habibu, ya ce, shirin ingantaccen yunƙuri ne duba ga muhimmacin yara. Kuma kula da lafiyar yara babban al'amari ne da ya shafi kowa. Shugaban majalisar kansulolin, wanda ya wakilici shugaban…
Read More

UAE ta zama ƙasar Larabawa ta farko da ta haramta wa ‘yan ƙasa da shekera 15 amfani da Soshiyal Mediya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta kafa tarihi a matsayin ƙasar Larabawa ta farko da ta haramta wa yara 'yan ƙasa da shekaru 15 amfani da kafafen Soshiyal Mediya a ƙasar. Haka kuma, ba ta iyakance waɗanda iyayensu suka amince musu amfani da kafafen ba. A ranar Alhamis ne majalisar zartarwar ƙasar ta ayyana haka, lamarin da ya sa ta zama ƙasar Gabas ta Tsakiya ta farko da ta yi wa yara katanga da kafafen bisa la'akari da zama barazana ga tarbiyya, shiga tattaunawar da ba su cancanta ba, yawan ɓata lokaci wajen kallon…
Read More

Real Madrid ta tabbatar da sayen Konate daga Liverpool

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta kammala ɗaukar ɗan ƙasar Faransar nan, Ibrahim Konate daga kulob ɗin Liverpool a hukumance. Ɗan wasan bayan ya rattaɓa hannun ne wa Madrid akan yarjejeniyar shekara huɗu sakamakon ƙarewa da kwantaraginsa ya yi a Merseyside. A ranar Alhamis Real Madrid ta Laliga ta sanar da cewa, ɗan wasan mai shekaru 27 ya zama mallakinta har zuwa bazarar shekarar 2030, inda ake fatan kammala sauya sheƙar ɗan wasan bayan kammala gasar Kofin Duniya. Konate ya koma Liverpool ne daga ƙungiyar RB Leipzig a shekarar 2021. Ya kuma bar…
Read More

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar NBC, ta jaddada haramcin tara akan gidajen yaɗa labarai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta yi watsi da yunƙurin Hukumar kula da Harkokin Gidajen Yaɗa Labarai (NBC) na neman soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya na haramta mata tilasta biyan tara ga wasu gidajen rediyo da talabijin. A wani hukuncin na tawagar alƙalai da aka gudanar a ranar Laraba, kotun ta yi watsi da buƙatar NBC, inda ta bayyana hakan a matsayin "kuskuren tsari" da "rashin fahimtar doka". Da take gudanar da hukuncin, Mai Shari'a Jane Inyang ta bayyana cewa yayin da shari'ar a Babbar Kotun Tarayya ake yin ta tsakanin tawagar amintattun 'yancin…
Read More

Bayan doguwar shari’a, kotun Birtaniya ta wanke zargin cin hanci akan Diezani

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An gano cewa tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke ba ta hannu a laifuka shida masu alaƙa da cin hanci da aka danganta su da ita, lamarin da ya kawo ƙarshen shari’ar rashawa da ake yi akanta. Alƙalan Kotun Southwark Crown da ke Birnin Landon ne suka yanke hukuncin bayan shafe sama da sa’o’i 46 suna tattaunawa akan shari’ar, inda suka same ta da rashin laifi akan dukkan tuhume-tuhumen da ake mata. Diezani, wacce ta riƙe muƙamin ministar man fetur daga 2010 zuwa 2015 a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ta musanta…
Read More