17
Jun
Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya musanta rahotannin da ke cewa ya zargi wasu da ƙirƙirasa hannun sanatoci a yayin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya. A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Oshiomhole ya ce an karkatar da kalamansa da ya yi a wani shiri na talabijin, lamarin da ya haifar da fahimtar cewa ya yi zargin an ƙirƙiri sa hannun wasu sanatoci. Ya ce “Zargin cewa na ce an ƙirƙiri sa hannun sanatoci ba daidai ba ne kuma ya saba da abin da na faɗa.” Tsohon gwamnan ya…
