Babaji

4789 Posts

Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da adaidaita sahu masu amfani da lantarki 10,000 a Agusta, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta shirya ƙaddamar da adaidaita sahu masu amfani da lantarki guda 10,000 a matsayin wani shiri na sauƙaƙe lamuran sufuri a Nijeriya da kuma bunƙasa harkokin fannin. Hukumar kula da Ci-gaban Shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC) ne za ta jagoranci raba adaidaitan a watan Agustan 2026 domin amfanin al'umma a shiyyar da ma wasu sassa. Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya bayyana haka yayin wani zama da Ƙungiyar 'Yan Sufuri masu goyon bayan Tinubu/Shettima a 2027 a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce shugaban ƙasar ya amince da maimaita irin shirin a…
Read More

Hukuncin soke rijistar ADC barazana ce ga dimukraɗiyya, inji jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar ADC ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja bisa hukuncin umarnin soke rijistarta, tana mai bayyana hukuncin a matsayin wata babbar barazana ga dimukraɗiyya da zaman lafiyar siyasa a ƙasar nan. Haka kuma, ADC Jam’iyyar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na cire ta daga cikin jam’iyyun da za su shiga zaɓe zai iya haifar da mummunan rikicin siyasa. Jam'iyyar ta bayyana haka ne ta bakin Sakataren Yaɗa Labaranta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi a wata takarda, inda ta ce wannan hukunci ya ƙara tabbatar da yadda jam’iyya…
Read More

An benca Lamin Yamal a wasan Sifaniya na farko a gasar Kofin Duniya na 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ake cigaba da fafatawa tsakanin ƙasashe daban-daban a Gasar Kofin Duniya na 2026 a satin farkon, ƙasar Sifaniya da ake ganin ka iya lashe kofin, za ta kara da Cape Verde ba tare da ɗan wasa Lamin Yamal ba a sahun farko. Wannan shi ne karo na farko da Cape Verde ta samu damar shiga gasar tun bayan zama mambar Hukumar Ƙwallon ta Duniya (FIFA) a shekarar 1985. Kasar ita ce ƙaramar ƙasa ta uku da taɓa nasarar hayewa zagayen shiga gasar ta fuskar yawan jama'a, inda Curacao da Iceland ne sauran…
Read More

Basaraken Kwara ya rasu a hannun ‘yan bindiga bayan neman fansar miliyan N21

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An tabbatar da rasuwar Mai Garin ƙauyen Olayinka da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara, Oba Salman Olatunji Aweda bayan waɗanda suka sace shi sun nemi a biya fansar Naira miliyan 21, sabbin babura guda biyu da jarkan fetur a matsayin sharuɗɗan sako shi. A cewar jaridar ShaharaReporters, an tabbatar da labarin ne a wani saƙon faifan murya daga wani mamban kwamitin da aka samar don ƙoƙarin ceton marigayin sarkin. A saƙon, mamban ya sanar da abin alhinin ne ga 'yan garin Olayinka, ina ya bayyana rashin basaraken a matsayin "ikon Allah" duk…
Read More

Kotu ta sake ɗage shari’ar zargin rashawa akan El-Rufa’i

Babbar Kotun Tarayya a Kaduna, ta sake ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i zuwa ranar 28 ga watan Yuni, 2026. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) na tuhumar El-Rufai da laifukan amfani da ofis ba daidai ba, damfara da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati a lokacin da yake gwamnan jihar. A zaman kotun da aka gudanar ranar Litinin kamar yadda rahotanni suka bayyanar, El-Rufai ya halarta tare da jami’an ICPC, DSS da kuma ’yan sanda. Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa an fitar da wasu kuɗaɗen gwamnati domin aiwatar da ayyuka da ba a…
Read More

ADC ta sanar da Amaechi a matsayin mataimakin takarar Atiku a zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar ADC ta sanar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, shi ne wanda zai yi wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar mataimaki yayin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ke cigaba da kusantowa. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa kai domin ƙarfafa matsayinsu a fagen siyasar Nijeriya musamman bisa la'akari da yadda fagen ke cigaba da ɗaukar ɗumi. Ana kallon tikitin Atiku da Amaechi a matsayin wani gagarumin yunƙuri na samar da zaɓin shugabanci daban ga ‘yan…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci da a soke rajistar jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyu huɗu bisa gazawar cika sharuɗɗan dokar ƙasa akan jam'iyyun siyasa a Nijeriya. Mai Shari'a Peter Lifu, wanda ya yi hukuncin, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, da ta soke rajistar jam'iyyun tunda sun gaza samun kaso 25 na ƙuri'a a babban zaɓen da ya gabata domin biyayya da hukuncin doka. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa, jam'iyyu biyar da suka haɗa ADC, Accord, AA, APP, da kuma ZLP ne kotun ta…
Read More

Gwamnatin Tarayya fara shari’ar mutum 400 da ake zargi da ta’addanci a kotun Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutane 400 da ake zargin su da hannu a ayyukan ta'addanci. An gudanar da shari'o'in ne a ɗakin kotuna da Babbar Kotun da ke Abuja. Tawagar masu gabatar da shari'ar ta ƙunshi Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi a matsayin shugaba da kuma Daraktan Harkokin Shari'o'in Gwamnatin Tarayya, Rotimi Oyedepo (SAN). Ana tuhumar mutane 400 ne da hannu a laifukan da aka alaƙanta da ta'addanci, taimakawa da ɗaukar nauyin ayyukan tayar da ƙayar baya. Babban Mai Shari'ar kotun, John Tsoho, ta tawagar alƙalai…
Read More

NBA ta koka kan cinkoson fursunoni a sabon gidan yarin Gombe

Daga ABUBAKAR a BOLARI Gombe Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta nuna damuwa kan tsananin cunkoson da ake fama da shi a Gidan Gyaran Hali na Gombe, inda ta bayyana cewa gidan yarin da aka gina domin ɗaukar fursunoni 390 kacal, a halin yanzu yake ɗauke da sama da fursunoni 1,000. NBA ta bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ta kai gidan gyaran halin a matsayin wani ɓangare na ayyukan bikin Makon Lauyoyi na shekarar 2026, inda ta kuma samu nasarar tabbatar da sakin fursunoni tara. Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala ziyarar, Shugaban…
Read More

Alhazan Legas 1,600 sun isa gida daga Makkah lafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Alhazan Jihar Legas guda 1,600 da suka je aikin Hajjin 2026 ne suka koma gida lafiya daga Saudiyya bayan kammala ibadar. Dawowar tawagar ƙarshe na mahajjata 187 a ranar Asabar ya nuna kammala aikin hajjin na 2026. Da yake ganawa da manema labarai a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Amirul Hajji kuma Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Legas, Ibrahim Layode ya ce gudanar da ibadar babbar nasar ce ga Jihar Legas. Ya kuma alaƙanta nasarar da gudanar da ayyukan mahajjatan bisa kyakkyawan tsari a ƙasa Mai Tsarki, yana mai cewa…
Read More