Babaji

4795 Posts

Kotu ta sake ɗage shari’ar zargin rashawa akan El-Rufa’i

Babbar Kotun Tarayya a Kaduna, ta sake ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i zuwa ranar 28 ga watan Yuni, 2026. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) na tuhumar El-Rufai da laifukan amfani da ofis ba daidai ba, damfara da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati a lokacin da yake gwamnan jihar. A zaman kotun da aka gudanar ranar Litinin kamar yadda rahotanni suka bayyanar, El-Rufai ya halarta tare da jami’an ICPC, DSS da kuma ’yan sanda. Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa an fitar da wasu kuɗaɗen gwamnati domin aiwatar da ayyuka da ba a…
Read More

ADC ta sanar da Amaechi a matsayin mataimakin takarar Atiku a zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar ADC ta sanar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, shi ne wanda zai yi wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar mataimaki yayin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ke cigaba da kusantowa. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa kai domin ƙarfafa matsayinsu a fagen siyasar Nijeriya musamman bisa la'akari da yadda fagen ke cigaba da ɗaukar ɗumi. Ana kallon tikitin Atiku da Amaechi a matsayin wani gagarumin yunƙuri na samar da zaɓin shugabanci daban ga ‘yan…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci da a soke rajistar jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyu huɗu bisa gazawar cika sharuɗɗan dokar ƙasa akan jam'iyyun siyasa a Nijeriya. Mai Shari'a Peter Lifu, wanda ya yi hukuncin, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, da ta soke rajistar jam'iyyun tunda sun gaza samun kaso 25 na ƙuri'a a babban zaɓen da ya gabata domin biyayya da hukuncin doka. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa, jam'iyyu biyar da suka haɗa ADC, Accord, AA, APP, da kuma ZLP ne kotun ta…
Read More

Gwamnatin Tarayya fara shari’ar mutum 400 da ake zargi da ta’addanci a kotun Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutane 400 da ake zargin su da hannu a ayyukan ta'addanci. An gudanar da shari'o'in ne a ɗakin kotuna da Babbar Kotun da ke Abuja. Tawagar masu gabatar da shari'ar ta ƙunshi Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi a matsayin shugaba da kuma Daraktan Harkokin Shari'o'in Gwamnatin Tarayya, Rotimi Oyedepo (SAN). Ana tuhumar mutane 400 ne da hannu a laifukan da aka alaƙanta da ta'addanci, taimakawa da ɗaukar nauyin ayyukan tayar da ƙayar baya. Babban Mai Shari'ar kotun, John Tsoho, ta tawagar alƙalai…
Read More

NBA ta koka kan cinkoson fursunoni a sabon gidan yarin Gombe

Daga ABUBAKAR a BOLARI Gombe Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta nuna damuwa kan tsananin cunkoson da ake fama da shi a Gidan Gyaran Hali na Gombe, inda ta bayyana cewa gidan yarin da aka gina domin ɗaukar fursunoni 390 kacal, a halin yanzu yake ɗauke da sama da fursunoni 1,000. NBA ta bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ta kai gidan gyaran halin a matsayin wani ɓangare na ayyukan bikin Makon Lauyoyi na shekarar 2026, inda ta kuma samu nasarar tabbatar da sakin fursunoni tara. Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala ziyarar, Shugaban…
Read More

Alhazan Legas 1,600 sun isa gida daga Makkah lafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Alhazan Jihar Legas guda 1,600 da suka je aikin Hajjin 2026 ne suka koma gida lafiya daga Saudiyya bayan kammala ibadar. Dawowar tawagar ƙarshe na mahajjata 187 a ranar Asabar ya nuna kammala aikin hajjin na 2026. Da yake ganawa da manema labarai a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Amirul Hajji kuma Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Legas, Ibrahim Layode ya ce gudanar da ibadar babbar nasar ce ga Jihar Legas. Ya kuma alaƙanta nasarar da gudanar da ayyukan mahajjatan bisa kyakkyawan tsari a ƙasa Mai Tsarki, yana mai cewa…
Read More

‘Mahaifina ba shi da cutar suga’, inji ɗan marigayi Janar Rabe Abubakar kan iƙirarin gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Isyaka Rabe, ɗan marigayi Manjo-Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) da ya rasu a hannun 'yan bindiga a kwanan nan, ya yi watsi da iƙirarin cewa mutuwar mahaifinsa ta faru ne sakamakon tashin "ciwonsa na cutar suga ko hawan jini". A wata hira da manema labarai a ranar Lahadi, Isyaka ya bayyana rahotannin da ke alaƙanta rasuwar mahaifinsa da cutar suga a matsayin abin da ba haka yake ba, yana mai cewa iyalansa ba su yarda cewa irin wannan rashin lafiyar ne sababin mutuwar tsohon sojan ba. Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kaɗan da…
Read More

Kano: Nan da mako uku za a gina wa ‘yan kasuwar Bichi Shagunansu, inji Garba Tukur

Shugaban Kasuwar Zamani ta Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, Alhaji Garba Tukur, ya ce sauran 'yan kasuwa da ba su mallaki shagunansu ba suna gab da mallaka. Shugaban kasuwar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gana wa da Jami'ar Yaɗa Labaran yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, a bisa ziyarar gani da ido sakamakon ginin shagunan da ake ta yi ka'in da na'in a cikin kasuwar a halin yanzu. Da yake jawabi, Alhaji Garba Tukur, ya kara da cewa, tsaikon da aka samu wajen mallaka wa sauran 'yankasuwar shagunansu, ya biyo bayan cigaba da tantance 'yankasuwar da…
Read More

Kano: Ayyukan gina Bichi muradun kyautata rayuwa masu ɗorewa ne, inji Maifata

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata ya ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa a wurare daban-daban na yankin ƙaramar hukumar. Ayyukan raya ƙasar, sun ƙunshi gyara da gina magudanan ruwa a unguwani da suka haɗa da; unguwar Zango da Maƙera da kuma Dakali. Haka ɓangaren gadoji, Shugaban yankin, Alhaji Hamza Maifata, ya sabunta gadar gaban Ofishin Hisba da Hukumar Ilimin Firamare na yankin (LEA) tare da gadar bakin masallacin 'yan Izala dake kan titin Gwarzo, dukkansu a ƙaramar hukumar. Kazalika, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya samar da wasu sababbin gadoji guda uku; a kan titin gidan Ibrahim Mu'azzamu da…
Read More

Pakistan ta sanar da shirin tsagaita wutar yaƙin Amurka da Iran yayin da Trump ya tabbatar da yarjejeniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Akwai yiwuwar yiwuwar a dakatar da kai hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya bayan ƙasar Pakistan ta sanar da cewa Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta da kuma wata yarjejeniyar zaman lafiya da ke da nufin kawo ƙarshen rikicinsu, wanda ya kawo cikas ga kasuwannin makamashi a duniya. Fraministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya ce an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, yayinda ake sa ran gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Yuni a ƙasar Switzerland. A nasa ɓangaren, Shugaba Donald Trump na Amurka ya…
Read More