22
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jinjina wa marigayiya Alhaja Abibatu Mogaji, wato mahaifiyar Shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana ta a matsayin wadda soyayyarta ta kere ga iyalanta kaɗai ta amfani hatta Nijeriya a matsayinta na ƙasa. A cewarsa, jagorancin marigayiyar, wadda ta rasu a shekarar 2013 tana da shekaru 96 a duniya, ya yi tasiri acikin al'umma ta yadda ya wuce iya furucin baka yak ai ga gani a ƙasa. Da yake jawabi a babban taron addu'ar ƙasa da aka yi a Abuja domin karrama Alhaja Magaji a Babban Masallacin Ƙasa, Sanata…
