22
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Akwai saɓani game da zaɓukan fidda gwani da aka gudanar a sassa daban-daban na Nijeriya a jam'iyyar adawa ta NDC a ranar 29 ga watan Mayu. Na kwanan nan shi ne wanda ya samu jam'iyyar a Jihar Ebonyi, musamman wajen yin murabus ɗin mambobin kwamitin zartarwarta. A yayin haɗa wannan rahoto, sama da mambobi guda 11 ne na kwamitin zartarwarta na jihar suka fice daga NDC. Daga saƙonnin da wakilin Blueprint.ng ya samu a ranar Litinin, waɗanda suka bar NDC a Ebonyi sun haɗa da Mataimakin Shugaban jam'iyyar; Kwamared Okey Idenyi, Sakatarenta; Barista Aduma…
