24
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Mashawartan Arewa (ACF) ta ƙaddamar da Kwamitin Samar da Kuɗaɗe da nufin tabbatar da tsare gaskiya da adalci wajen ciyar da harkokin ilimi da tattalin arziƙin al'umma gaba a sassan arewacin Nijeriya. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Talata, ta ce tsohon Sufeto Janar na Rundunar 'Yan sanda, Muhammad Dikko Abubakar ne zai jagoranci kwamitin, inda aka ɗora masa nauyin sanya dabarun jagoranci da tabbatar da nasarar aiwatar da manufofin kuɗaɗen. Da yake jawabi yayin ƙaddamar da kwamitin, Shugaban ACF kuma Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Ɗalhatu ya bayyana godiyarsa ga…
