Babaji

5698 Posts

Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da janar da kashe jami’an CJTF bayan ISWAP ta farmaki sojoji a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Juma'a Mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka yi kwantan-ɓauna akan tawagar motocin sojoji a Jihar Borno, inda suka halaka jami'an haɗaka na CJTF da wasu sojoji. Baya ga haka ne aka nemi ɗaya daga cikin sojojin mai muƙamin janar aka rasa. Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 5 na yamma a kusa da Sabon Gari akan hanyar Damoa zuwa Biu, a lokacin da sojoji suke rakiyar wani babban jami'i da makamai a wani yanki mai hatsari a Arewa maso Gabas. Majiyoyin tsaro da na al'umma sun tabbatar wa manema labarai cewa mayaƙan na…
Read More

Gwamnan Kaduna ya gabatar da kasafin biliyan N985.9 na 2026 da nasarorin da aka samu

A ranar Juma'a ne Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya gabatar da nasarorin da gwamnatinsa ta cimma tare da bayyana sabon taswirar ci-gaba a yayin taron tattaunawa da jama’a kan kasafin kuɗi na 2026. Uba Sani ya jaddada ƙudirinsa na tafiyar da gwamnati mai adalci, daidaito, da kuma zuba jari mai ma’ana wanda zai kawo sauyi kai tsaye ga al’ummomi a faɗin jihar. A ɓangaren gina manyan titina da ci-gaban karkara, Gwamnan ya bayyana cewa an kammala gina titina sama da kilomita 785 a mataki na ɗaya, yayin da ake cigaba da aikin wasu kilomita 550 a mataki na…
Read More

Gwamnatin Kaduna ta ƙaryata rahoton ShaharaReporters akan kuɗin tsaro

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna ta ƙaryata wani rahoton bogi da jaridar SaharaReporters ta wallafa, wanda ke ikirarin cewa babu ko sisin kwabo da aka kashe a ɓangaren tsaro a jihar. A cewar ma'aikatar tsaron wannan rahoto ƙarya ne kuma an wallafa shi ne da gangan domin yaudarar jama’a tana mai cewa gwamnatin Malam Uba Sani ta dade tana bai wa tsaro muhimmanci ta hanyar zuba jari mai yawa a fannin fasahar sa ido, kayan aiki, motocin aiki da kuma karfafa leƙen asirin al’umma wadanda suka kai darajar biliyoyin naira. A wata sanarwa da kwamishinan ma'aikatar…
Read More

Su waye ‘yan wasan Super Eagles 10 masu mafi yawan wasanni?

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Biyo bayan yadda ɗan wasan gaba na Super Eagles, Alex Iwobi ya zama na huɗu a jerin ƴan wasan da suka fi buga wasanni mafi yawa a tarihin tawagar ƴan ƙwallon Nijeriyar, Blueprint Manhaja ta zayyano ‘yan wasa guda 10 mafi yawan taka wa Nijeriya leda. Iwobi, wanda ke buga wa ƙungiyar Fulham ta ƙasar Ingila, ya wakilci Super Eagles a jimillar wasanni 90, lamarin da ya ba shi damar yin kankankan da tsohon tauraron ɗan wasa, wato John Obi Mikel. Ga jerin ƴan wasan da suka fi yawan wasanni a Super Eagles tun…
Read More

Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP kan hana Sule Lamiɗo takara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Juma'a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Babbar Jam'iyyar adawa (PDP) da ta dakatar da babban taronta na ƙasa da ta shirya gudanarwa a ranakun Asabar da Lahadi a Ibadan, Jihar Oyo. Kotun, a shari'ar da Alƙali Peter Lifu ya yi hukunci, ya kuma haramta wa Hukumar Zaɓe (INEC), sanya ido ko amince wa sakamakon taron matuƙar aka gudanar da shi ba tare da amincewa da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo a matsayin ɗaya daga cikin ƴan takarar shugabancin jam'iyyar ba. A cewar kotun, hujjar da aka gabatar mata…
Read More

‘Yan bindigar da suka yi awon-gaba da daraktocin Ma’aikatar Tsaro shida sun nemi a biya miliyan N150

'Yan bindigar da suka yi garkuwa da daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaro sun nemi kuɗin fansa har N150 miliyan, lamarin da ya ƙara gigita iyalan mutanen da aka sace, tare da jefa su cikin damuwa kan yadda za su iya tattara irin wannan maƙudan kuɗaɗen. Iyalan waɗanda abin ya faru da su sun bayyana cewa buƙatar kudin ta ƙara tsananta musu raɗaɗin mikin ciwon da suke fama da shi. "Har yanzu muna cikin fargabar abin da ya faru. Yanzu kuma suna neman Naira miliyan 150 domin sakin su shida gaba daya. Ta yaya za mu iya hada wannan kudin? Muna…
Read More

An raunata mutum ɗaya yayin faɗan ƴan sanda da sojoji a Benuwai

An samu saɓani tsakanin dakarun sojoji da wasu jami'an ƴan sanda a jihar Benuwai da ke yankin Arewa ta Tsakiyan Nijeriya, lamarin da ya haddasa harbe-harbe da kaiwa ga jikkata mutum ɗaya. Al'amarin ya auku ne bayan sojoji sun yi yunƙurin tsayar da ƴan sanda a wani shingen binciken da suka sanya a kan hanya. Rikicin ya auku ne a garin Naka da ke yankin Ƙaramar Hukumar Gwer ta Yamma aranar Talatar da ta gabata. Wannan al'amari ya jefa al’umma cikin tashin hankali a garin wanda yawancin mutanen da ke cikinsa ‘yan gudun hijira ne. An kuma gano cewa motar…
Read More

Abinda ya sa Nijeriya ba za ta iya samar da rigakafi ba – Minista

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙaramin Ministan Lafiya, Iziaq Salako ya ce har yanzu Nijeriya ba ta kai matsayin da za ta riƙa samar da rigakafin cututtuka a ƙasar ba bisa la'akari da matakin ƙarfinta. Salako ya bayyana haka ne a wata hira ta gidan talabijin na Channels a jiya Alhamis inda yake bayyana matakin ƙarfin Nijeriya game da samar da rigakafi. Ya ce, samar da rigakafi abu ne da ke buƙatar a yi la'akari da ƙarfin tattalin arziƙi da kayan aiki, lamarin da a cewarsa ke da buƙatar ɗaukar ɗawainiyar kansa yayin da aka fara. Ya ƙara da…
Read More

Ƙudirin hana ƴan ƙasa da shekaru 18 shiga aikin soja ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa na neman soke dokar da ta bada damar ɗaukar aikin soja ga waɗanda shekarunsu ya gaza 18, yayin da karatun buƙatar haka na ƙudirin 2025 ya tsallake karatu na biyu a wajenta. Sashen ƙudirin ya haramta wa ƙananan yara su shiga aikin soja bisa la'akari da kundin ƴancin yara na 2003 da dokokin ƴancin yara na Majalisar Ɗinkin Duniya da na Afirka. Haka kuma, ƙudirin, wanda Sanata Abdulaziz Yar'Adua na Katsina ta Tsakiya ya ɗauki nauyi, ya nemi a soke sashen sojojin na 2004 da maye gurbinsa da wani kundi da dokokin…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya sabunta naɗin Marwa a shugabancin NDLEA

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya sake naɗa Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin cigaba da jagorantar hukumar na tsawo wasu shekaru biyar nan gaba. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya sanar da haka a wata takarda, yau Juma’a. A watan Junairun shekarar 2021 ƙarƙashin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, aka fara naɗa Marwa a matsayin shugaban NDLEA bayan zama shugaban kwamitin shawarwari akan yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi daga 2018 zuwa Disambar 2020. Sake naɗa haifaffen Jihar Adamawan…
Read More