Babaji

5698 Posts

An zaɓi Kabiru Turaki a matsayin shugaban PDP bayan samun ƙuri’a 1,516

A daren Asabar wayewar Lahadi a birnin Ibadan, jam’iyyar PDP ta tabbatar da tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), a matsayin sabon shugabanta na ƙasa bayan ya samu rinjayen ƙuri'u a babban taron zaɓen jam’iyyar. Turaki, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan takarar da aka fi hasashe tun bayan goyon bayan da ya samu daga yawancin shugabannin jam’iyyar daga Arewa kafin taron. A sakamakon zaben da aka gudanar a gaban wakilai daga sassan kasar, Turaki ya samu kuri’u 1,516, yayin da abokin takararsa, Senator Shehu…
Read More

DSS ta kama wanda ake zargi da yi wa ƴan ta’adda jigilar makamai a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun yi nasarar cafke wani Musa Abubakar da ake zargi da aikin raba wa ƴan ta'adda makamai a Jihar Filato da wasu sassan arewa. Hakan ya biyo bayan wani sakamakon bincike na sirri da hukumar ta samu, wanda ya kai ga kama shi a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2025. Majiyoyi daga hukumar sun bayyana cewa, wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a haɗawa da raba muggan makamai da alburusai ga ƙungiyoyin ƴan ta'adda da ake danganta su da alhakin kai hare-hare a sassan…
Read More

Wike ya magantu akan korarsa a PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai taimaka wa Ministan Abuja Nyesom Wike akan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya bayyana sallamar mai gidansa da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose daga jam'iyyar PDP a matsayin abinda ya kira da 'bikin Disamba a Nuwamba'. A wata takarda da ya fitar a daren jiya Asabar, Olayinka ya bayyana cewa mambobin jam'iyyar suna taro a Ibadan domin yin biki tun kafin watan Disamba, yana mai cewa za a riƙa ganin tsokaci akan taron a matsayin saƙonnin ruɗar da jama'a. Ya ce, musamman ana gudanar da taron ne domin walwala da nishaɗin al'umma…
Read More

Gwamnoni sun tsame hannu a korar Wike da wasu a PDP yayin da INEC ta ƙaurace wa taron jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban taron jam'iyyar PDP ka iya fuskantar ƙalubale duba da cewa babu wakilci na musamman daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC). An gano haka ne a lokacin da Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana haka a wani jawabin faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen yaɗa labarai. Ya kuma ce, INEC ba ta turo wakilanta ba domin sanya ido akan taron jam'iyyar, wanda ake gudanarwa a filin wasa na Lekan da ke Birnin Ibadan a Jihar Oyo. Haka kuma gwamnan ya nesanta kansa da batun nan na sallamar Ministan Abuja, Nyesom Wike da…
Read More

Gwamnan Taraba zai koma APC

Gwamnan Jihar Taraba ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa mai mulki, wato APC. Hakan na zuwa ne bayan dogon nazari da tattaunawa tsakanin manyan jagororin siyasa a jihar da matakin na ƙasa. Majiyoyi masu ƙarfi sun tabbatar da cewa an sanya ranar 19 ga wannan watan domin gudanar da bikin tarbarsa cikin jam’iyyar ta APC a wani babban taro da ake sa ran zai janyo hankalin jam’iyyu da dama a faɗin ƙasar. Ana sa ran zuwan gwamnan cikin APC zai kawo sabon salo a tsarin siyasar Taraba tare da yiwuwar samun sauye-sauye a a harkokin ci-gaban siyasar gwamnan.
Read More

Zamfara: ‘Yan bindiga sun halaka jigon APC, Umar Moroki a hanyar Gusau

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar yau Asabar ne ƴan bindiga suka kashe Alhaji Umar S Fada Moriki wanda fitaccen ɗan siyasa a jihar Zamfara kuma jigo a jam'iyyar APC. Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne wani yanki na babban titin Gusau zuwa Tsafe, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Gusau. A wata sanarwa da jam'iyyar APC reshen jihar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta, Yusuf Idris ya ce marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan halartar taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, wanda Ƙaramin Ministan tsaron Nijeriya,…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsagin PDP ya amince da Damagum a matsayin tabbataccen shugaba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsagin Babbar Jam'iyyar adawa (PDP) ya tabbatar da Umaru Damagum a matsayin halastaccen shugaba. An yanke hukuncin ne yayin wani babban taron jam'iyyar na 2025 wanda ake gudanarwa a yau Asabar a filin wasa na Lekan da ke Ibadan a Jihar Oyo. Hon. Tony Abineri, wato Shugaban jam'iyyar na Jihar Edo tare da masu zaɓe (deliget) guda 3,000 suka gabatar da shi, lamarin da ya samu goyon baya daga Edward Marshal. Abineri ya bayyana cewa matsayar ta yi daidai da sashe na 32 da kundin dokokin jam'iyyar. "Ina mai gabatar da ƙudirin gamsuwa da…
Read More

‘Yan sanda sun tsare Alwan Hassan kan zargin Barau da hana tabbatar da shugabancin Ramat a NERC

Rundunar ƴan sanda ta tsare Alwan Hassan, Shugaban kungiyar Grassroots Initiative Concept, kwana kaɗan bayan ya zargi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da hana tantance Abdullahi Garba Ramat a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa, NERC. Rahotanni sun bayyana cewa an tsare Hassan ne a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yansanda, FCID, da ke Abuja bayan ya amsa gayyatar ƴansanda a jiya Juma’a. Babu cikakken bayani kan ƙorafi ko zargin da ya haifar da wannan gayyata a lokacin da aka samun wannan rahoto. Hassan, wanda tsohon hadimin shugaban kasa, a kwanan nan yi zargin cewa…
Read More

Ba a yi garkuwa da janar ba a harin ISWAP, inji Rundunar Sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojoji ta tabbatar da kai wa dakarun Task Force Brigade na 25 ƙarƙashin jagorancin mayaƙan ISWAP a Jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas. Al'amarin ya faru ne a lokacin da jami'an suke kan hanyar dawowa daga wani atisayen da suka yi nasara a Dajin Sambisa, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji biyu da mambobin jami'an sa kai na haɗaka na CJTF su ma su biyu. Harin, wanda ya auku a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 5 na yamma an ƙaddamar da shi ne a yankin Sabon Gari a babbar hanyar Damoa…
Read More

Taron PDP: ‘Yaƴan jam’iyya sun cika Ibadan duk da umarnin kotu na hanawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma sun cika filin wasa na Lekan da ke Birnin Ibadan a Jihar Oyo, yayin da babbar jam'iyyar adawa a Nijeriya (PDP) ta fara shirye-shiryen gudanar da Babban taronta na ƙasa duk da rikicin cikin gida da na shari'a da ake cigaba da fuskanta jagororinta. Rahotanni sun bayyana cewa tun da misalin ƙarfe 7 na safe ne aka ga taron deliget, jami'an tsaro, ma'aikatan sufuri da magoya baya sun yi cincirindo domin fara taron. A cewar jaridar NewsPointNigeria, an ga dandazon jama'a a wajen taron, wanda hakan ya sa kwamitin shirye-shirye ya ƙara adadin…
Read More