Babaji

5698 Posts

Ministan Labarai ya taya sabon shugaban GOCOP, Ɗanlami Nmodu murna

Ministan Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, ya taya Alhaji Ɗanlami Nmodu murnar zaɓen sa da aka yi a matsayin Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Jaridun Yanar Gizo (GOCOP) a zaɓen da aka gudanar a Jihar Legas. Idris ya ce: “Malam Nmodu, mawallafin Newsdiary Online, wanda nake da alaƙa ta abota da ta aiki da shi tsawon shekaru da dama, ɗan jarida ne nagari wanda ya tabbatar da cancantar sa a aikin jarida, kuma ya dace da wannan matsayi mai daraja.” Ministan ya kuma yaba wa tsohuwar Shugabar ƙungiyar, Hajiya Maureen Chigbo, mawallafiyar RealNews Online, kan jagorancinta na mawallafan onlayin…
Read More

Babu wata barazana da za ta tsorata mu – ASUU ga Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ASUU, ta yi watsi da umarnin gwamnati na kada a biya albashi ga mambobinta da suka shiga yajin aiki, yana mai gargaɗin cewa babu wata barazana da za ta sa su ja da baya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels inda ya ce a shirye suke su cigaba da bin tsarin tattaunawa, amma ba za su lamunci kama karya daga ɓangaren gwamnati ba wajen ƙoƙarin raina ikon fannin ilimi. ASUU ta shiga cikakken yajin aiki na makonni biyu tun a ranar…
Read More

NiMET ta yi hasashen ƙwala zafin rana a jihohin Arewa

Jihohin Arewa za su fuskanci zafin rana a wannan mako, kamar yadda NIMET, watoHukumar kula da yanayi ta ƙasa ta bayyana. Ta ce, za a fuskanci ƙwala zafin ranar ne a sassa daban-daban na Nijeriya daga Litinin zuwa Laraba. A cikin hasashen da hukumar ta fitar a Abuja, ta ce Arewa za ta fuskanci rana mai zafi da girgijen hadari, yayin da ake sa ran ruwan sama da iska a wasu sassan Taraba da Kebbi. Daga bisani kuma, ana iya samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu yankuna kamar Adamawa, Kaduna, Borno, Bauchi, Gombe, Kebbi da Kudancin Sokoto. Hsashen…
Read More

Kano: Ƙungiyar ƴan kasuwa a Bichi ta ziyarci malamai a Ƙaramar Hukumar

A kokarin bunkasa al'amuran da za su habaka gina rayuwar al'umma, kungiyar 'yan kasuwa ta Bichi, Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited, ta samu ganawa da Sheikh Lawan Abubakar da Alh. Musa Yaro da Malam Isah Bala da kuma Hon. Sani Mukaddas Bardan Bichi. Shugaban Kungiyar, Alhaji Abubakar Mazahim Sale ne ya sanar da haka ga manema labarai cewa Sheikh Lawan Abubakar, da ya kansance limamin babban masallacin Juma'a na Karamar Hukumar Bichi, ya ja hankalin 'yan kasuwa su ci gaba da ba da hadin kai da goyon bayan dukkan al'amuran da za su ciyar da su gaba. Haka kuma su…
Read More

An rage wa Kano Pillars maki uku da tarar miliyan N9.5 bisa cin zarafin alƙalin wasa da wasu laifukan

Hukumar Gudanarwar Gasar Nigerian Premier League, NPFL ta ci tarar ƙungiyar Kano Pillars bayan wani hayaniya da ya ɓarke a yayin karawarta da Shooting Stars a mako na 8 da wannan kakar. Akan haka ne Kano Pillars za ta biya Naira milyan 9.5, sannan za a zaftare mata maki uku da kuma haramta mata wasa a gida saboda rikici. Hukuncin da aka ɗauka akan Kano Pillars shi ne kamar haka: Tarar Naira Miliyan Daya (₦1,000,000.00) saboda rashin samar da isasshen tsaro da inganci. Tarar Naira Miliyan Daya (₦1,000,000.00) saboda jefa abubuwa masu hadari zuwa cikin filin wasa da jifan jami'an…
Read More

An tayar mana da mikin ciwo – Iyalan Marigayi Bello sun yi tir da afuwar Tinubu ga Maryam Sanda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iyalan Marigayi Bilyaminu Ahmed Bello, wanda matarsa, Maryam Sanda ta halaka a shekarar 2017, sun koka da yin alla-wadai da afuwar shugaban ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa matar a ƙarƙashin ikon doka. A wata takarda da Dakta Bello Haliru Mohammed (Ɗan Galadiman Gwandu) ya fitar a madadin iyalan, ƴan uwan marigayin sun bayyana matakin a matsayin abinda ya sabunta musu raɗaɗin rashinsa musamman duba da yadda aka yi ta ɗauki-ba-daɗi a yayin shari'ar al'amarin. A cewarsa, iyalan sun zaɓi yin shuru da riƙe kansu tun lokacin faruwar al'amarin a ranar 19…
Read More

Ƙananan Hukumomin Katsina uku sun yi sulhu da ƴan bindiga

Daga UMAR GARBA a Katsina Kananan hukumomin Malumfashi, Funtua da Bakori sun bi sahun wasu takwarorinsu da suka yi sulhu da ƴan bindiga a jihar da ke fama da matsalar tsaro. Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya da ke fama da matsalar ƴan bindiga masu kai hare-hare a ƙauyuka da garuruwan jihar da kashe mutane da sace wasu domin neman kuɗin fansa. An gudanar da zaman sulhun ne a garin Kakumi da ke yankin qaramar hukumar Bakori, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana. Taron sulhun ya samu halartar shugabannin alumomin yankunan da wakilan ƴan bindigar. A…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Tarayya ta umarci a dakatar da biyan albashin ‘yan ASUU

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da biyan albashin malaman jami'o'in da suke ƙarƙashin ƙungiyar ASUU da ta shiga yajin aiki a yau Litinin. Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ya sanar da umarnin hakan a cikin wata takarda da ya sanya wa hannu, inda ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da biyan albashi ga ma’aikatan da suka daina aiki ba, bisa ka’idar “no work, no pay.” A cewar ministan, Gwamnatin Tarayya tana buɗe ƙofa ga tattaunawa da ƙungiyar ASUU domin magance matsalolin da suka jawo yajin aikin, amma ta jaddada cewa za a cigaba da aiwatar da dokokin…
Read More

Soja ya kashe kansa bayan halaka matarsa a Neja

Wani mummunan lamari ya faru a sansanin sojoji na Wawa da ke Jihar Neja, inda wani soja mai suna Lance Corporal Akenleye Femi, da ke aiki a Bataliya ta 221, ya kashe matarsa sannan ya kashe kansa. Al'amarin ya auku ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025, lamarin da ya tayar da hankula a cikin sansanin, inda mazauna yankin suka shiga cikin firgici da mamaki. Rahotanni daga rundunar sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa an gano gawar sojan da matarsa a cikin gidansu da ke Block 15, ɗaki na 24, a wajen mazaunin sojoji masu ƙananan mukamai a sansanin. Bincike…
Read More

Babu shirin sauya Ministan Kuɗi kan rashin lafiyarsa, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Kasa ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa ana shirin maye gurbin Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Mr. Wale Edun, wanda yake rashin lafiya a halin yanzu. Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi karin haske akan hakan a daren Lahadi yayin da jita-jitar ta ci gaba da yaduwa a tsakanin al'umma. Wannan bayanin na zuwa ne bayan jita-jitar da ta yadu cewa ministan yana cikin matsanancin rashin lafiya kuma har ma an tafi da shi Asibiti a ƙasar waje. Onanuga ya nanata cewa Yana rashin lafiya ne…
Read More