Babaji

5698 Posts

Rashin lafiya: Gwamnan CBN zai maye gurbin Ministan Kuɗi a zaman IMF

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso zai jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron shekara-shekara na Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Ƙasa-da-Ƙasa (IMF) da za a gudanar a birnin Washington DC daga ranar Litinin, 13 ga Oktoba. Olayemi Cardoso zai wakilci Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙin Ƙasa, Mista Wale Edun, wanda ba zai samu damar halarta ba sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita. Sannan daga cikin tawagar Nijeriyar akwai Ƙaramar Ministar Kuɗi, wato Doris Uzoka-Anite da wasu manyan jami'an gwamnati. A cewar Bankin Duniya, muhimman abubuwan da za su gudana a taron sun haɗa da Zaman Babban…
Read More

Sufeto Janar ya sauya wa kwamishinan Abuja wajen aiki kan kisan ƴar jaridar Arise News

Sufeto Janar na Ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ƴan sandan Birnin Tarayya Abuja, Ajao Adewale daga muƙaminsa. Kodayake ba a bayyana dalilin sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa an yi hukuncin ne duba da yadda rundunar ta Abuja ta gudanar da batun gilashin mota mai duhu da kuma kisan ƴar jaridar Arise News, Sommie Maduagwu a ƴan kwanakin nan. Ana ganin waɗannan matsaloli biyu ne suka haifar da sauya masa wajen aikin zuwa wajen da ya fi dacewa da ƙwarewarsa. Wata majiya ta ce, Sufeton Janar ɗin ne zai bayyana hakan wajen za a…
Read More

Nijeriya na alfahari da kai – Tinubu ga Seyi kan zagayowar ranar haihuwarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya miƙa saƙon taya murna ga ɗansa Seyi Tinubu, wanda ke cika shekaru 40 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin kamili mai mayar da hankali akan al'amuransa masu amfani, lamarin da ke tasiri acikin al'umma da ma ƙasa baki ɗaya. A wata takarda da Tinubu ya fitar a jiya Lahadi, Shugaban ƙasar ya yaba wa ɗan nasa akan yadda yake da ƙwarewar shugabanci da ƙoƙarin gina al'umma yana mai bayyana hakan a matsayin abin alfahari ga Nijeriya. Ya ce, Seyi ya kasance mai jajircewa akan ababe masu amfani tun…
Read More

Magoya bayan Kano Pillars sun farmaki ƴan wasa bayan Shooting Stars ta farke ana dab da tashi

An samu tashin hankali a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar Kano a yayin wasan da ya gudana tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars da Shooting Stars (3SC), bayan da magoya bayan Kano Pillars suka mamaye filin wasa cikin fushi sakamakon farke kwallon da baƙuwar ƙungiyar ta yi. Rahotanni sun bayyana cewa magoya bayan sun kai hari kan alƙalin wasa, wanda ya tsere domin tsira da ransa, yayin da wasu daga cikin ƴan wasan 3SC suka gamu da farmaki. Daga bisani, jami’an ‘yan sanda da ke tsaron filin sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen…
Read More

Ba aiki ba albashi – Gwamnatin Tarayya ga ASUU

‎Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da cewa duk wani malami da ya shiga yajin aikin gargaɗi da ƙungiyar ta sanar, ba za a biya shi albashi ba a lokacin. A wata takardar haɗaka tsakanin Ministan Ilimi Tunji Alausa da Ƙaramar Ministar Ilimi, Suwaiba Sa'id suka fitar, Ma'aikatar ta bayyana cewa gwamnati ba za ta amince da biyan albashi ga malaman da ba su je aiki ba domin ba a biyan albashi ga wanda bai yi aiki ba.‎‎Gwamnatin ta jaddada cewa ƙofa a buɗe take don cigaba da tattaunawa da ƙungiyar, amma hakan ba zai hana…
Read More

Yanzu-yanzu: ASUU ta tsunduma yajin aikin gama-gari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami'o'in Nijeriya ASUU ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na makonni biyu a baki ɗaya jami'o'in da ke faɗin ƙasar. Za a fara yajin aikin ne daga ƙarfe 12 na daren Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana haka a Jami’ar Abuja yayin ganawa da manema labarai a yau Lahadi. A cewarsa, hakan ya biyo bayan ƙarewar wa'adin kwanaki 14 na gargaɗin da ƙungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayyar na ta warware matsalolin walwalar lakcarori da, samar da wadatattun kuɗaɗe ga jami'o'i da aiwatar da…
Read More

CBN ya ba bankuna sa’o’i 48 su riƙa mayar wa kwastomomi kuɗaɗensu da suka maƙale a na’urar ATM

Babban Bankin NNijeriya CBN) ya umarci dukkan bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin kuɗi da su riƙa mayar wa abokan kwastomominsu kuɗaɗen da suka maƙale a sakamakon gazawar na’urar ATM cikin sa'o'i 48. CBN ya yi haka ne domin kare masu amfani da bankuna da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin kuɗi. Umarni na ƙunshe ne cikin sabuwar ƙa’ida da Babban Bankin ya fitar mai taken 'Jagororin Ayyukan Na’urar ATM a Najeriya', wanda Daraktan Sashen Tsarin Biyan Kuɗi, Musa I. Jimoh, ya sanya wa hannu. CBN ya ce bankuna su tabbatar da cewa idan sabis ya gaza, ana mayar da…
Read More

BIVAS da IReV ba za su iya magance matsalolin zaɓe a Nijeriya ba – Tsohon Shugaban INEC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da ya sauka a kujerar kwanan nan, ya ce duk da cewa an ƙirƙiro amfani da na'urorin zamani don inganta harkokin zaɓe musamman wajen tabbatar da gaskiya da adalci a tsawon shekaru goma baya, hakan bai wadatar ba wajen hana samuwar matsaloli a lamuran zaɓen ƙasar. Farfesan ya bayyana haka ne a wani sabon littafinsa mai shafi 200 da INEC ta fitar mai suna 'Election Management in Nigeria: 2015-2025', wanda ya yi tsokaci akan ayyukan INEC, nasarori, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ƙalubale a yayin zangonsa biyu a…
Read More

Ƙungiyar HURIWA ta caccaki Tinubu kan naɗa Amupitan a matsayin shugaban INEC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar kare ci-gaban ƴancin al'umma ta ƙasa (HURIWA), ta yi tir da naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe (INEC) da Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon da ya gabata. Ta bayyana hakan a matsayin yunƙurin maguɗi a baban zaɓen 2027 wajen bai wa Jam'iyya mai mulki ta APC nasara. A wata tarda da Shugabanta, Kwamared Emmanuel Onwubiko ya fitar, HURIWA ta zargi Tinubu da naɗa yaronsa domin sanya ido akan lamuran shirye-shiryen zaɓen ƙasar yayin da ake cigaba da tunkarar 2027, tana mai cewa hakan na nuna yadda…
Read More

Tinubu zai je Italiya taron Aƙaba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Lahadi Shugaba Bola Tinubu zai je Rome, Babban Birnin ƙasar Italiya daga Abuja domin halartar zaman shugabannin ƙasashe na 'Aqaba Process', wanda zai mayar da hankali akan matsalolin tsaro da suka shafi yankin Yammacin Afirka. Za a fara zaman ne a ranar 14 ga watan nan na Oktoba, inda jagororin ƙasashe da manyan jami'an tsaro na gwamnatoci za su haɗu da wakilan ƙungiyoyin gwamnati da waɗanda ba su ba domin tattauna batutuwan ƙalubalen tsaro a shiyyar. A shekarar 2015 Sarki Abdullah na II na ƙasar Jordan ya samar da tsarin zaman shugabanni…
Read More