Babaji

5715 Posts

Hisbah ta jinjina wa Majalisar Dokokin Katsina bisa amincewa da kafa hukumar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar Hisbah a Jihar Katsina ta bayyana jin-daɗinta tare da godiya ga Majalisar Dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasiru Yahaya bisa amincewa da suka yi na kafa hukumar. Shugaban hukumar, Dakta Aminu Usman wanda aka sani da Abu Amar ya bayyana hakan a lokacin da tawagarsa suka kai ziyarar girmamawa ga kakakin. Dakta Usman ya faɗi wasu nasarori da hukumar ta samu tun daga kafuwar ta inda ta fara da ziyarar ɓangarori daban-daban na malaman addinin Musulunci domin neman haɗin-kai . Ya ƙara da cewa, hukumar ta kuma ziyarci hukumomin tsaro tare…
Read More

Eguavoen zai cigaba da jagorancin Super Eagles yayin da Madugu ya zama kocin Super Falcons

Daga BELLO A. BABAJI Kwamitin Zartarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF), ya tabbatar da zaɓin kwamitin gudanarwa da ci-gaba na a bai wa Daraktan gudanarwa, Augustine Eguavoen damar cigaba da zama kocin ƴan Super Eagles. Eguavoen, mai shekaru 58 ya jagoranci tawagar a wasanni uku da suka buga a baya da ƙasashen Jamhuriyar Benin da ta doke da ci 3 da 1 da kuma Ruwanda a wasanni biyu. Hakan ya nuna cewa, kocin shi zai jagoranci Super Eagles a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka na 2025 da za a yi a wata mai zuwa da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Matar gwamnan Akwa-Ibom ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI An tabbatar da mutuwar Misis Patience Martha Umo Eno, matar Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Fasto Umo Eno. Kwamishinan Labarai na jihar, Ini Ememebong ya faɗi hakan cikin Wata sanarwa da ya fitar da asubahin ranar Juma'a. Ya ce, matar da rasu ne a wani asibiti a daren ranar Alhamis a yayin da iyalanta ke kusa da ita. Ememebong ya ƙara da cewa, iyalan marigayiyar sun miƙa al'amarin ga Ubangiji tare da roƙon addu'a daga wajen al'umma da taimakon su a lokacin ƙuncin da suka tsinci kansu. Gwamna Eno ya yi godiya ga waɗanda suka tsaya a kan…
Read More

Ɗalibai 29,633 ne suka ci kiredit biyar zuwa sama a NECO a Katsina – Gwamnatin jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ce, ɗalibai 29,633 daga jihar sun samu nasarar lashe kiredit 5 zuwa sama, ciki harda darasin Lissafi da Turanci a jarrabawar NECO ta shekarar 2024. Kwamishinar Ilimi, Zainab Musa Musawa ce ta bayyana hakan yayin da ta ke zantawa da manema labarai a birnin Katsina. Ta ce, alƙaluman da hukumar shirya jarabawa ta NECO ta fitar, ya nuna cewa Katsina ce jiha ta shida a jerin jihohin Nijeriya wajen samun sakamako mai kyau. “Wannan babbar nasara ce, inda ɗalibai 29,633 suka cika wannan muhimmin ma’auni a cikin jihohi 30 har da…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya karɓi baƙoncin zaɓaɓɓen gwamnan Edo da gwamnonin APC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganawa da zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da ya karɓi baƙoncinsa. Okpebholo ya je fadar ne tare da wasu gwamnonin jami'yyar APC da suka haɗa da; Shugaban tawagar gwamnnonin (PGF) kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma; Shugaban gwamnonin Nijeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak; Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna; Gwamna Usman Ododo na Jihar Kogi da kuma Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun. Sauran sune; Sanata Adams Oshiomhole da kuma Mataimakin gwamnan Edo Mista Philip Shaibu. Hukumar zaɓe (INEC) ta sanar da Monday…
Read More

Bayan shekara shida a tsare, kotu ta yanke wa ɓarayin da suka yi sata a Offa hukuncin kisa

Daga BELLO A. BABAJI Mai Shari'a Haleemah Salman ta babbar kotun tarayya da ke Jihar Kwara ta tabbatar da waɗansu mutane biyar da hannu a laifukan mallakar malamai ba bisa ƙa'ida ba da fashi da makami da kuma kisan kai, inda ta ce hukuncin waɗannan laifuka shi ne kisa. Lamarin ya auku ne a watan Afrilun 2081 inda ta ce baki ɗaya hujjojin da aka gabatar a kan su sun tabbatar da cewa mutanen su na da hannu dumu-dumu acikin laifukan. Mutanen sune; Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salahudeen Azeez da kuma Niyi Ogundiran. A lokacin da ya ke…
Read More

Majalisa ta tabbatar da Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattijai ta tabbatar da naɗin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya, CJN. Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio shi ya yi hukuncin bayan sauraron bayanan tabbatarwar daga kwamitinsa kan batun, a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024. Kekere-Ekun ita ce Alƙali ta 23 ta hawa kan kujerar muƙamin kuma mace ta biyu a irin muƙamin.
Read More

Yahaya Bello ya maka EFCC a Kotun Ƙoli kan almundahana

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya kai ƙarar Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ga Kotun Ƙoli kan shelanta shi a matsayin wanda ake nema. EFCC ta na tuhumar Yahaya Bello ne da hannu a laifuka 19 bayan zargin sa da hannu a sauya akalar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 80.2. A ranar Laraba ne aka buƙaci Bello ya halarci babban kotun tarayya don sauron ƙarar da ke kansa. Saidai, a lokacin fara tattaunawa kan batun, tawagar lauyoyin da ke kare Bello ƙarƙashin jagorancin A. M. Adoyi sun…
Read More

Shettima ya nemi a samar da mafita ta dindindin ga yaƙin Gaza

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga shugabannin duniya su samar da mafita ta dindindin game da yaƙin Gaza da ake cigaba da yi. Ya ce, akwai buƙatar al'ummar Palestine su samu ƴanci ganin yadda ake cigaba da ɗaiɗaita su. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabin yayin muhawara da shugabannin duniya a taron game da batutuwan da suka shafi al'umma. A ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 ne aka fara yaƙin Gaza a ƙasar…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da aniyar Tinubu na yi wa ministocinsa garambawul

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta yi wa tawagar ministocinsa garambawul. Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya bayyana hakan wa wakilan Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja inda ya ce gwamnati ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na farfaɗo da tattalin arziƙi wanda al'umma ba ta sani ba. Onanuga, ya ce Shugaba Tinubu ya umarci ministocinsa su ke bayyana wa al'umma ayyukan da ma'aikatu da dama ke yi na inganta ƙasa. A baya ne Tinubu ya sha alwashin yin nazari game da ayyukan ministocin wanda hakan…
Read More