Babaji

5681 Posts

DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace mahaifiyar Mawaƙi Rarara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rahotanni daga Jihar Katsina sun ce Rundunar 'Yan sandan jihar ta kama mutum biyu da ake zargin su da hannu a garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Dauda Ƙahutu Rarara, Hajiya Ibrahim. Kakakin Rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce ana cigaba da binciken waɗanda aka kama, a ƙoƙarinsu na ceto ta. A yau juma'a ne aka yi garkuwa da Hajiyar mai kimanin shekaru 75 a ƙauyen Kahutu dake Ƙaramar Hukumar Danja, a Jihar Kastina da misalin ƙarfe 1:30 na rana. Wannan wani huɓɓasa ne da rundunar 'Yan sandan ta yi wajen ganin an daƙile ayyukan garkuwa da…
Read More

Lookman ya zama gwarzon shekara a Atalanta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan wasan Nijeriya da ke buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atalanta, Ademola Lookman ya lashe kyautar ɗan wasan gwarzon shekara na kakar wasan 2023/2024 a ƙungiyar biyo baya taka rawar gani da ya yi. Lookman mai shekaru 26, ya yi ƙoƙari wajen nuna bajinta wa ƙungiyar a gasar 'Serie A' ta ƙasar Italiya wanda hakan ta sa ya kai Atalanta ga nasarar lashe kofin gasar 'Europa' inda ya zura ƙwallaye uku a wasan ƙarshe tsakanin kulob ɗinsa da ƙungiyar Bayer Leverkusen ta ƙasar Jamus. Har ila yau, Lookman ya lashe kyautar cin ƙwallo mafi kyau…
Read More

Sabon kocin Napoli ya amince da ficewar Osimhen daga ƙungiyar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli, Antonio Conte ya ce ya amince da buƙatar Victor Osimhen na son barin ƙungiyar a kakar wasan bana. Conte ya faɗi hakan ne kasancewar akwai yarjejeniya tsakanin ɗan wasan Nijeriyan da kuma Napoli. Ƙwararren ɗan jaridan wasannin, Fabrizio Romano ya ruwaito cewa, Conte ya ce yana sane da yarjejeniyar da ke tsakanin ɗan wasan da kulob ɗin saɓanin sauran ƴan wasa. Ganin haka ke da wuya, ake ta jita-jitar cewa Conte na son kawo ɗan wasan ƙasar Baljika, Rumelu Lukaku domin maye gurbin Osimhen.
Read More

Zafin rana ya sa an taƙaita huɗubar sallar juma’a a Saudiyya da Dubai

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙasashen Saudiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sun sanar da rage adadin lokacin gudanar da huɗubobin sallar jumma'a a masallatai saboda tsananin zafin rana da su ke fama da shi. Al'ummar musulmi a ƙasashe da dama na duniya kan gabatar da sallar jumma'a ne da rana wacce masallata ke zama domin sauraron ta ciki da wajen masallaci da wuraren da babun rumfuna, don haka ƙasashen biyu suka yanke hukuncin hakan domin sauƙaƙa mu su kamar yadda addinin Musulunci ya karantar. Shugaban ma'aikatar kula da harkokin addini na ƙasar Saudiyya ya ce, sun rage adadin lokacin huɗubar zuwa…
Read More

Wike zai tashi kasuwar ‘Mechanic Village’ zuwa Wassa

Daga KHADIJA ABUBAKAR Majalisar kula da ayyukan birnin tarayya, AMMC ƙarƙashin ofishin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta ce za ta sauya wa makanikai da ƴan kasuwan kan hanya na 'Mechanic Village' dake yankin Apo wajen aiki zuwa Wassa. Sanarwar ta fito ne daga shugaban Majalisar, Felix Obuah a wata hira da manema labarai bayan ganawa da wikilan makanikan da na ƴan kasuwan da abin ya shafa, a ranar Talata. Obuah, ya ce Wike ya tabbatar da aikin wanda aka shirya shi musamman don ƴan kasusuwar kan hanya da makamantansu kuma ya ce za'a fara korar su nan da wata ɗaya…
Read More

El-Rufai ya karɓi baƙuncin Kwankwaso kwanaki bayan kai wa Buhari ziyara

Daga FAROUK ABBAS Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya karbi baƙuncin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja a ranar Alhamis, kwanaki kaɗan bayan kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ziyara a Daura, Jihar Katsina. A ƴan kwanakin nan ne El-Rufa'i na jam'iyyar APC, ya yi ta ganawa abokanan hamayyarsu na siyasa ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma ziyartar shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa a Abuja da ya yi. El-Rufa'i, wanda tsohon ministan Abuja ne, na ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa za a basu muƙaman…
Read More

Ƙananun ma’aikatan gidan yari sun koka kan dokar sabon kaya a jarrabawar ƙarin girma

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙananan jami'an hukumar gidajen yari ta NCS, sun koka kan yadda ta gagara raba musu sabon kayan sa wa na hukumar a kyauta bayan bai wa manyan jami'anta. Jami'an sun ce abun da ya ƙara dagula lamarin shi ne yadda hukumar ta sanya mallakar sabon kayan a matsayin ɗaya daga cikin rukunan jararbawar ƙarin girma da ta yi, wanda za'a gudanar daga ranar 1 zuwa 6 ga watan Yuli, 2024. Wani jami'i da bai yadda a faɗi sunansa ba, ya ce a ayyukan da ake sanya inifom, a kan bai wa manyan jami'ai kyauta, amma ƙananan…
Read More

Tinubu ya amince da bayar da tallafin 50,000 ga magidanta 100,000 na tsawon watanni uku

Daga KHADIJA ABUBAKAR Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da shirin gina ƙasa da tallafawa magidanta a yayin wani zama da Majilisar kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasa, NEC a Abuja. Wani jawabi da ya fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya ce manufar shirin su ne dan a inganta harkokin noma da tattalin arziƙi gami da bada tallafi domin rage raɗaɗin talauci ga ƴan Najeriya. Shirin wanda ya samu goyon bayan Majalisar ta NEC, ya ƙunshi rarraba kuɗaɗe da yin ayyukan more rayuwa a dukkan shiyyoyin ƙasarnan guda shida, inda za a bada tallafin Naira…
Read More

Mutum biyu sun kamu da kwalara a Katsina, 118 kuma na karɓar kulawa

  Daga Naziru Adam Ibrahim Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina, ta ce an tabbatar da cutar kwalara ta kama mutum biyu a ƙaramar hukumar Kusada, da ke jihar tare da wasu 118 da a ke binciken lafiyarsu. A cewar hukumar, tuni an ɗauki matakan fara amfani da tsarin kula da al’amuran da ke faruwa domin hana yaɗuwar cutar da sauran cutukan da za a iya rigakafinsu a jihar. Daraktan kula da cutuka na hukumar, Dakta Kabir Sulaiman, a wani taron manema labarai a cibiyar bayar da agajin gaggawa ta hukumar, ya bayyana cewa gwamnatin…
Read More

Rikicin Masarauta: Aminu Ado ya ɗaga tuta a fadar Nasarawa

Daga Sadiq Yayin da ake tsaka da rikicin masarautar Kano, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya ɗaga tutar mulki a ƙaramar fadar da ke Nassarawa inda hakan ke nuna iko da Sarkin yake da shi a yanzu. A bisa al’ada, tutar na zama ne a matsayin alamar iko, kuma ɗaga ta na alamta cewa sarki yana cikin fada. Hakan kuwa na zuwa ne duk da umarnin gwamnatin Kano ga Sarki Aminu na ya fice daga fadar a yayin da ake cigaba da dambarwar sarautar Kano. Akan ɗaga tutar ce da misalin karfe 6 na safe a kuma sauke…
Read More