30
Jun
Daga DAUDA USMAN a Legas Wani babban dillalin sayar da doya a Legas kuma babban mai saukar baƙi masu kawo doya daga jihohin Nijeriya zuwa Legas, Alhaji Lado Yaro Jos ya bayyana yadda hauhawar farashin doya a samo asali a Legas. Alhaji Lado Yaro Jos ya yi wannan tsokaci ne a Legas a lokacin da yake zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja dangane da yanayin kasuwancin doya a Nijeriya da kuma matsatsin rayuwar al'umma bakiɗaya. Alhaji Yaro, ɗan asalin Jihar Kano mazaunin Legas wanda yake gudanar da harkokin kasuwancin doya a kasuwar doya ta Shukura Yam Salas da ke kasuwar…
