29
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan Majalisar Wakilai 50 sun aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wasiƙar neman ya saki shugaban ƙungiyar ta’addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu. Honorabul Mohammed Jajere ya tabbatar wa Manhaja goyon bayansa ga buƙatar a saki Namadi Kanu, wanda ƙungiyarsa ta IPOB ke neman ɓallewa daga Nijeriya domin kafa ƙasar Biafra. A halin yanzu dai Gwamnatin Tarayya tana gurfanar da shi a kan laifukan ta’addanci da kuma cin amanar ƙasa. Mohammed Jajere ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu zai sa samu wanzajjen zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas da ma Nijeriya baki ɗaya.…
