ukarofi

12525 Posts
Sojoji sun ceto mutum tara daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Sojoji sun ceto mutum tara daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar sojoji ƙarƙashin Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su, sun ƙwato dabbobi 56 da aka sace haka kuma sun kama wani da ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci a wasu hare-haren da suka gudana a Jihar Katsina. A cewar rundunar, dakarun sashi na 2 sun ceto mutanen ne yayin wani sintirin yaƙi a ƙaramar hukumar Faskari. Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata uku, maza huɗu da yara biyu. Binciken farko ya nuna cewa an yi garkuwa da su ne a kan hanyar Tsafe zuwa Kuchere da…
Read More
Kwamishinan ilimi ya duba wuraren da ɗalibai ke ɗaukar jarrabawar NECO a Katsina

Kwamishinan ilimi ya duba wuraren da ɗalibai ke ɗaukar jarrabawar NECO a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan ma'aikatar ilimin firamare da sakandare ta Jihar Katsina, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya duba yadda ake gudanar da jarabawar NECO da kuma ayyukan gina makarantu a yankin Daura. A ziyarar, ya bibiyi jarabawar Chemistry ta NECO da ta gudana a wasu makarantu, ya kuma gana da shugabannin makarantu kan inganta koyarwa, sannan ya duba aikin gina Model Special Secondary School a Dumurkur da kuma ɗaya daga cikin sabbin makarantun sakandare 30 da gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ke ginawa. Kwamishinan ya yaba da ingancin ayyukan tare da buƙatar masu aikin su kammala su cikin…
Read More
Gombe South LCDA za ta bai wa walwala da tsaron ‘yan hidimar ƙasa fifiko — Bappi

Gombe South LCDA za ta bai wa walwala da tsaron ‘yan hidimar ƙasa fifiko — Bappi

Daga RABILU ABUBAKAR a Gombe Shugaban hukumar raya ƙaramar hukumar Gombe ta Kudu (LCDA), Hon. Auwalu Jauro Bappi, ya yi alƙawarin bai wa jin daɗi da tsaron mambobin hukumar yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke yi wa ƙasa hidima a yankin fifiko, inda ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa shirin tare da samar musu da ingantaccen yanayin gudanar da hidimarsu. Bappi ya bayyana hakan ne yayin da koodinatan NYSC ta Jihar Gombe, Misis Chinwe Nenna Nwachuku, tare da tawagarta suka kai masa ziyarar girmamawa. Tawagar ta samu tarba tare da shugaban ƙaramar hukumar Gombe ta…
Read More
Gwamnatin Kano ta biya bashin kuɗin magunguna biliyan N1.2 da ta gada — Pharm. Ghali Sule

Gwamnatin Kano ta biya bashin kuɗin magunguna biliyan N1.2 da ta gada — Pharm. Ghali Sule

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Daraktan Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Lafiya ta Jihar Kano (DMCSA), Pharm. Ghali Sule, ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta biya bashin magunguna da ta gada daga gwamnatin da ta gabata wanda ya kai Naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari biyu. Pharm. Ghali Sule ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar hukumar a Kano, a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cika shekaru uku na gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ya ce an shirya bikin na tsawon mako guda domin…
Read More
SCHST Kano ta yaye ɗalibai 75 a fannonin lafiya da kimiyya

SCHST Kano ta yaye ɗalibai 75 a fannonin lafiya da kimiyya

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Kwalejin Koyar da Ayyukan Lafiya da Kimiyyar Zamani ta Sahal College of Health Sciences and Technology (SCHST), Kano, ta gudanar da bikin yaye ɗalibai 75 da suka kammala karatunsu a fannoni daban-daban. Daga cikin ɗaliban da aka yaye akwai ɗalibai 25 a fannin Basic Health Orientation da kuma ɗalibai 50 a fannin Basic Remedial Science. An gudanar da bikin ne a harabar kwalejin da ke Kano a ranar Lahadin da ta gabata tare da halartar iyaye, malamai da sauran baƙi. A jawabinsa na maraba, ɗaya daga cikin malaman kwalejin, Malam Hassan Magaji, ya yi…
Read More
Amina Dala Comprehensive College ta karrama Dr. Dangwani, Dantata da wasu fitattun mutane

Amina Dala Comprehensive College ta karrama Dr. Dangwani, Dantata da wasu fitattun mutane

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Makarantar Amina Dala Comprehensive College da ke ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano ta karrama wasu fitattun mutane bisa gudummawar da suke bayarwa wajen tallafa wa al’umma da kuma bunƙasa harkokin ilimi, musamman ilimin addinin Musulunci a jihar. An gudanar da bikin karramawar ne a yayin saukar karatun Alƙur’ani mai girma na mahaddata 15 da aka shirya a dakin taro na Cibiyar Koyar da Ilimin Siyasa da ke Mambayya a Kano a makon da ya gabata. Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maiduguri, Dr. Adamu Yunusa Dangwani, Gwaggo Fatsama…
Read More
’Yan kasuwar ‘Yankaba sun nemi tallafin jari daga gwamnatin Kano

’Yan kasuwar ‘Yankaba sun nemi tallafin jari daga gwamnatin Kano

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Kungiyar ’yan kasuwar Yankaba da ke sana’ar sayar da kayan miya a Jihar Kano ta roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya saka mambobinta cikin shirin tallafin jari na wata-wata da gwamnatin jihar ke gudanarwa domin bunƙasa kasuwanci. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Rabiu A. Danladi, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da wakilin Manhaja a ofishinsa da ke kasuwar a ranar Lahadi. Ya ce yawancin ’yan kasuwar, musamman masu ƙaramin jari, na fuskantar ƙalubale sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita a halin yanzu. A cewarsa, saka mambobin ƙungiyar cikin shirin tallafin zai…
Read More
‘Yan sanda sun kama wani mutum da ke kai wa ‘yan bindiga miyagun ƙwayoyi a Katsina

‘Yan sanda sun kama wani mutum da ke kai wa ‘yan bindiga miyagun ƙwayoyi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda a Katsina ta sami nasarar kama wani mai suna Sunday Eze da aka fi sani da suna Danbuje da ke kai wa yan bindiga miyagun ƙwayoyi a ƙaramar hukumar Funtua. A cewar jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu, Danbuje ya zo hannu bayan da jami'an 'yan sanda a Funtua suka sami bayanan sirri game da wannan ƙasurgumin dillalin ƙwayoyi a garin na Funtua. Ya bayyana cewa a lokacin da 'yan sanda suka kama Danbuje yana ɗauke da ƙwaya 500 na D5 a tare da shi.…
Read More
POLAC ta ƙara wa’adin rajista ga masu neman shiga kwalejin zuwa mako guda

POLAC ta ƙara wa’adin rajista ga masu neman shiga kwalejin zuwa mako guda

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Hukumar gudanarwar Kwalejin Horar da Manyan Jami’an ’Yan Sanda ta ƙasa (POLAC) da ke Wudil a Jihar Kano ta sanar da ƙara wa’adin rajistar masu sha’awar shiga kwalejin da mako guda. Shugaban kwalejin, AIG Patrick A. Atayero, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin, DSP Umar Musa Isa, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata. Sanarwar ta bayyana cewa tun da farko an tsara rufe shafin rajistar ne a ranar 15 ga watan Yuli, amma sakamakon wasu matsalolin da masu neman gurbin suka fuskanta, an…
Read More
Hajjin 2026: Za mu mayar wa alhazai kuɗin da ba a yi musu hidima ba – NAHCON

Hajjin 2026: Za mu mayar wa alhazai kuɗin da ba a yi musu hidima ba – NAHCON

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta tabbatar wa alhazan Nijeriya cewa za ta mayar musu da kuɗin ayyukan da suka biya amma ba su samu ba yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026. Shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Abba Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin Taron Masu Ruwa da Tsaki kan Bitar Hajjin 2026 da Tsare-tsaren Garambawul na NAHCON, inda ya ce tuni hukumar ta fara tantance asusun kuɗaɗe tare da kamfanonin da suka ba da hidima a Saudiyya. Ya bayyana cewa, bayan kammala aikin Hajji, NAHCON ta fara amfani da tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyoyin da…
Read More