ukarofi

12525 Posts
An kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga Sani Yellow a Zamfara

An kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga Sani Yellow a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaro na haɗaka da ke taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma sun kashe wani fitaccen shugaban ’yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Sani Yellow a Jihar Zamfara. Majiyoyin tsaro sun shaida cewa an kashe Sani Yellow ne bayan wani shiri na musamman da aka gudanar bisa bayanan sirri da aka samu daga mazauna yankin, inda aka yi masa kwanton ɓauna yayin da ake zargin ya je wata kasuwa domin karɓar kuɗaɗen shanun da aka sace da kuma kuɗin fansa daga…
Read More
Mun samu kyakkyawar tarbiyya daga wajen iyayenmu — Dakta Balaraba Ganduje

Mun samu kyakkyawar tarbiyya daga wajen iyayenmu — Dakta Balaraba Ganduje

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Daya daga cikin 'ya'yan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wato Hajiya Dakta Balaraba Abdullahi Umar Ganduje, ta bayyana cewa tana da ƙwarin gwiwar ci gaba da janyo da tallafa wa matasa masu karatu da masu sana'a, har ma tana ɗaukar wasu daga cikinsu a matsayin 'yan kafafen sada zumunta na ƙungiyarta. Hajiya Balaraba ta ce duk wanda zai ce shi ɗan social media ne na Balaraba amma ba shi da aiki ko kuma baya zuwa makaranta, to daga yanzu sun rabu. "Abin da na ga…
Read More
Tinubu ya nemi majalisa ta sake nazari kan ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Tinubu ya nemi majalisa ta sake nazari kan ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Wakilai ta sake nazari tare da ƙara himma wajen duba ƙudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya domin samar da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, a wani sabon yunƙuri na gwamnatin tarayya na sake fasalin tsarin tsaron ƙasar. A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 15 ga Yuni da shugaban ya aika wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya buƙaci majalisar ta gaggauta duba ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin da zai ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi. A cewar shugaban ƙasar, ƙudirin zai samar da…
Read More
NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na biliyan N10.3 a tashar jiragen ruwa ta Apapa

NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na biliyan N10.3 a tashar jiragen ruwa ta Apapa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hana Sha da Safarar Muggan ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wasu muggan kwayoyi da ake zargin nau'in Canadian Loud ne, masu nauyin kilo 4,143.5, waɗanda aka ɓoye cikin buhuna 8,287 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas. Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja. A cewarsa, an kama muggan kwayoyin ne a cikin wani kwantena da aka shigo da shi daga ƙasar Kanada zuwa Nijeriya, inda jami'an NDLEA suka gudanar da aikin tare da haɗin gwiwar Hukumar Kwastam da sauran…
Read More
ADC ta zaɓi Dr Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan Kebbi

ADC ta zaɓi Dr Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jam'iyyar ADC a Jihar Kebbi ta amince da ɗaukar Dakta Musa M Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027 idan Allah ya kai mu. Wannan yana ƙunshe ne a cikin takarda mai ɗauke da sa hannun mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar ADC ta Jihar Kebbi Injiniya Abubakar Atiku Musa ranar Juma'ar nan. Takardar, bayan taya shi murna ta kuma yi fatan Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da Allah ya ɗora masa da fatan Allah ya bai wa jam'iyyar ADC nasara a dukkan matakan kujerun tun daga ƙananan hukumomi…
Read More
Sojoji sun kama wanda ake zargin ɗan ISIS ne daga ƙasar waje a Borno

Sojoji sun kama wanda ake zargin ɗan ISIS ne daga ƙasar waje a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sojojin Nijeriya sun kama wani mutum da ake zargin mamba ne na ƙungiyar ISIS, wanda ake kyautata zaton ɗan ƙasar Moroko ne, a yankin Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun shaida wa jaridar Zagazola Makama cewa an kama mutumin ne bayan da sojoji suka dakile wani harin ta'addanci da aka kai a Cross Kauwa, lamarin da ya tilasta wa 'yan ta'addar tserewa tare da barin wasu kayayyakinsu a wurin. Bayan harin, sojoji sun fara bincike da kuma farautar 'yan ta'addar a hanyoyin da suka bi wajen tserewa.…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta ƙara kuɗin fansho tare da biyan basussukan shekaru 18

Gwamnatin Tinubu ta ƙara kuɗin fansho tare da biyan basussukan shekaru 18

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A cikin shekaru biyu da suka gabata, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar da manyan sauye-sauye a fannin fansho da suka kawo ƙarshen wasu matsalolin da suka daɗe suna addabar masu ritaya, tare da ƙara yawan kuɗaɗen da suke karɓa a kowane wata. Darakta Janar ta Hukumar Kula da Fansho ta ƙasa (PenCom), Misis Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Talata. Ta ce gwamnatin ta kashe Naira biliyan 758 domin biyan haƙƙoƙin fansho da suka taru tun…
Read More
Ribadu ya karɓi baƙuncin babban jami’in diflomasiyyar Amurka, Garcia, kan haɗin gwiwar tsaro

Ribadu ya karɓi baƙuncin babban jami’in diflomasiyyar Amurka, Garcia, kan haɗin gwiwar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya gudanar da wata ganawa da wata babbar tawagar gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Frank Garcia, sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mai Kula da Harkokin Afirka, domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa taron, wanda aka gudanar a Abuja, shi ne ziyarar aiki ta farko da Garcia ya kai Nijeriya tun bayan da ya karɓi muƙaminsa a ranar 1 ga Yuni, 2026, kuma yana cikin wata babbar ziyarar diflomasiyya da yake yi a ƙasashen…
Read More
Gwamnatin Jihar Neja ta haramta bukukuwan yaye ɗalibai a makarantun kuɗi

Gwamnatin Jihar Neja ta haramta bukukuwan yaye ɗalibai a makarantun kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Jihar Neja ta hana makarantu masu zaman kansu gudanar da bukukuwan yaye dalibai, tare da umartar dukkan cibiyoyin ilimi masu zaman kansu da su maye gurbinsu da bukukuwan gabatar da jawabi da bayar da kyaututtuka domin karrama nasarorin ɗalibai. News Point Nigeria ta ruwaito cewa an ƙaddamar da wannan tsari ne ta hannun Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Neja, domin daidaita shirye-shiryen ƙarshen zangon karatu da kuma magance abin da hukumomi suka bayyana a matsayin yawaitar bukukuwan yaye dalibai masu tsada da nuna almubazzaranci a makarantu masu zaman kansu.…
Read More
Kotun ƙoli ta umarci lauyoyi su loda takardun shari’o’i kafin zaman Satumba

Kotun ƙoli ta umarci lauyoyi su loda takardun shari’o’i kafin zaman Satumba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ƙolin Nijeriya ta umarci lauyoyin da ke kula da ƙarar daukaka ƙara da kuma buƙatun da aka tsara za a saurara tsakanin watan Satumba zuwa Disambar 2026 da su loda dukkan takardun shari'o'insu ta hanyar Tsarin Gudanar da Shari'o'in Nijeriya (Nigerian Case Management System - NCMS), daidai da tanadin Doka ta 10(1) na Jagororin Aiki na Kotun ƙoli na shekarar 2026. Wannan umarni na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Magatakardan Kotun ƙoli, Kabir E. Akanbi, ya aikewa da News Point Nigeria, inda ya buƙaci lauyoyi su duba jerin shari'o'in da…
Read More