18
Jul
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) ta fara karɓar buƙatun neman aiki na shekarar 2026, inda ake ɗaukar ma'aikata a rukunonin Mataimakin Jami'in Kiyaye Haɗurra (RMA), Sufeton Kiyaye Haɗurra (MI), Jami'ai (Officer Cadre) da kuma Likitoci (Officer – MBBS). A matsayin wani ɓangare na tsarin neman aikin, ana buƙatar masu neman aiki su fara ƙirƙirar asusu a shafin ɗaukar ma'aikatan FRSC kafin su cika fom ɗin neman aikin. Sai dai, bayan kammala rajistar farko, mutane da dama sun koka cewa ba sa samun saƙon imel na tabbatar da rajista, wato Activation Email, duk da sun duba…
