17
Jul
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jam’iyyun siyasa uku ne har zuwa ƙarshen wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayar ba su kai sunayen ‘yan takararsu na shugaban ƙasa da mataimakansa cikin tsarin lantarkin hukumar ba, gabanin rufe shafin karɓar sunayen da ƙarfe 11:59 na daren ranar Talata. Wani babban jami’in INEC, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a hukumance, ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyun da abin ya shafa sun haɗa da Jam’iyyar APGA, ɓangaren Jam’iyyar PDP da Nyesom Wike ke jagoranta, da kuma ɓangaren Jam’iyyar LP ƙarƙashin…
