15
Jul
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cikakken ƙwarin gwiwarsa cewa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta samu nasara a babban zaɓen shekarar 2027. Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen "Tinubu-Dikko Again 2027" a birnin Katsina. Ofishin yaƙin neman zaɓen, wanda tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shema ya kafa, domin haɗa kai da daidaita goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa yana da…
