13
Jun
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Katsina ta sanar da rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya wanda yayi kusan mako uku a hannun 'yan bindiga shi da uwargidansa. Wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar cikin gida da tsaro ɗauke da sa hannun kwamishinan ma'aikatar, Dr Nasiru Mu'azu Ɗanmusa ya sanya wa hannu ya ce Marigayi Manjo Janar Rabe ya rasu yana hannun 'yan bindiga bayan gajeruwar rashin lafiya. Dr Nasiru Ɗanmusa ya bayyana cewa marigayin wanda ke ɗauke da cutar suga da hawan jini ya sami wata yar matsala da cutar. Kafin dai rasuwar sa, kwamishinan ya ce…
