29
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani babban masani kan harkokin tsaro, Farfesa Oyesoji Aremu, ya bayyana cewa Nijeriya ta fuskanci mummunar matsalar tsaro inda aka kiyasta an yi garkuwa da mutane kusan miliyan 2.2, tare da biyan kuɗin fansa da ya kai kusan Naira tiriliyan 2.2 cikin shekara guda. Farfesa Aremu ya bayyana hakan ne yayin wani babban taron lacca da ƙungiyar Caliban Kimiyyar Zamantakewa (Social Sciences Students’ Association – SOSSA) ta Jami’ar Adekunle Ajasin, Jihar Ondo, ta shirya, inda ya yi cikakken bayani kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya, matsayinta a jerin ƙasashen duniya, da kuma mummunan tasirin da rashin tsaro…
