ukarofi

12558 Posts
Jihohi 21 na cikin haɗarin fallatsar cutar Ebola – Gwamnatin Tarayya

Jihohi 21 na cikin haɗarin fallatsar cutar Ebola – Gwamnatin Tarayya

Daga USMAN KAROFI Gwamnatin tarayya ta bayyana jihohi 21 da kuma babban birnin tarayya Abuja a matsayin wuraren da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar Ebola, bayan ɓarkewar cutar a ƙasashen Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da Uganda. Hukumar NCDC ta ce an ɗauki matakin ne domin ƙara shiri da sanya ido kan yiwuwar shigowar cutar Najeriya. Daraktan hukumar NCDC, Jide Idris, ya bayyana cewa har yanzu ba a samu ɓullar cutar Ebola a Najeriya ba, amma yawaitar cutar a ƙasashen gabashi da tsakiyar Afirka na ƙara haddasa fargabar yaɗuwarta zuwa wasu ƙasashe. Ya ce alamomin Ebola suna kama da na zazzaɓin…
Read More
Ka nesanta kanka daga takarar PDP – Tsagin Wike ga Jonathan

Ka nesanta kanka daga takarar PDP – Tsagin Wike ga Jonathan

Daga USMAN KAROFI Tsagin jam’iyyar PDP mai biyayya ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, da ya fito fili ya nesanta kansa daga raɗe-raɗin da ke alaƙanta shi da takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran tsagin, Jungudo Haruna Mohammed, ya sanya wa hannu. Tsagin ya bayyana cewa rahotannin da ke cewa jam’iyyar PDP na shirin gudanar da taro domin tabbatar da Jonathan a matsayin ɗan takararta ƙarya ne kuma ba su da sahihanci. A cewarsu, tuni jam’iyyar ta…
Read More
Masu zaɓe a Zamfara za su ɗanɗana kuɗarsu idan suka zabi shugabannin da basu dace ba a 2027, inji Sanata Marafa

Masu zaɓe a Zamfara za su ɗanɗana kuɗarsu idan suka zabi shugabannin da basu dace ba a 2027, inji Sanata Marafa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sanata Kabiru Garba Marafa, ɗan takarar gwamna na jam'iyyar National Democratic Congress NDC a Zamfara, ya yi kira ga masu zaɓe da su zaɓi cancanta a zaɓen 2027, yana mai cewa sakamakon zaɓen shugabanni marasa tasiri zai dogara ne kawai ga masu zaɓe kuma alummar jihar za su ɗanɗana kuɗarsu a hannun shugabannin da ba su dace ba in har suka zaɓe su. Marafa ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis a Gusau, jim kaɗan bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamna a jam'iyyar NDC da aka…
Read More
Rubutun Turanci ya fi min sauƙin rubutawa da sarrafa jigo – Fatima AbbaGana

Rubutun Turanci ya fi min sauƙin rubutawa da sarrafa jigo – Fatima AbbaGana

"Ina ba littafi daraja sosai fiye da yadda a ke zato" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Sunan Fatima Ibrahim AbbaGana ba ɓoyayye ba ne a tsakanin marubutan adabi na Nijeriya, musamman saboda yadda take da zumunci da ilimin zama da jama'a. Bayan kasancewarta marubuciya, Fatima ta kasance tsohuwar ma'aikaciyar banki, ýar kasuwa, kuma ƙwararriya kan binciken shigi-da-ficen kuɗi. Ta rubuta littattafai daban-daban cikin harshen Hausa da Turanci, inda take mayar da hankali kan labaran da suka shafi raya al'ada, inda zamantakewa da kyautata tarbiyya. Ita ce ta rubuta littafi mafi girma da wata marubuciya a Arewa ta wallafa, domin kuwa littafin…
Read More
Sojoji sun ceto mutum 92 a Borno

Sojoji sun ceto mutum 92 a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sojojin Nijeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai OPHK’ dake aikin samar da tsaro a Arewa maso Gabas sun ceto mutum 92 daga hannun mahara da suke zargin Boko Haram ko kungiyar ISWAP a hanyar Buratai zuwa Kamuya dake karamar hukumar Biu a jihar Borno. Kakakin rundunar Sani Uba ya sanar da haka a wani takarda da ya fitar inda yake cewa jami’an tsaron rundunar ‘135 special Forces Battalion’ dake Dutse Kura suka samu bayanin cewa mahara sun tasa keyar mutane matafiya daga cikin motocin su a titi zuwa cikin daji da…
Read More
Ranar Yara: Gwamnan Ondo ya yi kira da ceto ɗaliban Oyo da aka sace

Ranar Yara: Gwamnan Ondo ya yi kira da ceto ɗaliban Oyo da aka sace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Jihar Ondo, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ceto ɗalibai da malamai da ’yan ta’adda suka sace a Oyo. Gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ne, ya bayyana hakan ta bakin mataimakinsa da ya wakilce shi a bikin Ranar Yara ta ƙasa da aka gudanar a jihar. Ya kuma jaddada ƙoƙarin gwamnatin wajen samar da manufofi da tsare-tsare domin walwalar yara ƙanana, da kuma hana bautar da su. Hakazalika, ya ce bikin ba zai tsaya a iya gudanar da taro ba kawai, zai ninka ƙoƙari wajen kare rayukansu, da inganta fannin…
Read More
Kwalara ta kashe mutum 27 a Borno

Kwalara ta kashe mutum 27 a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla mutum 27 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a wasu ƙananan hukumomi shida na Jihar Borno, yayin da aka samu mutum 2,715 da ake zargin sun kamu da cutar cikin kwanaki 24 na farkon watan Mayu. Rahoton da aka samu ya nuna cewa cutar ta ɓarke a ƙananan hukumomin Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri, inda birnin Maiduguri ya kasance cibiyar da cutar ta fi ƙamari da mutum 1,568 da ake zargi sun kamu. Rahoton ya ce annobar na ƙara tsananta, yayin da ake ci gaba da samun sabbin masu ɗauke…
Read More
’Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan tara wajen sayen kati da data a 2025 – Rahoto

’Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan tara wajen sayen kati da data a 2025 – Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rahoto ya nuna cewa kwastomomin manyan kamfanonin sadarwa guda huɗu a Najeriya sun kashe kusan Naira tiriliyan 9 wajen sayen kati da data a shekarar 2025, lamarin da ya ƙara yawan kuɗaɗen shiga na kamfanonin. Kamfanin MTN  ya samu sama da Naira tiriliyan 5.3 daga kwastomomi miliyan 90.3, inda ya koma samun riba bayan haraji ta Naira tiriliyan 1.11. Haka kuma Airtel ya samu kusan Naira tiriliyan 3.1 daga kwastomominasa miliyan 60.9. Rahoton ya ce ƙarin kuɗaɗen shiga ya samo asali ne daga ƙaruwar amfani da data, yawaitar amfani da wayoyin zamani da kuma…
Read More
’Yan bindiga sun ƙona fadar sarki da sace mata da yara a Kwara

’Yan bindiga sun ƙona fadar sarki da sace mata da yara a Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu ‘yan bindiga sun kai hari mummunan hari da tsakar dare a garin Yashikira da ke karamar hukumar Baruten a jihar Kwara, inda suka kai farmaki ofishin ‘yansanda da kuma fadar Sarkin Yashikira tare da kona wani bangare na fadar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito. Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 2:00 na dare ranar Litinin, inda suka rika harbe-harbe wanda ya jefa mazauna yankin cikin firgici tare da sa mutane guduwa zuwa dazuka domin tsira. An bayyana cewa maharan sun sace kimanin mutum 10, ciki har…
Read More
2027: Kalubalen da tsofaffin ministocin Tinubu ke fuskantar bayan saukarsu

2027: Kalubalen da tsofaffin ministocin Tinubu ke fuskantar bayan saukarsu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, wasu tsofaffin ministocin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka yi murabus daga Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin neman muƙaman siyasa sun fara fuskantar wata sabuwar ƙalubale ta siyasa. Abin da tun farko aka ɗauka a matsayin wata dabara ta siyasa daga manyan jami’an gwamnatin domin ƙarfafa burinsu na zaɓe, yanzu ya fara bayyana irin tsananin rikicin cikin gida, ƙarfin tsarin jam’iyya da kuma fafatawar maye gurbi a jam’iyyar APC. Ya zuwa yanzu, mutum biyu kacal daga cikin ministoci biyar da suka ajiye muƙamansu bayan…
Read More