30
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gabanin tsayar da ɗan takarar gwamna, rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa, jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi shirin bayyana tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamred Aminu Abdussalam, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar. Idan za a iya tunawa, Abdussalam ya yi murabus daga mukaminsa na mataimakin gwamna a watan Maris na 2026, makonni kaɗan bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano ta aika masa da takardar tsige shi daga muƙamin bayan da ya ƙi amincewa da koma wa Jam’iyyar APC tare da gwamnan jihar, Abba Kabir…
