18
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙara ta’azzara matsalolin rashin tsaro, talauci da yunwa a faɗin Nijeriya. Tambuwal ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi ga wakilai a taron jam’iyyar ADC na jihar Sokoto. A cewarsa, “Na yi imanin cewa ‘yan Nijeriya sun riga sun gani da kansu abin da Bola Ahmed Tinubu zai iya kawowa, idan ma akwai wani abu da aka samu.” Sanatan ya kuma yi zargin cewa ana samun rashin kyakkyawan tafiyar da dukiyar jama’a da kuma karkatar…
