ukarofi

12572 Posts
Gwamnatin Tarayya ta cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci daga tuhume-tuhumen da ake yi wa Malami

Gwamnatin Tarayya ta cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci daga tuhume-tuhumen da ake yi wa Malami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin tarayya ta gyara tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, da ɗansa Abdulaziz, inda ta cire zargin da ya shafi tallafawa ta’addanci kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito. A zaman kotu na ranar Laraba, lauyan Hukumar DSS, Akinlolu Kehinde, ya sanar da kotu cewa an yi wannan gyara, tare da neman a maye gurbin tsohuwar ƙarar da sabuwa. Sabuwar tuhumar ta ta’allaka ne kan mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. Lauyan waɗanda ake ƙara, Shaibu Aruwa, ya tabbatar da cewa an ba su sabuwar takardar ƙarar, kuma ya…
Read More
Dalilin da ya sa ICPC ta ci gaba da tsare El-Rufai duk da samun belin miliyan N200

Dalilin da ya sa ICPC ta ci gaba da tsare El-Rufai duk da samun belin miliyan N200

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a shari’ar cin hanci da rashawa da Hukumar ICPC ke tuhumarsa da ita. Rahotanni sun bayyana cewa alkalin kotun, Mai shari’a Rilwanu Aikawa, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan da ya ɗage sauraron ƙarar daga ranar 1 ga Afrilu zuwa 14 ga Afrilu, 2026 domin nazarin hujjojin ɓangarorin biyu. Kotun ta amince da bayar da belin kan kuɗi Naira miliyan 200, amma ta umarci cewa El-Rufai zai ci gaba da kasancewa a hannun…
Read More
Kwasau ɗin Sarkin ƙaraye ya yi kira ga matasa su ƙara himma wajen neman ilimi da sana’o’in dogaro da kai

Kwasau ɗin Sarkin ƙaraye ya yi kira ga matasa su ƙara himma wajen neman ilimi da sana’o’in dogaro da kai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yi kira ga matasan Jihar Kano da ma na ƙasa baki ɗaya da su ƙara himma wajen neman ilimi, na addinin Musulunci da na zamani, tare da koyon sana’o’in dogaro da kai. Kwasau ɗin Sarkin Karaye, Ambasada Hashim Yahaya Jibrin Mijinyawa ne ya yi wannan kira yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ambasada Hashim Yahaya Jibrin, wanda shi ne shugaban matasan ƙananan hukumomin Gwarzo, ƙaraye, Kabo, Rimin Gado, Bichi, Tsanyawa da Shanono, ya bayyana cewa rashin ilimi a tsakanin wasu matasa na taka rawa sosai wajen amfani da su wajen tayar…
Read More
Karuwar cutar sanƙarau a Arewacin Nijeriya: Lokaci ya yi na ɗaukar matakin gaggawa

Karuwar cutar sanƙarau a Arewacin Nijeriya: Lokaci ya yi na ɗaukar matakin gaggawa

Nijeriya na fuskantar wani sabon ƙalubale mai tsanani a fannin kiwon lafiya, yayin da cutar sanƙarau ke ƙara yaɗuwa a jihohin arewacin ƙasar. Masana kiwon lafiya na gargaɗi cewa alluran rigakafin da ake da su a yanzu ba sa ba da cikakken kariya kan sabon nau’in ƙwayar cutar, wato Neisseria meningitidis nau’i na C, wanda ke bazuwa cikin sauri a yankin. Rahotanni daga Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) sun nuna cewa yara masu shekaru tsakanin ɗaya zuwa goma sha biyar ne suka fi kamuwa da cutar. Haka kuma, cunkoson jama’a da ake samu a lokacin zafi, musamman a…
Read More
2027: Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

2027: Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, ya ce ba zai sake neman takarar shugaban ƙasar daga 2027 ba. Ya ce idan aka yi la'akari da shekarunsa da kuma damar da yake da ita ba lallai ya ci gaba da neman damar daga shekara mai zuwa ba. Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Laraba. Da aka tambaye shi game da cikarsa shekaru 80 a shekarar 2027 da yadda hakan zai iya daƙile masa damarsa, Atiku ya ce: "Tabbas za a samu…
Read More
Hukumar ƙididdiga ta Kano ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a 

Hukumar ƙididdiga ta Kano ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a 

* Ta yaba wa gwamnati kan shirye-shiryen lafiya da ilimi Daga RABIU SANUSI a Kano Daraktan Hukumar ƙididdiga ta Jihar Kano, Dr. Surajo Sulaiman, ya sake jaddada ƙudirin hukumar na ƙara zage damtse wajen wayar da kan al’umma, bunƙasa haɗin kan jama’a, da kuma tallafawa manyan shirye-shiryen ci gaban gwamnati a faɗin jihar. Da yake bayani kan ayyukan hukumar, Dr. Sulaiman ya bukaci al’ummar jihar da su hada kai wajen magance matsalolin da ke addabar yankunansu, yana mai cewa cigaba mai dorewa ba zai samu ba sai da hadin kai da jajircewar jama’a. Ya shawarci al’umma da su rika kafa…
Read More
Gwamnatin Kaduna ta shirya taron wayar da kai kan alaƙar amfani da muggan ƙwayoyi

Gwamnatin Kaduna ta shirya taron wayar da kai kan alaƙar amfani da muggan ƙwayoyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Hana Sha da Kula da matsalolin tabuwan hankali na jihar Kaduna KADSAMHSA ta bayyana cewa ta shirya taro domin wayar da kan mutane domin samar wa mata kariya daga kamuwa da cututtuka kamar su Kanjamau da hepatitis. Shugaban Hukumar Joseph Ike ya sanar da haka a ranar farko na taron tattauna alakar amfani da muggan kwayoyi da kamuwa da cututtuka . Ike ya ce matan dake amfani da muggan kwayoyi na daga cikin rukunin mutanen dake da wahalar samu musamman a Arewacin Nijeriya. Ya ce alkalumar binciken da Cibiyar UNODC da ma’aikatar lafiya…
Read More
Yadda aka gudanar da bikin turaren wuta na shekara-shekara karo na farko a Kano

Yadda aka gudanar da bikin turaren wuta na shekara-shekara karo na farko a Kano

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An gudanar da bikin turaren wuta na shekara-shekara karo na farko a birnin Kano, wanda ya gudana a dakin taro na Meena Event Centre da ke kan titin Lodge, karkashin shirya kamfanin By Ray, a jagorancin shugabar kamfanin, Hajiya Rahanatu Aliyu. Bikin, wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu daga ranar Asabar zuwa Lahadi da ta gabata, ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan, ciki har da sarakuna, attajirai da sauran al’umma. Da take jawabi a wajen bude taron, Hajiya Rahanatu Aliyu ta bayyana cewa babban makasudin shirya bikin shi ne…
Read More
Yadda lauyoyi suke muhawara kan dambarwar korar Nafi’u Bala daga ADC

Yadda lauyoyi suke muhawara kan dambarwar korar Nafi’u Bala daga ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar ADC mai adawa ta sanar da korar tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar wanda ke iƙrarin shi ne halastaccen shugabanta, Nafi'u Bala Gombe tare da wasu 'yan jam'iyyar da ke kiran kansu jagororin jam'iyyar A ƙarshen babban taronta da ta gudanar ranar Talata a Abuja, ADC ta ce ta kori mutanen ne bisa ayyukansu yin zagon ƙasa domin wargaza jam'iyya. Tun bayan da hukumar INEC ta sanar da cire sunan Sanata Daɓid Mark da Rauf Aregbesola daga na'urarta a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar ADC. A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba ta 1…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniyar dala biliyan ɗaya da kamfanin sarrafa ƙarafa na Indiya

Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniyar dala biliyan ɗaya da kamfanin sarrafa ƙarafa na Indiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya (MoU) da wani babban kamfanin sarrafa ƙarafa na ƙasar Indiya mai suna Rashmi Metaliks Group, domin zuba jarin dalar Amurka biliyan daya (kimanin naira triliyan 1.5) a cikin shekara uku. Ministan Raya Fannin Karfe, Prince Shuaibu Abubakar Audu, shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa birnin Kolkata na kasar Indiya, inda aka kulla wannan yarjejeniya bayan ya ziyarci masana’antar kamfanin. Cikin wata sanarwa da Shugabar Sashin Yada Labarai na Ma’aikatar, Salamatu Jibaniya, ta fitar ranar Talata, Minista Audu ya bayyana matakin a matsayin gagarumin ci gaba…
Read More