17
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Alhazai ta Nijeriya, wato NAHCON, ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga al’ummar ƙasar kan yawaitar ‘yan damfara da asusun sada zumunta na bogi da ke ikirarin samar da bizar aikin Hajji, duk da cewa hukumomin Saudiyya sun riga sun rufe bayar da bizar bana. A cewar hukumar, Saudiyya ta rufe bayar da bizar Hajjin shekarar 2026 tun daga ranar 1 ga Shawwal 1447 Hijira (20 ga Maris, 2026), wanda hakan ke nufin an kammala duk wata sahihiyar hanya ta neman bizar aikin Hajji na bana. Hukumar ta bayyana cewa an riga an tantance…
