ukarofi

12618 Posts
Ƙaramar Sallah: Jakadun ƙasashen ƙetare 17 suka halarci bikin hawan sallah a Katsina

Ƙaramar Sallah: Jakadun ƙasashen ƙetare 17 suka halarci bikin hawan sallah a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. Jakadun da suka sauka Katsina ƙarƙashin jagorancin jakadar ƙasar Belgium Mr Peter Leenknegi sun sami tarba daga Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa da mataimakin sa da sauran manyan jami'an gwamnati. Gwamnan ya wuce da jakadun zuwa fadan Sarkin Katsina da ke Kofar Soro a Katsina inda a kai bikin hawan Sallah. Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman da tawagar sa suka fara iso Kofar Soro suna sanye da tufafin gargajiya da yaba jakadun da dubban mutane sha'awa. Haka kuma manyan hakimai fiye da 50 da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya wanda…
Read More
Cire ni daga Sarkin Kano a 2020 bai firgita ni ba – Sarki Sanusi

Cire ni daga Sarkin Kano a 2020 bai firgita ni ba – Sarki Sanusi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa ya kasance cikin natsuwa da jajircewa bayan rasa manyan mukaman da ya taba rike wa a rayuwar jama’a. Sanusi ya yi wannan bayani ne yayin jawabinsa a taron Fola Adeola Annual Ramadan Lecture, inda ya yi magana kan muhimmancin juriya da imani da Allah wajen fuskantar sauye-sauyen rayuwa. Ya ce dogaro da Allah ne ya taimaka masa wajen tsallake mawuyacin lokaci bayan dakatar da shi daga muƙamin gwamnan CBN da kuma cire shi daga sarautar…
Read More
Shugaban ƙaramar Hukumar Funakaye ya yaba da ayyukan ci gaban Gwamna Inuwa

Shugaban ƙaramar Hukumar Funakaye ya yaba da ayyukan ci gaban Gwamna Inuwa

Daga GAMBO ISA a Abuja Shugaban ƙaramar Hukumar Funakaye, Honarabul Shuaibu Abdulrahman Adam, ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa jajircewarsa wajen gudanar da ayyukan ci gaba da kuma shugabanci mai hada kan al’umma a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja kuma aka rabawa manema labarai, shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a fannoni da dama da suka haɗa da bunƙasa jarin ɗan Adam, noma da kiwo, noman rani (irrigation), ilimi, kiwon lafiya, tsaro da kuma gina ababen more rayuwa. Ya kuma jaddada muhimmancin ƙarƙirar ƙananan hukumomin cigaba…
Read More
Yadda jama’ar gari suka kashe ’yan bindiga uku a Sakkwato

Yadda jama’ar gari suka kashe ’yan bindiga uku a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu mazauna da ke aikin sa-kai a ƙauyen Bargaja da ke ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, sun kashe wasu ’yan bindiga uku a wani artabu da ya faru a ranar Lahadi. Rahotanni daga yankin sun ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka kurɗo ta wasu hanyoyi da ke wajen gari domin yi wa al’ummar shigar ba-zata. Wani jagoran al’umma a ƙauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun ɓuya a kan bishiyoyi da ke kusa da maƙabartar ƙauyen, yayin da wasu…
Read More
Kishi: Mace ta goge lamba a wayar mijinta ta janyo masa asarar biliyoyin Naira

Kishi: Mace ta goge lamba a wayar mijinta ta janyo masa asarar biliyoyin Naira

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani lamari mai cike da ruɗani ya ɗauki hankalin jama’a a kafafen sada zumunta, bayan wata mata ta jefa mijinta cikin babbar asarar kasuwanci har ta kai Naira biliyan 7.8, sakamakon zargin cin amana a aurensu. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya fara ne bayan matar ta lura mijinta na yawan mu’amala da wata lamba a wayarsa, lamarin da ya sa ta zargi cewa yana hulɗa da wata mace a ɓoye.  Wannan zargi ne ya sa ta ɗauki mataki cikin gaggawa ta hanyar gogewa don katse hulɗa da wannan lambar, ba tare da cikakken bincike ba.…
Read More
Sojoji sun ƙwato kundin ISWAP mai ƙunshe da tsarin hare-hare a Borno

Sojoji sun ƙwato kundin ISWAP mai ƙunshe da tsarin hare-hare a Borno

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Dakarun rundunar sojin Nijeriya sun samu gagarumar nasara bayan da suka ƙwato wasu littattafan sirri daga hannun mayaƙan ISWAP da aka kashe a yankin Mallam Fatori, jihar Borno, waɗanda ke nuna yadda ƙungiyar ke tsara hare-harenta da rarraba makamai. Rahotanni sun nuna cewa littattafan sun ƙunshi jerin sunayen mayaƙan da aka tura domin kai hari, rawar da kowannensu zai taka, irin makaman da aka ba su, da kuma adadin harsasai da aka ware musu. Wannan na nuna irin tsari mai ƙarfi da ƙungiyar ke da shi wajen gudanar da ayyukanta. Wani masanin harkokin tsaro, Brant Philip,…
Read More
Amurka ta nesanta kanta da harin Isra’ila kan cibiyar gas ɗin Iran

Amurka ta nesanta kanta da harin Isra’ila kan cibiyar gas ɗin Iran

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili ya nesanta ƙasarsa daga harin sama da Isra'ila ta kai kan babbar cibiyar iskar gas ta Iran wato filin South Pars, yana mai cewa Amurka ba ta da hannu a lamarin. A wata sanarwa da aka fitar ta bakin Fadar Shugaban ƙasa ta White House ta hanyar shafin ɗ da kuma manhajar Truth Social, Trump ya bayyana cewa Isra’ila ta kai harin ne cikin fushi sakamakon abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya jaddada cewa Amurka ba ta da masaniya game da harin, tare da ƙara…
Read More
Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin sace ɗalibai a Kwalejin ’Yan Mata ta gwamnati a Bauchi

Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin sace ɗalibai a Kwalejin ’Yan Mata ta gwamnati a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jami’an tsaro sun daƙile wani yunƙurin sace ɗalibai a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati (Government Girls’ College) da ke jihar Bauchi kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa. Wani rahoto daga jaridar Zagazola Makama, wadda ke mayar da hankali kan batutuwan yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Lahadi, 15 ga Maris. Rahoton ya bayyana cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun yi ƙoƙarin shiga harabar makarantar ta wani ɓangare na katangar makarantar da ke kusa da gidajen…
Read More
Tinubu ya zama Shugaban Nijeriya na farko da aka karrama a fadar Windsor Castle

Tinubu ya zama Shugaban Nijeriya na farko da aka karrama a fadar Windsor Castle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nufi birnin London na ƙasar Burtaniya domin gudanar da wata gagarumar ziyarar ban-girma (State Visit), wadda ita ce irinta ta farko da wani shugaban Nijeriya ya kai ƙasar cikin shekara 37. Sarki Charles III da matarsa Sarauniya Camilla ne suka gayyaci Shugaba Tinubu, inda za su karɓe shi da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, a gidan sarauta na Windsor Castle daga ranar Laraba zuwa Alhamis. Wannan ziyara ta kafa tarihi ta fuskoki da dama: Shekara 37: Rabon da wani shugaban Nijeriya ya kai ziyarar aiki irin wannan tun a shekarar…
Read More
Tinubu ya jaddada ƙarfafa dangantakar Nijeriya da Birtaniya a fadar Sarkin Ingila

Tinubu ya jaddada ƙarfafa dangantakar Nijeriya da Birtaniya a fadar Sarkin Ingila

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada muhimmancin dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da ƙasar Birtaniya, inda ya bayyana ta a matsayin alaƙa mai zurfin tarihi, haɗin kai da kuma hangen makomar gobe. Yayin da yake jawabi a liyafar ƙasa da Sarki Charles III ya shirya a Fadar Windsor ranar 18 ga Maris, 2026, Tinubu ya ce babban abin alfahari ne gare shi ya wakilci Nijeriya a wannan wuri mai cike da tarihi, yana mai cewa taron na nuna irin ƙaƙƙarfan alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu. Shugaban ƙasar, wanda ke ziyarar aiki a Birtaniya,…
Read More