ukarofi

12644 Posts
Arewa mai maƙiya da yawa

Arewa mai maƙiya da yawa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Daga bara 2025 kamfen ɗin iƙirarin Hausa zalla ya ƙara bayyana don yadda masu ɗaukar nauyin makircin ke son a yi-ta-ta ƙare duk ko ina ma a ƙona ƙurmus. Siyasar 2023 da a ka yi shelar wai Musulmi da Musulmi ne su ka hau karaga na daga abun da ke ƙonawa ‘yan ƙaryar Hausa zalla rai duk da gaskiyar magana wallahi lamarin na cimma burin siyasa ne ba wai ƙarfin maida Nijeriya ƙasar Musulmi ba. Yo da Nijeriya ƙasar Musulmi ne akwai wani mugu da zai shiga daji ya riƙe makami ya na sace mutane a…
Read More
Zawarci: Wasu mata na guje wa rabuwar aure ne don kada su rasa mu’amular aure – Yabi Muhammadu

Zawarci: Wasu mata na guje wa rabuwar aure ne don kada su rasa mu’amular aure – Yabi Muhammadu

"Mace a gidan miji sarauniya ce komai rashin daɗin gidan auren" Daga AISHA ASAS A 'yan kwanakin baya can, wata baiwar Allah ta aiko da tambayarta a ƙarƙashin Dandalin Shawara wanda muka wallafa a shafin Iyali na wannan jarida. A cikin bayanin ta, ta bayyana irin gallazawar da mijinta ke yi mata, tun daga ɓangaren abinci zuwa taɓa ɓangaren da mata da yawa ba sa iya jurewa wato neman mata, zuwa dai wasu ababe da na manta da su. Saidai a mamakin duk ta yi haƙuri da su, amma fa dalilin nata ne zai fi baka mamaki wato tana yin…
Read More
Hon Khamis ya tallafa wa ɗaliban Dutsinma da Naira miliyan 33

Hon Khamis ya tallafa wa ɗaliban Dutsinma da Naira miliyan 33

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hon. Khamis ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce tallafin ya shafi ɗalibai 231, waɗanda ke karatu a matakai da fannoni daban-daban a faɗin ƙasar nan. Hon Mohammed A Khamis ɗan majalisar dokoki a Katsina mai wakilan ƙaramar hukumar Dutsinma ya ce tallafin zai taimaka wa ɗalibai yan asalin mazaɓarsa wajen biyan kuɗin makarantar su. A cewarsa, a shekarar da ta gabata 2025, an kashe kimanin Naira miliyan 20.8 (₦20,899,000) domin biyan kuɗin karatun ɗalibai 209, waɗanda ke karatu daga matakin SSCE zuwa PhD. Rabon ɗaliban ya haɗa…
Read More
Sojoji sun ƙwato dabbobi 529 daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Sojoji sun ƙwato dabbobi 529 daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A yayin da jami'an tsaro ke ta ƙoƙarin samar da tsaro da zaman lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan, a Jihar Katsina sojojin ayarin Forward Operation Base (FOB) sun samu nasarar ƙwato dabbobi 529 daga hannun 'yan ta'adda, biyo bayan fafata artabu da su a ƙaramar hukumar Kafur ta Jihar Katsina. Laftanar Kanal MM Isa, Kwamandan FOB Malumfashi ya jagoranta, biyo bayan samun sahihan bayanan sirri dangane da ’yan ta’adda a yankin kasuwar Sabo ta ƙaramar hukumar Ƙafur. Ana zargin ’yan ta’addar sun shigo ne daga maƙwabciyar Jihar Zamfara kuma an samu tabbacin cewa…
Read More
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta bai wa Dikko Raɗɗa digirin girmamawa

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta bai wa Dikko Raɗɗa digirin girmamawa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Raɗɗa ya yi alƙawarin ba da ayyukan yi nan take ga ɗalibai mafi hazaƙa. Ya kuma amince da ƙarin albashi ga ma’aikata, da ba da kyautar mota ga ɗalibi mafi hazaƙa a taron yaye ɗalibai na (UMYUK). Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa yabfaɗi haka bayan da jami'an ta karrama shi da digirin girmamawa na Dakta a fannin gudanar da harkokin jama’a (Public Administration) a Katsina. Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan karramawa a matsayin kira na ƙara jajircewa wajen hidima, tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa jami’ar jihar, wadda ya bayyana a matsayin cibiyar…
Read More
Yadda APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Yadda APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Daga UMAR GARBA a Katsina Jam'iyyar APC mai ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa. Babban sakataren jam'iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Jam'iyyar ta saka ranakun 27 da 28 ga watan Maris na wannan shekarar a matsayin ranakun da za ta gudanar da babban taronta na ƙasa. Surajudeen Basiru ya ce a yanzu gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar zai yi aiki a matsayin ma'ajin kwamitin…
Read More
Sabbin takardun Epstein da girman abinda yake ƙunshe a ciki

Sabbin takardun Epstein da girman abinda yake ƙunshe a ciki

Daga AISHA ASAS Fitar da sabbin takardu sama da miliyan uku kan shari'ar Jeffrey Epstein ya sake zama batu mafi tattaunawa a kafafen sada zumunta tare da tayar da hankulan al'umma fiye da ƙima, wanda hakan ya sa ya kasance lamarin da ya fi komawane tashe a wannan makon. Haka muka ya zama abu da ya sanya ɗimbin tambayoyi a zukatan dubatan mutane daga koina a faɗin duniya. Duk da cewa, Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta bayyana wannan bankaɗo takardun da ta yi a matsayin babban mataki na yunƙurin bayyana gaskiya, saidai masana doka da kuma shahararrun 'yan jaridu da…
Read More
Guterres ya sake matsa wa Isra’ila lamba kan kai agaji Gaza

Guterres ya sake matsa wa Isra’ila lamba kan kai agaji Gaza

Babban sakataren Majalisar ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya sake kiran Isra’ila da ta gaggauta ba da damar shigar da kayan agaji Gaza, yana mai cewa abin da ke faruwa a yankin ya wuce rikicin siyasa zuwa bala’i na rashin jinƙai na duniya. Duk da sake buɗe mashigar Rafah, alkaluma daga hukumomin jinƙai sun nuna cewa adadin mutanen da ke fita domin neman magani ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da buƙatar da ke akwai. Dubban marasa lafiya, musamman yara da tsofaffi, na jiran damar fita yayin da lokaci ke kara kurewa. Manyan jaridun duniya sun ruwaito cewa kusan dukkan…
Read More
Sojojin Amurka sun harbo jirgin Iran marar matuki a Tekun Arabiya

Sojojin Amurka sun harbo jirgin Iran marar matuki a Tekun Arabiya

Amurka ta ce ta harbo wani jirgin Iran marar matuƙi bayan ya kusanci jirgin yaki USS Abraham Lincoln, lamarin da ya sake tunatar da duniya irin kaifin rikicin da ke iya tashi a Gabas ta Tsakiya. Masu sharhi na tsaro sun bayyana cewa duk da iƙirarin kare kai, irin waɗannan matakai na ɗauke da saƙon siyasa ga Tehran, musamman a daidai lokacin da ake kokarin buɗe sabon shafin tattaunawa kan shirin nukiliya. Duk da haka, ɓangarorin biyu sun nuna cewa ba sa son rikicin kai tsaye, abin da ke nuna cewa har yanzu diflomasiyya na da muhimmiyar rawa.
Read More
Sojojin Pakistan sun kashe ‘yan bindiga 145 bayan kai masu hari

Sojojin Pakistan sun kashe ‘yan bindiga 145 bayan kai masu hari

Sojojin Pakistan sun ce sun kashe ’yan bindiga 145 bayan hare-haren da suka kashe kusan mutane 50. Wannan na daga cikin mafi girman hare-haren ramuwar gayya da gwamnati ta taɓa kaiwa a yankin. Jaridun duniya sun bayyana cewa rikicin Balochistan ya samo asali ne daga korafin rashin adalci, rabon arziki da siyasar tsakiya, wanda ke kara rikitar da matakan soja. Pakistan ta sake zargin Indiya da Afghanistan, yayin da kasashen ke musanta hannu a cikin kowanne irin rikici da ƙasar ke fuskanta.  Saidai duk da hakan lamarin na kara tsananta rikicin diflomasiyya a yankin Kudancin Asiya.
Read More