ukarofi

12715 Posts
Karfafa jarin bankuna zai ɗora Nijeriya kan hanyar tattalin arzikin Dala tiriliyan ɗaya – CBN

Karfafa jarin bankuna zai ɗora Nijeriya kan hanyar tattalin arzikin Dala tiriliyan ɗaya – CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa tsarin ƙarfafa jarin bankuna da ake aiwatarwa a yanzu ba kawai don bin ƙa’idar doka ba ne, amma wani mataki ne na dabarar ƙasa da nufin ƙarfafa tsarin kuɗi, tabbatar da juriya, da shirya bankunan ƙasar wajen taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin tattalin arzikin Dala Yiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030. Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da Tsarin Kuɗi, Philip Ikeazor, ne ya bayyana haka a Abeokuta, Jihar Ogun, yayin taron shekara-shekara na Association of Corporate Affairs Managers of Banks (ACAMB), inda ya ce wannan mataki “alama ce…
Read More
Tsaro da abinci: Gwamnatin Tarayya za ta gyara da gina sabbin dam a faɗin ƙasar – Minista

Tsaro da abinci: Gwamnatin Tarayya za ta gyara da gina sabbin dam a faɗin ƙasar – Minista

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na gyarawa tare da gina sabbin madatsun ruwa (dams) a sassa daban-daban na ƙasar domin ƙarfafa noma ta hanyar ban ruwa da kuma samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa. Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin da yake jagorantar Babban Sakataren Ma’aikatar, Mista Richard Pheelangwah, da wasu daraktoci na fasaha a ziyarar duba ayyukan Azare–Jere Irrigation Project da Gurara Multipurpose Dam a Jihar Kaduna. Farfesa Utsev ya ce wannan shiri yana daga cikin muhimman ayyukan da Shugaban ƙasa Bola Ahmed…
Read More
Sarkin Musulmi ya ba wa makarantu tallafin N1.3bn a Kebbi

Sarkin Musulmi ya ba wa makarantu tallafin N1.3bn a Kebbi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya samu rakiyar Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya miƙa kayan ne a hukumance a ranar Litinin ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, a Bulasa Warehouse da ke kusa da Birnin…
Read More
NNPP ta zargi Kwankwaso da yin sanadiyyar fitar Kofa da Oguntoyinbo daga jam’iyyar 

NNPP ta zargi Kwankwaso da yin sanadiyyar fitar Kofa da Oguntoyinbo daga jam’iyyar 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ce ficewar dan majalisa Abdulmuni Jibrin Kofa zuwa jam’iyyar APC da kuma Amb. Oluremi Oguntoyinbo zuwa jam’iyyar PDP ta faru ne sakamakon zagon ƙasa da cin amana da Sanata Rabiu Kwankwaso ya aikata. Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin martaninta kan sauyin sheka da wasu daga cikin mambobinta suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP. A tuna cewa, Kofa, a ranar Litinin, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC tare da bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027. Haka kuma, tsohon…
Read More
Hanyoyin diflomasiyya da muka ɗauka na aiki tsakanin Nijeriya da Amurka – Minista Idris

Hanyoyin diflomasiyya da muka ɗauka na aiki tsakanin Nijeriya da Amurka – Minista Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa hanyoyin diflomasiyya suna aiki yadda ya kamata wajen daidaita dangantaka tsakanin gwamnatin Nijeriya da ta Amurka. Idris ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin “The World With Yalda Hakim” na gidan talbijin ɗin Sky News da ke Birtaniya, inda ya ce, “An buɗe hanyoyin sadarwa, kuma zan iya tabbatar da hakan; muna magana da su, kuma ina ganin suna fara fahimtar halin da ake ciki. Muna ganin cewa yawancin bayanan da suke samu sakamakon rashin…
Read More
’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum huɗu a Sakkwato

’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum huɗu a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su…
Read More
Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu

Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Nijeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed…
Read More
Kyakkyawan shugabanci shi ne ginshiƙin cigaban aiki – Musa Makama

Kyakkyawan shugabanci shi ne ginshiƙin cigaban aiki – Musa Makama

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An bayyana cewa kyakkyawan shugabanci da jagoranci nagari sune ginshiƙan samun ci gaba a kowanne wurin aiki.  Wannan bayani ya fito ne daga bakin Daraktan Mulki na ƙaramar Hukumar Minjibir, Alhaji Ahmad Musa Makama, a lokacin da Cibiyar Wayar da Kan Al’umma da Kyakkyawan Shugabanci ta karrama shi da lambar yabo saboda jajircewarsa wajen gudanar da aiki da gaskiya da rikon amana. An gudanar da bikin karramawar ne a ofishin Daraktan dake sakatariyar karamar hukumar Minjibir, ranar Litinin da ta gabata. A yayin taron, Alhaji Makama ya bayyana cewa nasara da ci gaba a…
Read More
Yadda ‘yan bindiga ke tilasta wa manoma biyan haraji kafin girbe amfanin gona a Zamfara

Yadda ‘yan bindiga ke tilasta wa manoma biyan haraji kafin girbe amfanin gona a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu manoma a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Nijeriya sun ce 'yan bindiga sun tilasta masu biyan haraji kafin girbe amfanin gonarsu. Mazauna yankin ƙananan hukumomin Tsafe da Talatar Mafara a jihar Zamfara sun ce 'yan bindigar sun mayar da yanzu gonaki wurin da suke kai hari, lamarin da ya jefa manoman yankin cikin tsoro da fargaba. Wasu al'ummar yankin sun shaida wa BBC cewa sun biya 'yan bindigar maƙudan kuɗi kafin suka amince suka girbe abin da suka shuka. "Na biya naira dubu 50 a gonata sannan aka bari na…
Read More
Nijeriya ta fi yawan yara masu fama da rashin abincin mai gina jiki a duniya, inji MSF

Nijeriya ta fi yawan yara masu fama da rashin abincin mai gina jiki a duniya, inji MSF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa, Médecins Sans Frontières (MSF) ta bayyana cewa ta kula da yara masu fama da rashin abincin dake gina jiki mafi yawa a Nijeriya. Shugaban ƙungiyar Ahmed Aldikhari ya ce likitocin kungiyar sun kula da yara kusan 300,000 dake fama da matsalar a jihohin dake Arewacin Nijeriya a shekarar 2024. Aldikhari ya faɗi haka ne a taron tattauna hanyoyin yakan yunwa a jikin yara ƙanana a jihar Katsina da jihohin dake Arewa maso Yamma wanda gwamnatin jihar Katsina da MSF suka shiyar Kuma aka yi ranar Alhamis a Abuja.…
Read More