15
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Tsofaffin Sojoji ta Nijeriya ta buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen inganta rayuwar mata zawarawan sojojin da suka mutu a bakin aiki tare da ba su goyon bayan da ya dace. Sabon shugaban ƙungiyar a Jihar Bayelsa, Mista Baratuaipre Allison-Alamini, ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan rantsar da shi. Ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari ganin cewa muryar zawarawan sojojin da suka rasu ta isa inda ya kamata, ta yadda za a inganta rayuwarsu da kuma tabbatar da samun tallafin da suka cancanta. Allison-Alamini ya kuma sha…
