ukarofi

12715 Posts
Sarkin Kabin Argungu ya ’yanta fursunoni 12

Sarkin Kabin Argungu ya ’yanta fursunoni 12

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  A cikin shagalin murnar cikarsa shekaru 29 da hawa karagar mulkin daular Masarautar Kabin Argungu, Mai Martaba Alhaji Sama'ila Muhammad Mera, ya ziyarci gidan yari mai matsakaicin tsaro da ke garin Argungu, inda ya 'yanta fursunoni 12 masu ƙananan laifuka da kuma waɗansu da wannan wannan shi ne karon farko da aka tsare su. Da ya ya ke jawabi a yayin ziyarar, mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama'ila Muhammad Mera, bayan addu'o'i na musamman ga waɗanda ke tsare a gidan ya kuma ya hankalin su a matsayin su na Musulmi da su mayarda duk…
Read More
An hana ’yan ci-rani 332 shiga Nijeriya ta iyakar Seme – NIS

An hana ’yan ci-rani 332 shiga Nijeriya ta iyakar Seme – NIS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta hana wasu ‘yan ci-rani 332 shiga ƙasar nan ta iyakar Seme, bayan da aka gano ba su da sahihan takardun tafiya. Kwamturola Janar ta Hukumar, Kemi Nandap, ce ta bayyana haka a Abuja ranar Talata, yayin taron wayar da kai ga masu ruwa da tsaki mai taken “Evolving Patterns in Smuggling of Migrants: Towards a Coordinated National Response.” Nandap ta ce, hukumar ta ƙarfafa tsarin doka da horar da jami’anta don ƙara inganta bincike da hana harkar safarar mutane da shige da ficen ba bisa ƙa’ida ba. “Kwanan…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta bayyana raguwar mace-macen mata da jarirai a Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana raguwar mace-macen mata da jarirai a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta sanar da samun gagarumar nasara a gyaran tsarin kiwon lafiya, inda ta ce an samu raguwar mace-macen mata masu juna biyu da kashi 17%, tare da raguwar mace-macen jarirai da kashi 12% a faɗin ƙasar, musamman a cikin ƙananan hukumomi 172 da ke da matsalar yawan mace-mace. Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na ma’aikatar da aka gudanar a Abuja, ranar Laraba. Farfesa Pate ya bayyana cewa, za a gudanar da Bita na Shekara-shekara na haɗin gwiwa domin tantance cigaban da aka…
Read More
Manufofin Tinubu za su daidaita arzikin Nijeriya mai ɗorewa – CBN

Manufofin Tinubu za su daidaita arzikin Nijeriya mai ɗorewa – CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki da sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa — duk da cewa suna haifar da ƙalubale na ɗan lokaci — suna da matuƙar muhimmanci wajen daidaita tattalin arzikin ƙasar bisa turbar ci gaba mai ɗorewa. Cardoso ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Abuja, yayin gabatar da jawabin buɗe taro a taron shekara-shekara na manyan jami’an CBN na 2025, mai taken “Deepening Reforms: Path to Diversification and Sustainable Growth.” Ya ce, taken taron ya zo a lokaci mai muhimmanci kuma…
Read More
Dalilin da ya sa Tinubu ba zai tsoma baki a shari’ar Nnamdi Kanu ba – Fadar Shugaban ƙasa

Dalilin da ya sa Tinubu ba zai tsoma baki a shari’ar Nnamdi Kanu ba – Fadar Shugaban ƙasa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai yi wani mataki ko magana kan shari’ar da ke gaban kotu ta shugaban ƙungiyar da aka haramta ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ba. Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin hulɗa da al’umma na yankin Kudu maso Gabas, Chioma Wesley, ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa, Abuja, a ranar Litinin, bayan ta da wasu mataimaka uku daga sauran yankuna sun yi wa Shugaban ƙasa bayani kan aikinsu. Ta ce, “Shari’ar Nnamdi Kanu tana…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe tiriliyan N1 wajen ayyukan hanya

Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe tiriliyan N1 wajen ayyukan hanya

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ta amince da kashe fiye da naira tiriliyan 1.04 domin gudanar da manyan ayyukan gina hanyoyi a sassa daban-daban na ƙasar. Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ƙarshen mako, inda ya ce Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da wannan kuɗin ne a zaman ta na ranar 6 ga Nuwamba, 2025. A cewar Umahi, cikin ayyukan da aka amince da su akwai: Sokoto–Badagry Coastal Superhighway (Sashen 3, daga Badagry zuwa iyakar Ogun–Oyo) mai tsawon kilomita 163,…
Read More
MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC

MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ƙungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta buƙaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Nijeriya. Manhaja ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne sananne cewa ana aikata laifuka a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa a Nijeriya, musamman laifukan da suka shafi cin zarafin bil’adama, laifukan yaƙi da kuma kisan ƙare dangi.” Ya ƙara da cewa: “Kalma guda da hukumomin Nijeriya da masu…
Read More
Shirye-shiryen gwamnatin Nijeriya ba su rage talauci ba – Bankin Duniya

Shirye-shiryen gwamnatin Nijeriya ba su rage talauci ba – Bankin Duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Bankin Dunya ya ce kuɗaɗen kasafin da gwamnatin Nijeriya ke kashewa kan shirin walwalar jama'a bai kai yawan na sauran ƙasashen hamadfar Afirka ba kuma bai yi wani tasiri wajen talauci ba a ƙasar. Cikin wani sabon rahoto, bankin ya ce kasafi na 0.14 cikin 100 na arzikin cikin gida na Nijeriya bai kai 1.1 ba da sauran ƙasashen Afirka suka saba warewa duk shekara domin inganta rayuwar 'yan ƙasarsu. Rahoton wanda ya duba dukkan shirye-shiryen da gwamnatin Nijeriya ke aiwatarwa, ya nuna cewa talauci ya ragu ne da maki 0.4 kacal a Nijeriya.…
Read More
Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro

Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tare da shugabannin Rundunonin Sojin Nijeriya, za su ci gaba da kare duk wani jami’i da ke gudanar da aikinsa bisa doka. Badaru, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a taron da aka shirya domin bikin tunawa da Sojojin Nijeriya na shekarar 2026 a Abuja. Wannan na zuwa ne bayan ce-ce-ku-cen da ya faru ranar Talata tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima. An yi taƙaddama ne kan wani fili…
Read More
Barazanar da rigakafin cutar shan inna ke fustanta a Nijeriya

Barazanar da rigakafin cutar shan inna ke fustanta a Nijeriya

A shekarar 2020, Nijeriya ta rubuta tarihi da ruwan zinariya bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa an kawar da cutar shan inna (wild poliovirus) daga ƙasar gaba ɗaya. Amma shekaru kaɗan bayan haka, wannan nasara mai girma na fuskantar barazana — ba daga ƙwayar cutar kanta ba, sai dai daga ƙin amincewar jama’a da rigakafi sakamakon rashin gaskatawa da yaɗuwar bayanan ƙarya. ƙididdiga daga bikin Tanar Yaƙi da Cutar Shan Inna ta Duniya na baya-bayan nan sun nuna gagarumin koma baya: sama da gidaje 3,000 a jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara sun ƙi bari a…
Read More