14
Nov
*Ba gudu ba ja da baya, inji jam'iyyar *Saraki ya nemi a tsahirta Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar jam'iyyar adawa a Nijeriya, PDP, tana ci gaba da ninƙaya cikin wutar rikici bayan da kotuna daban-daban ke bayar da mabambantan hukunce-hukunce game da babban taronta na ƙasa. A ranar Talata wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sake dakatar da jam'iyyar daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jihar Oyo. Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam'iyyar hamayyar ke shirin yi…
