ukarofi

12715 Posts
Kotu a Kano ta umarci ‘yan sanda su binciki Abdullahi Abbas kan zargin kalaman ɓatanci ga al’ummar Fagge

Kotu a Kano ta umarci ‘yan sanda su binciki Abdullahi Abbas kan zargin kalaman ɓatanci ga al’ummar Fagge

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Babbar Kotun Majistare mai lamba 5 da ke Court Road, Kano, ta ba da umarni ga Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano da ya gudanar da bincike kan Abdullahi Abbas, shugaban jam'iyyar APC na Kano bisa zargin yin kalaman ɓatanci , tunzuri da kuma maganganun da ka iya haifar da ƙiyayya tsakanin al’umma, musamman a yankin Fagge. Fitaccen lauya mai rajin kare ƴancin ɗan Adam, Abba Hikima ne ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook. Ya ce masu shigar da ƙorafin sun haɗa da wasu fitattun malamai, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma, waɗanda suka…
Read More
Tsadar rayuwa yana durƙusar da kafafen yaɗa labarai

Tsadar rayuwa yana durƙusar da kafafen yaɗa labarai

*Tinubu ya amince da rangwamen haraji ga gidajen jarida *Gwamnatin Tarayya ba ta tsangwamar manema labarai, inji Idris Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI MUSA MUH’D Shugaban ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE), Kwamred Eze Anaba, ya koka kan yadda tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki suke hana kafafen yaɗa labarai gudanar da aikinsu yadda ya kamata, yana mai roƙon Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan tallafi, don ceto masana’antar da ke fuskantar barazanar rushewa. Yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara na 21 na ƙungiyar Editoci ta Nijeriya (ANEC), wanda aka gudanar a Dakin Taron Fadar Shugaban ƙasa a Abuja, Anaba ya…
Read More
Rashin kishin ƙasa ne murnar barazanar Amurka kan Nijeriya

Rashin kishin ƙasa ne murnar barazanar Amurka kan Nijeriya

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Sam ba mu yi mamaki da wasu marar sa kishin ƙasa da ke zaman ‘yan kwangilar rusa Arewa su ka ɓarke da sowa kamar yadda a ke yi in an sha ƙwallo yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya jefa sunan Nijeriya a bakin littafin Amurka da tuhumar yi wa mabiya addinin Kirista kisan kare dangi. Dama aikin ‘yan kwangila shi ne jawo fitina ta ‘yar gaba ɗaya ga Nijeriya musamman Arewa. Asalin wanda ya mika ƙorafi Amurka Bishop Wilfred Chikpa Anagbe ya na magana kan jihar Binuwe ne, ya yi ta bayanai har ya fake…
Read More
APC a Zamfara ta zargin PDP da haifar da rikici yayin ziyarar Matawalle

APC a Zamfara ta zargin PDP da haifar da rikici yayin ziyarar Matawalle

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jami'ar All Progressive Congress reshen Jihar Zamfara ta koka kan abin da ta bayyana da zargin shirin da gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ƙarƙashin jagorancin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ke yi na kawo ruɗani da kuma haifar da rikici a lokacin ziyarar ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Mohammed Matawalle zuwa jihar. Jam'iyyar ta sanar da cewa Ministan zai kawo ziyara ta kwanaki uku a jihar. Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar Yusuf Idris ya yi wannan tsokaci a wani taron manema labarai kafin ziyarar Minista Matawalle da aka shirya yi gobe. "Dangane da rahoton da jam'iyyar…
Read More
Remi Tinubu ta raba kayan tsaftar jinin al’ada ga ɗalibai mata a Zamfara

Remi Tinubu ta raba kayan tsaftar jinin al’ada ga ɗalibai mata a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta raba kayan tsaftar jinin al'ada ga ɗalibai mata a makarantun sakandare don inganta lafiyar su. Sanata Oluremi Tinubu wadda matar gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta wakilta, ta bayyana cewar, a ƙarƙashin wannan shiri, za a rarraba kayan tsaftar jinin al’ada ga ‘yan mata 370,000 a faɗin ƙasar nan. Hakazalika ta bayyana cewar, kowace jiha da babban birnin tarayya za su samu kunshi 10,000 na kayan tsafta. A cewar ta, wannan taimako ne musamman ga ‘yan mata na ƙauyukka da ba su da ƙarfin sayen kayan…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane 20 bisa zargin fyaɗe

‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane 20 bisa zargin fyaɗe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Waɗannan da aka kama na daga cikin mutane 120 da rundunar 'yan sandan suka kama kan laifuka daban daban. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a hira da manema labarai a ofishin sa. Ya ce haka kuma a cikin waɗanda da aka kama mutane 18 ana zargin su da fashi da makami sai wasu 28 da ake zargi da laifin kisan kai, da mutum 28 da suma ake zargi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi. DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa waɗannan da aka…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta taimaka wa matasa domin su dogara da kansu

Gwamnatin Katsina za ta taimaka wa matasa domin su dogara da kansu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana haka ta bakin Mataimakin Malam Faruk Lawal Joɓe, a lokacin da yake ƙaddamar da buɗe taron na ƙungiyoyin matasa. Taron mai taken alfanu da matasa suka samu daga gwamnati da kuma hanyoyin da ya kamata subi wajen bayyana manufofin Gwamnatin domin cigaban al'umma. Ma'aikatar matasa da wasannin da ofshin mai bai wa gwamna shawara akan harkokin matasa Dakta Abubakar Tsanni suka shirya taron. Da yake gabatar da jawabin shi Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa" Gwamnatin Katsina, ta sake yin kyakkyawan shiri, wanda zai sake taimaka wa…
Read More
Amazons: Dakaru mata zalla a daular Dahomey

Amazons: Dakaru mata zalla a daular Dahomey

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A yau ma dai jaridar Manhaja ta sake binciko wani ƙayataccen tarihin da ba kowa ya san da zamansa ba, wannan tarihi na wasu jaruman dakarun mata mayaƙa ne da aka yi a Dahomey, waɗanda aka fi sani da ‘Amazons’ a bayyana. Ficen da masarautar Dahomey ya yi tsakanin karni na 17-19, da a yau ake kira Jamhuriyar Benin, ya samu ne saboda kafa wata rundunar mayaƙa da ta ƙunshi mata zalla, waɗanda ake kira ‘Dahomey Amazon’. Yankin Dahomey wanda ke a ƙasar da ake kira Benin a yau, yanki ne mai ɗumbin tarihi daga cikin…
Read More
2027: Zamanin ɗauki ɗora na ‘yan takara ya ƙare a Zamfara – Shinkafi

2027: Zamanin ɗauki ɗora na ‘yan takara ya ƙare a Zamfara – Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD. Gusau Jigo a jam'iyyar All Progressive Congress APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya sake jaddada cewa zamanin da ake ɗauki ɗorar 'yan takara a ƙarƙashin jam'iyyar a jihar ya ƙare, musamma a zaɓen shekarar 2027. Ya yi wannan sanarwar a wani taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyar Wamban Shinkafi Democratic Front ta shirya a Gusau yau Talata. "Lokacin da ake ɗauki ɗorar 'yan takara a ƙarƙashin babbar jam'iyyarmu ta APC ya kawo ƙarshe musamman a babban zaɓen 2027 mai zuwa. Ba zamu sake amince wa da shi ba kuma dole ne a bai…
Read More
Ilimi shi ne ke ba mace damar tsayawa da ƙafarta ko an juya mata baya – Sarauniya Cleopatra

Ilimi shi ne ke ba mace damar tsayawa da ƙafarta ko an juya mata baya – Sarauniya Cleopatra

Idan mace ta san darajar kanta, duniya za ta san darajar ta - Sarauniya Cleopatra Daga AISHA ASAS Idan kuna neman macen da za a iya cewa ta haɗa komai da mata ke burin samu na daga kyau, farin jini da kuma mulki. Macen da za mu iya cewa mai kamar maza, wani sa'in ma har ta fi wasu mazan. Cleopatra ta kasance sarauniyar da ta kafa tarihin da har yau ba a samu wadda ta maye gurbinta ba, saidai a samu masu kusa da ita.  A ɓangare guda, za mu iya cewa, ta aikata ababe na ƙarfin hali da…
Read More