ukarofi

12715 Posts
Ranbir Kapoor zai farfaɗo da gidan fim na RK Studios da aka kafa a 1948

Ranbir Kapoor zai farfaɗo da gidan fim na RK Studios da aka kafa a 1948

Daga AISHA ASAS  Shahararren jarumin Bollywood, Ranbir Kapoor, ya sanar da fara aikin farfaɗo da gidan fim mai ɗinbin tarihi na RK Studios, wanda kakansa Raj Kapoor ya kafa a shekarar 1948 a Mumbai. Gidan ya kasance cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire, inda aka samar da fina-finai masu tarihi da suka shahara a duniya baki ɗaya, kamar 'Barsaat' (1949), 'Awaara' (1951), 'Mera Naam Joker' (1970), 'Bobby' (1973), 'Satyam Shivam Sundaram' (1978), 'Prem Rog' (1982), da 'Ram Teri Ganga Maili' (1985).  Wannan aikin na farfaɗo da gidan na nuni da yadda Ranbir ke son haɗa gado da ƙirƙire-ƙirƙire na zamani, domin bai wa masana’antar…
Read More
BON Awards 2025: An fito da jerin sunayen da za su fafata 

BON Awards 2025: An fito da jerin sunayen da za su fafata 

Daga AISHA ASAS  A wani muhimmin mataki na cigaba a masana’antar fim ta Kudu, wato Nollywood shi ne yadda taron Best of Nollywood Awards (BON Awards) ke ƙara samun tagomashi da kuma ƙwarewa, inda a bana ma suka ɗaura aniyyar gabatar da shi cikin ƙwarewa da kuma adalci. Rahotanni bayyana cewa, yanzu haka an bayyana sunayen yan takara a kowane ɓangare inda aka bayyana fim ɗin 'Seven Doors' a matsayin fim ɗin da ya shiga ɓangare har tara don fafatawa, wanda hakan ma babbar nasara ce ga fim ɗin tun a matakin farko. Fim ɗin 'Abanisete ya biyo baya da shiga guraben takara takwas, yayin…
Read More
Gwamnatin Katsina ta musanta jita-jitar rikici a wasan Katsina United da Barau FC

Gwamnatin Katsina ta musanta jita-jitar rikici a wasan Katsina United da Barau FC

Daga UMAR GARBA a Katsina A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Katsina, Injiniya Sirajo Yazid Abukur, ma’aikatar ta bayyana cewa labarin da ake yaɗawa cewa magoya bayan Katsina United sun tayar da tarzoma a lokacin wasan su da Barau FC ba gaskiya ba ne. Ma’aikatar ta ce bayan cikakken bincike daga jami’an tsaro, jami’an wasan, da masu sa ido masu zaman kansu, babu wani abu da ya nuna an samu tashin hankali ko jikkata mutum. An tabbatar cewa wasan ya gudana cikin kwanciyar hankali, inda magoya baya daga ɓangarorin biyu suka…
Read More
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi ya sami ‘yanci

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi ya sami ‘yanci

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ƙarshen makon nan ne mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Kebbi Honarabul Sama'ila Muhammad Bamboo ya sami kan sa bayan kwashe sama da sati ɗaya hannun masu garkuwa da mutane da suka tafi da shi tun ranar Juma'ar da ta gabata. Bayanai daga fadar gwamantin jihar ta Kebbi sun bayyana cewa an sako mataimakin Kakakin majalisar ne a ƙarshen makon nan sai dai babu wani cikakken bayani dangane da ko an kai kuɗin fansa ko kuma nawa ne aka kai don fansar sa. Bayanan dai sun nuna cewa yanzu haka dai yana wata asibiti da ita…
Read More
Ƙaramar Hukumar Mai’adua ta bada Naira Miliyan 30 ga masu ƙananan sana’o’i

Ƙaramar Hukumar Mai’adua ta bada Naira Miliyan 30 ga masu ƙananan sana’o’i

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tallafin kuɗin za a raba shi ga matasa maza da mata masu ƙananan sana'o'i su 3000 da suka fito daga lungu da saƙo na karamar hukumar Mai'adua, inda ko wannan su zai amfana da kudi Naira 10,000. Da yake gabatar da jawabin shi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ta bakin Hon. Ibrahim Yusuf Jirdede ya bayyana cewa" Tallafin kuɗin zai taimaka ma masu ƙananan sana'o'i domin su yi dogaro da kai. Ya yabawa shugaban ƙaramar hukumar akan bada tallafin kuɗin ga al'ummar shi domin dogaro da kai. "Wannan abin alheri babu shakka zai taimaka…
Read More
Bai kamata ‘yan kannywood su rinƙa ƙauracewa KILAF AWARD ba – Ali Nuhu

Bai kamata ‘yan kannywood su rinƙa ƙauracewa KILAF AWARD ba – Ali Nuhu

DAGA MUKHTAR YAKUBU Fitaccen jarumi kuma shugaban hukumar fim ta ƙasa Ali Nuha ya nuna damuwar sa a game da ƙauracewa KILAF AWARD da 'yan fim na Arewa musamman 'yan Kannywood.Ali Nuhu ,ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wajen taron karrama jarumai na KILAF AWARD 2025 da aka yi a daren jiya Asabar 8 ga Nuwamba a ɗakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kano. Tun da farko dai Ali Nuhu ya jinjinawa masu shirya taron ganin sun daɗe suna yi wanda har an zo karo na 8 in da yake cewa " Dole ne a yi jinjina ga…
Read More
Fim ɗin Kakanda ne gwarzon fim na gasar KILAF Award 2025

Fim ɗin Kakanda ne gwarzon fim na gasar KILAF Award 2025

DAGA MUKHTAR YAKUBU Sakamakon gasar fina-finai ta KILAF AWARD 2025 da aka sanar a daren jiya Asabar 8 ga Nuwamba 2025 an bayyana fim ɗin Kakanda ne ya kasance gwarzon fim na wannan shekarar inda ya yi fice a cikin fina finai masu yawa da suka shiga gasar daga ƙasashe daban daban na duniya da aka yi su da yare da kuma al'adun mutanen Afrika. Taron wanda aka yi shi a babban ɗakin taro na gidan gwamnatin Jihar Kano mai taken Night Award ya samu halartar manyan mutane daga nan gida Nijeriya da ƙasashe daban daban na Afrika. Tun da…
Read More
Zauren shugabannin hukumomin gwamnatin Kano sun yarjewa Abba sake tsayawa takarar gwamna

Zauren shugabannin hukumomin gwamnatin Kano sun yarjewa Abba sake tsayawa takarar gwamna

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban zauren Tukur Bala ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina wanda ɗaukacin shugabannin hukumomin suka halarta. Tukur Bala wanda babban daraktan hukumar yawon buɗe ido na jihar Kano ya ce cigaba da aka samu a tsawon mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano yasa suka ga wajibi ne su kira wannan taron su nuna goyon bayan su ga Abba domin ya sake tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar. Tukur ya ce da hawan gwamna Abba Yusuf mulkin ya kafa dokar ta ɓaci kan harkar ilimi a jihar. "Wanda sakamakon haka…
Read More
Ɗalibai 17,000 suka amfana da tallafin Gidauniyar Lado Ɗanmarke

Ɗalibai 17,000 suka amfana da tallafin Gidauniyar Lado Ɗanmarke

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sakataren Gidauniyar Muhammad Ghali Bakori ya shaidawa manema labarai a cikin jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma wajen da Gidauniyar ta gama tantance ɗalibai 1,500 da za biya masu kuɗin makaranta. Ya ce Gidauniyar ta zaɓo ɗaliban waɗanda yan asalin jihar Katsina ne daga manyan makarantu na jihar da ma na wasu jihohi domin biya masu kuɗin makaranta. "Makarantun sun haɗa da jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma da jami'ar Umaru Musa Yar'adua da kuma makarantar kimiya da fasaha na Hassan Usman da sauran su,"Ghali ya ce. Ya ƙara da cewa akwai jami'ar ABU Zaria…
Read More
Zuwa ga masu neman matan aure ta hanyar fasiƙanci

Zuwa ga masu neman matan aure ta hanyar fasiƙanci

Ku karanta wannan wasiƙa cikin natsuwa. Wannan wasiƙa ce ga duk wani mutum — ko da ma’aikaci ne, ko malami, ko limami, ko ɗan kasuwa, ko jami’in gwamnati, ko ɗan siyasa — wanda ya zama mai neman mata, musamman matan aure, ta hanyoyi marasa daraja: ta hanyar yaudara, amfani da matsayin addini, amfani da iko, turo saƙonni marasa kyau, neman hotuna, ko karya amana. Wannan wasiƙa ba wai ta nuna-hannu ce ga mutum guda ba; kira ce ga al’umma baki ɗaya da kuma gargaɗi ga masu irin wannan hali su daina nan take, su gyara, ko su fuskanci sakamakon abin…
Read More