ukarofi

12715 Posts
Ban taɓa ganin uwargida mai sa’a kamar uwargidan Gwamna Raɗɗa ba – Sarkin Daura

Ban taɓa ganin uwargida mai sa’a kamar uwargidan Gwamna Raɗɗa ba – Sarkin Daura

Daga RABIU SANUSI a Kano Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya bayyana cewa bai taɓa ganin uwar gida mai sa’a da natsuwa irin Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda ba. Ya ce Hajiya Zulaihat ta samu baiwar Allah ta musamman da ke bayyana a cikin jajircewarta wajen gudanar da ayyukan taimako ga al’umma, musamman mata da marasa galihu. Sarkin ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke Daura, yayin da yake karɓar gaisuwar godiya daga Uwargidan Gwamna Radda, wadda ta kai masa ziyara domin nuna godiya bisa nadin sarautar “Jagabar Matan Kasar Hausa” da aka ba…
Read More
Masana sun danganta cunkoson manyan asibitoci da raunin cibiyoyin lafiya

Masana sun danganta cunkoson manyan asibitoci da raunin cibiyoyin lafiya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Masana harkar kiwon lafiya sun ɗora alhakin cunkoson marasa lafiya a manyan asibitocin gwamnati ga rashin ingancin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko (PHC) a ƙasar nan, suna masu cewa matsalar na janyo ƙarancin gadon kwanciya da tsaikon kula da marasa lafiya a matakai biyu da uku na jihohi da tarayya. A tattaunawa da manema labarai a Legas a ranar Litinin, ƙwararrun sun ce ana ci gaba da ganin ɗaruruwan mutane na kwararowa zuwa manyan asibitoci domin neman kulawa, duk kuwa da cewa yawancin lamurran lafiyar da suke kai su can za a iya magance…
Read More
Kano: Mutane fiye da 200 ne suka samu tallafin jari a Mariri

Kano: Mutane fiye da 200 ne suka samu tallafin jari a Mariri

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Mutane sama da dari biyu maza da mata ne suka amfana da tallafin kuɗi na N20,000 kowannensu domin gudanar da sana’o’in dogaro da kai, daga Kansilan Mazabar Mariri, kuma Shugaban Majalisar Kansilolin Kumbotso, Hon. Nafi’u Alhassan Garba Roja. Hon. Roja ya bayyana cewa wannan tallafi yana cikin ƙudirin Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ke da nufin tallafawa jama’a musamman matasa da talakawa domin rage zaman banza da dogaro da wasu. Ya ce, “Mun ɗauki wannan mataki ne domin karfafa sana’o’i da tabbatar da cewa mutanenmu suna da abin dogaro da kansu.” Ya roƙi…
Read More
Mun shafe kusan shekara 70 muna neman hanyar Tamburawar Gabas – Bala Tamburawa

Mun shafe kusan shekara 70 muna neman hanyar Tamburawar Gabas – Bala Tamburawa

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Bayan shekaru kusan saba’in na jiran a gyara hanya, al’ummar Tamburawar Gabas a karamar hukumar Warawa sun samu gagarumar farin ciki bayan Shugaban ƙaramar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, ya kammala gina musu hanya da ta dade tana janyo musu matsala. Jagoran al’ummar garin, Alhaji Bala Tamburawa, ya bayyana cewa wannan hanya ta kasance mafarkin jama’a shekaru da dama, inda aka sha nema a lokutan da suka gabata amma babu wanda ya aiwatar. Ya ce, “Mun shafe shekaru da dama muna neman wannan hanya, sai yanzu Allah ya kawo mana wannan hazikin shugaba…
Read More
Kungiyar MODESA a Bauchi ta gano hanyoyin kama baburan hawa da aka sace a jihohin da ake rikici

Kungiyar MODESA a Bauchi ta gano hanyoyin kama baburan hawa da aka sace a jihohin da ake rikici

Daga MU'AZU HARDAWA a Bauchi  ƙungiyar dillalai masu sana'ar sayar da baburan hawa ta ƙasa reshen jihar Bauchi MODESA ta fito da sabbin hanyoyin magance satar baburan hawa a jihohin Nijeriya. Shugaban ƙungiyar dillalan sayar da baburan hawa ta ƙasa reshen jihar Bauchi, Alhaji Muazu Chiroma shi ne ya bayyana cikin jawabinsa ga manema labarai bayan an sake rantsar da shi na tsawon shekara huɗu a karo na biyu. Ya ƙara da cewa a halin yanzu sun fito da sabbin hanyoyin magance sayen baburan hawa na sata da ke fitowa daga wasu jihohin musamnan wuraren da ake fama da tashe-tashen…
Read More
Gwamna Yusuf ya jinjina wa rundunar sojin Nijeriya bisa ƙoƙarin daƙile harin ‘yan bindiga a Kano

Gwamna Yusuf ya jinjina wa rundunar sojin Nijeriya bisa ƙoƙarin daƙile harin ‘yan bindiga a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Rundunar Sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro bisa hanzari da jajircewar da suka nuna wajen daƙile hare-haren ɓarayin daji da suka faru a wasu yankunan jihar a kwanakin baya. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar. Gwamna Yusuf ya yi wannan magana ne lokacin da yake karɓar baƙon hanya, Babban Jami’in Kwamando (GOC) na Runduna ta 1 ta Sojin Nijeriya, Manjo Janar Abubakar Sadiƙ Muhammad Wase, a Fadar Gwamnati da ke Kano. Manjo…
Read More
Abba ya umarci a riƙa gudanar da taron tsaro a ƙananan hukumomin Kano

Abba ya umarci a riƙa gudanar da taron tsaro a ƙananan hukumomin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugabannin dukkan ƙananan hukumomin jihar da su riƙa gudanar da tarukan tsaro akai-akai domin ƙarfafa zaman lafiya da kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma. A cewar wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayar su a tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin magance matsalolin da ke addabar yankuna. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rahotannin hare-haren ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin da ke kan iyaka da Jihar Katsina…
Read More
Masu aiki a tukubar sayar da tsire sun fi ma’aikatan gwamnati samun garabasa – Abdullahi Kunya

Masu aiki a tukubar sayar da tsire sun fi ma’aikatan gwamnati samun garabasa – Abdullahi Kunya

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Wani fitaccen ɗan kasuwa a fannin sayar da tsire a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Yusuf Kunya, ya bayyana cewa ma’aikatan da ke cikin tukubar tsire ta Rahusa Suya, sun fi yawancin ma’aikatan gwamnati samun garabasa da walwala ta fuskar albashi, lafiya, da jin daɗin rayuwa. Alhaji Abdullahi, wanda shi ne Manajan Rahusa Suya, kuma ɗan marigayi Sarkin Fawar Kunya na ƙaramar hukumar Minjibir, ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a kasuwar Dimawa da ke Kano, inda ya ce sana’ar tsire ta zama wata babbar hanyar samar da ayyukan yi ga…
Read More
‘Yan kwangilar Majalisar Wakilai sun hana zama kan haƙƙoƙinsu

‘Yan kwangilar Majalisar Wakilai sun hana zama kan haƙƙoƙinsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su. Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya…
Read More
Ya kamata mu riƙa gyaran maƙabartunmu – Garba Maigemu

Ya kamata mu riƙa gyaran maƙabartunmu – Garba Maigemu

Daga DAUDA USMAN a Legas A ranar Lahadi da ta gabata, al’ummar Musulmi na kasuwar Mile-12 International Market, Legas, ƙarƙashin jagorancin Malam Garba Mai Gemu (ɗan asalin ƙaramar hukumar Rogo, Jihar Kano), suka gudanar da aikin gaishe-gaishe da cika ƙasa a tsohuwar maƙabarta domin dawo da ita yadda ta dace. Aikin ya hada da tunkuɗe ƙasa, shimfiɗa ƙasa da kuma shirya wajen domin a mayar da shi sabuwar maƙabarta mai ɗorewa. Malam Garba Mai Gemu ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa unguwar Mile 12 na da maƙabartu guda biyu,  tsohuwar da sabuwa. Tsohuwar makabartar da ake amfani da ita ta…
Read More