ukarofi

12715 Posts
‘Safe Corridor’: Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirin daidaita tarbiyyar tubabbun ’yan daba 

‘Safe Corridor’: Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirin daidaita tarbiyyar tubabbun ’yan daba 

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da ƙudurinta na ci gaba da tallafawa da kuma sake tsare tarbiyya ga matasa tubabbun 'yan daba, ta ƙarƙashin shirin Safe Corridor, wani shiri na musamman da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙirƙiro domin dakile ta’addanci da tashin hankali a tsakanin matasa tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar. Wannan tabbacin ya tabbata ne a lokacin da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Waiya wanda kuma shi ne Kwamandan Shirin Safe Corridor na Jihar Kano, ya jagoranci taron hadin gwiwa tsakanin jagorancin matasa…
Read More
Netherlands ta amince da mayar da abin tarihin Fir’auna da aka sace ga Masar

Netherlands ta amince da mayar da abin tarihin Fir’auna da aka sace ga Masar

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Netherlands ta sanar da cewa za ta miƙa wani abin tarihi mai shekara 3,500 da aka sace a lokacin tashin hankalin Arab Spring ga Masar, a wani mataki da masana suka ce na tabbatar da mutunta kayan tarihi da martabar al’adu. Rahotanni sun ce wannan sassaƙaƙƙen akwatin ajiye mutum daga zamanin sarautar Fir’auna Thutmose na Uku an yi amannar an fitar da shi ba bisa ƙa’ida ba a shekarar 2011 ko 2012. Sai dai shekaru bayan nan, aka sake gano shi a bikin nune-nunen fasaha a birnin Maastricht, bayan wata bayanai da aka bai wa…
Read More
Gwamnatin Kano ta ƙuduri aniyar mallakar kamfanin KEDCO don ƙarfafa samuwar lantarki

Gwamnatin Kano ta ƙuduri aniyar mallakar kamfanin KEDCO don ƙarfafa samuwar lantarki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki sabon mataki na tarihi wajen shata muradunta a fannin samar da lantarki, inda ta amince da shirin mallakar kaso mafi rinjaye na hannun jari a Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO). Wannan mataki, a cewar gwamnatin jihar, zai buɗe sabon babi na ci gaba, musamman wajen inganta wutar lantarki da farfaɗo da masana’antu da harkokin kasuwanci a jihar. Sanarwar ta fito ne daga kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa karo na 33 a Kano. A cewar gwamnatin, mallakar KEDCO zai bayar…
Read More
Oyetola ya buƙaci jihohin Yarabawa su gina wuraren shaƙatawa na bakin teku

Oyetola ya buƙaci jihohin Yarabawa su gina wuraren shaƙatawa na bakin teku

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Dr. Adegboyega Oyetola, ya buƙaci gwamnatocin jihohin Yammacin Nijeriya su yi amfani da damar da tekun Leges–Kalaba ke bayarwa domin raya yawon shaƙatawa da sauran ayyukan kasuwanci na bakin teku, don haɓaka tattalin arzikin yankin. Da yake jawabi a taron hulɗar gwamnati da jama’a na Yankin Kudu maso Yamma da aka gudanar a Akure, jihar Ondo, a ranar Laraba, 29 ga Oktoba 2025, Oyetola ya bayyana wannan babbar hanya ta bakin teku a matsayin aikin da zai sauya fasalin tattalin arziki da sadarwa a gaɓar tekun Nijeriya. Ya ce,…
Read More
NNPC na ƙoƙarin ninka hannun jarinsa zuwa kashi 20 a matatar Dangote

NNPC na ƙoƙarin ninka hannun jarinsa zuwa kashi 20 a matatar Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta hannun Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC) ta sanar da shirin ƙara hannun jarinta a matatar mam fetur ta Dangote daga kashi 7.2% zuwa kashi 20%, a wani mataki da ake ganin zai ƙarfafa ikon Nijeriya wajen tace mai a gida da rage dogaro da shigo da man waje. Hakan ya fito ne daga bakin Babban Daraktan NNPC, Bayo Ojulari, yayin wani taron masana’antar mai da aka gudanar a birnin Abu Dhabi (ADIPEC 2025). Ya ce wannan shawara na nuna burin gwamnati na ƙarfafa Nujeriya a masana’antar makamashi da kuma tabbatar da tsaron…
Read More
‎Mun buɗe ƙofofi ga bankuna don ƙarfafa tattalin arzikin Kano – Gwamna Yusuf

‎Mun buɗe ƙofofi ga bankuna don ƙarfafa tattalin arzikin Kano – Gwamna Yusuf

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa tana ci gaba da jajircewa wajen bunƙasa shigar jama’a cikin harkokin kuɗi, don ƙarfafa tattalin arziki, musamman ga matasa da mata, yayin. Yayin da ya ƙaddamar da sabon reshen Signature Bank a Kano ranar Talata, gwamnan ya ce, zuwan Signature Bank Kano hujja ce ta yadda jihar ke ƙara zama cibiyar kasuwanci mai jan hankalin masu zuba jari. Ya sha alwashin bai wa bankin cikakken haɗin kai tare da tabbatar da sauƙaƙa yanayin kasuwanci a jihar. Yusuf ya bayyana cewa, tsarin tattalin arzikin gwamnatinsa…
Read More
Kogi: NYSC ta bai wa matasan da suka yi aure a sansani kyautar N500,000

Kogi: NYSC ta bai wa matasan da suka yi aure a sansani kyautar N500,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Hidimar ƙasa ta Nijeriya (NYSC) a Jihar Kogi ta karrama wasu matasa ‘yan hidimar ƙasa guda biyu masu suna Popoola Afeez da Monica Feliɗ, waɗanda soyayyarsu ta fara ne tun lokacin shirin horarwa a sansanin NYSC, har ta kai su ga aure cikin shekarar hidimar su ta ƙasa. Wannan soyayya da ta kunno kai daga sansanin shirin ƙasa ta ci gaba da ƙulluwa, inda ta kai ga ɗaura aure, lamarin da ya jawo yabo daga abokan hidima da jami’an NYSC. An bayyana cewa ma’auratan sun sami kyautar kuɗi har N500,000 daga hukumar a…
Read More
Imagireshin za su fara bai wa ’yan Nijeriya mazauna waje fasfon gaggawa

Imagireshin za su fara bai wa ’yan Nijeriya mazauna waje fasfon gaggawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta bayyana cewa za ta ƙaddamar da sabon fasfon gaggawa na tafiya ɗaya 'Single Travel Emergency Passport' (STEP), domin tallafa wa ’yan Nujeriya da ke ƙasashen waje waɗanda fasfo ɗinsu ya ƙare, ya ɓace, ko kuma aka sace musu, domin su samu damar dawowa gida cikin sahihanci da tsaro. Wannan mataki, wanda zai maye gurbin 'Emergency Travel Certificate' (ETC) da ake amfani da shi yanzu, na cikin shirin sabunta harkokin shige da fice da inganta tsaro da tabbatar da sahihin fasfo ga ’yan Nijeriya, bisa tsarin duniya. Hedikwatar hukumar…
Read More
Borno: Sojoji sun daƙile harin diron daga Boko Haram, sun kashe da dama

Borno: Sojoji sun daƙile harin diron daga Boko Haram, sun kashe da dama

Daga MAHDI MUSA MUAHMMAD Sojojin Nijeriya tare da haɗin gwiwar dakarun Nijar sun cimma gagarumar nasara a safiyar Talata, bayan sun fatattaki mummunan harin da Boko Haram ta kai a Malam Fatori, hedikwatar ƙaramar hukumar Abadam a jihar Borno. Aƙalla ‘yan ta’adda shida aka kashe a wurin, yayin da sauran suka tsere da munanan raunuka bayan artabu mai tsanani. Rahotanni daga hukumomin tsaro sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 4:30 na safe, inda suka yi ƙoƙarin mamaye sansanin Forward Operating Base (FOB) na sojoji. Boko Haram ta yi amfani da manyan makamai, har da makaman…
Read More
Rundunar ’yan sanda ta ƙaryata zargin tilasta jami’anta sayen littafin ƙwarewar aiki

Rundunar ’yan sanda ta ƙaryata zargin tilasta jami’anta sayen littafin ƙwarewar aiki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta musanta zargin da ake yaɗawa cewa ana tilasta jami’an ta a faɗin Nujeriya su sayi wani littafi mai suna “Attitudinal Change Handbook for the Nigeria Police Force” akan kuɗin Naira 2,000. Wani rahoto daga wata jarida ta yanar gizo ya yi iƙirarin cewa an bayar da umarnin wajabta sayen littafin tare da sanya wa’adin kammala karanta wa da yiwuwar ladabtar da duk jami’in da ya ƙi bi. Sai dai bayanan da aka samu a ranar Litinin sun nuna cewa izinin da Hedikwatar ‘Yan Sanda ta bayar shi ne bai wa marubucin…
Read More