08
Nov
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Matuƙan Jiragen Sama da Injiniyoyin Kayan Jirage ta Nijeriya (NAAPE) ta sanar da ƙaddamar da sabon tsarin inshorar “Loss of Licence”, domin tabbatar da kariya ga mambobinta — musamman matuƙa da injiniyoyi — idan suka rasa lasisin aikinsu sakamakon rashin lafiya ko wasu dalilai na ƙwarewa da ƙa’ida da ka iya hana su ci gaba da aiki. A cewar ƙungiyar, wannan shiri da aka ƙirƙira tare da First Standard Insurance Brokers, zai ba da cikakkiyar kariya ta inshora ga duk matuaa jirage da injiniyoyin jirage a Nijeriya da suka fuskanci rasa lasisin aikinsu saboda nakasar…
