ukarofi

12715 Posts
Nijeriya ta samu amincewar gudanar da Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta UNESCO ta farko

Nijeriya ta samu amincewar gudanar da Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta UNESCO ta farko

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta ƙasa da ƙasa a Abuja, Nijeriya, a matsayin Cibiyar UNESCO ta Rukuni na Biyu, wacce ita ce irin ta ta farko a duniya. A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mai Taimaka wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa UNESCO ta bayar da wannan muhimmiyar amincewa ne a Babban Taro na 43 na Hukumar Sadarwa da Bayanai da aka gudanar a birnin…
Read More
Wajibi a riqa tantance hadisai da Qur’ani

Wajibi a riqa tantance hadisai da Qur’ani

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Kusan daga shekaru ashirin da su ka gabata zuwa yanzu, na sha gwagwarmaya da Yan Quraniyyun game da yarda da amfani da hadisi, abinda su ke suka tare da kafa hujjar cewa Qurani kadai ya ishe mu saboda ayoyi irinsu Q6:38 "... Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi (Quran)." Ko Q12:111 "..(Qurani) Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni." To amma shin, wadannan ayoyi na nufin…
Read More
Da sauti Allah zai tashi kiyama?

Da sauti Allah zai tashi kiyama?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Allah ya gaya mana cikin Qurani cewa a ranar da za'a tashi kiyama, wani Kaho za'a busa wanda zai halaka dukkan halittu masu Rai da mara Rai (face yan kalilan) a cikin sammai da ƙassai; Q39:68 "Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo." Wato tashin alkiyama, ko muce karshen duniya/sammai (universe) wadda ta faro kimanin shekaru biliyan 13.8 (ko biliyan 28 sakamakon wasu sabbin alkaluma na…
Read More
Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai

Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hafsan Sojin Sama na Nijeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama  A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Ya ce, “Dole ne yayin kowane aiki a nuna ƙwarewa da ƙaunar ƙasa.” Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce taron ya mayar da hankali kan duba dabarun aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai…
Read More
Kotu ta dakatar ya ‘yan sanda daga neman Sowore ruwa a jallo

Kotu ta dakatar ya ‘yan sanda daga neman Sowore ruwa a jallo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Kotun Tarayya a ke zamanta aLegas, ta hana Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Legas da sauran hukumomin tsaro kama wani mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore. Ta kuma hana su tsoratarwa ko bayyana cewa ana neman ɗan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress (AAC) a zaɓen 2023. Manhaja ta ruwaito cewa umarnin Alƙali Musa Kakaki ya shaida haka biyo bayan buƙatar da Sowore ya shigar bayan rahotannin da suka bayyana cewa rundunar 'yan sandan Jihar Legas ta ayyana nemansa ruwa a jallo bisa zargin da ba a bayyana ba. A…
Read More
ASUU ta musanta bayanan ministan ilimi kan cika mata alƙawari

ASUU ta musanta bayanan ministan ilimi kan cika mata alƙawari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ƙungiyar Malaman jami'o'in Nijeriya, ta ASUU, ta mayar da kakkausan martani ga gwamnatin ƙasar, bayan ta zargi ministan ilimi, Dokta Tunji Maruf Alausa, da yin wasu bayanai masu cike da kura-kurai, dangane da batun cika alƙawuran da gwamnati ta yi a yarjejeniyoyin da ta ƙulla da ma'aikatan jami'o'in ƙasar. ƙungiyar ta ASUU ta ce har yanzu romon baka kawai gwamnatin ƙasar ke yi wa ma'aikatan jami'o'i. Ga dukkan alamu dai har yanzu tana kasa tana dabo, dangane da ja-in-jar da ke tsakanin gwamnatin Nijeriya da ƙungiyar malaman jami'o'in ƙasar, ta ASUU. Rahotanni sun ambato…
Read More
Haɗin kan sojojin Nijeriya da Faransa: Ma’anar ziyarar Janar Charpy zuwa NDA

Haɗin kan sojojin Nijeriya da Faransa: Ma’anar ziyarar Janar Charpy zuwa NDA

Daga SANATA IROEGBU Ziyarar da Laftanar Janar Emmanuel Charpy, kwamandan École Spéciale Militaire de Saint-Cyr (ESM) ta Faransa, ya kai Kwalejin Horar da Sojoji ta Nijeriya (NDA) da ke Kaduna, ta fi zama wata al’ada ta diflomasiyya kawai. Tana ɗauke da ma’ana mai zurfi ga tsaron ƙasa, haɗin kai da matsayin Nijeriya a fagen soja na duniya. A zamanin da ake gaggawar siyasantar da hulɗa tsakanin ƙasashe, ya zama wajibi a fahimci irin wannan ziyara a matsayin girmamawa da haɗin kai, ba nuna rauni ko dogaro ba. Wannan haɗin gwiwa tana nuni da ƙarfin Nijeriya da kuma ikon ta na…
Read More
Yadda ake rufa-riufa kan matsalar tsaro a Kebbi – Rahoto

Yadda ake rufa-riufa kan matsalar tsaro a Kebbi – Rahoto

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Duk da irin zagin da ake yi na rufa-rufa da Gwamnatin Jihar Kebbi ke yi dangane da matsalar tsaro, bincike ya nuna cewa, gaskiyar magana a kullum sai ƙara bayyana ta ke yi. Wani bincike da Wakilin Blueprint Manhaja ya gudanar a waɗansu sassa daga Jihar Kebbi ya nuna a ƙaramar Hukumar Arewa ya nuna cewa, daga cikin makarantu 198 da suke akwai yanzu, aƙalla 144 sun koma kango, saboda babu ɗalibai ballantana malamai, domin kowa ya watse, saboda ’yan bindiga da Lakurawa sun mamaye yankin. Waɗansu sahihan majiyoyi sun tabbatar da cewa, malamai da…
Read More
An fara rage farashin fetur bayan saukar kuɗin shigo da mai

An fara rage farashin fetur bayan saukar kuɗin shigo da mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni daga Babban Birnin Tarayya Abuja sun nuna cewa wasu gidajen mai sun rage farashin litar man fetur, bayan da farashin shigo da mai daga ƙasashen waje ya sauka ƙasa warwas da farashin dillalan matatar Dangote. An ruwaito cewa, a ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, wasu manyan dillalai kamar NIPCO, AA Rano, Eterna, da Empire Energy sun rage farashin su a sassa daban-daban na Abuja. A cewar rahoton, NIPCO da AA Rano sun saukar da farashin su zuwa N940 a kan kowace lita, daga tsohon farashin N950 zuwa N955. Eterna na sayarwa kan N945, yayin da…
Read More
Matasa sun lakaɗa wa limami duka har lahira bisa zargin maita

Matasa sun lakaɗa wa limami duka har lahira bisa zargin maita

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata gungun matasa a ƙauyen Sokupkpan na ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara sun kashe babban limamin ƙauyen bayan sun zarge shi da haddasa mutuwar wani matashi ta hanyar tsafi. Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka kashe, Mallam Abdullahi Audu, ya rasu ne a ranar Laraba bayan wasu fusatattun matasa sun yi masa dukan kawo wuƙa bisa zargin cewa shi ne ya haddasa mutuwar Ibrahim Gana, matashi mai shekara 25 da suka fito daga yanki ɗaya. Lamarin ya tayar da hankula a cikin ƙauyen Sokupkpan, inda fargaba da ruɗani suka riƙa yaɗuwa tsakanin jama’a. Wani mazaunin…
Read More