ukarofi

12715 Posts
Majalisa ta umarci NAFDAC ta fara aiwatar da haramcin barasar leda daga Disambar 2025

Majalisa ta umarci NAFDAC ta fara aiwatar da haramcin barasar leda daga Disambar 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayar da umarni ga Hukumar Kula da Abinci da Magunguna (NAFDAC) da sauran hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da cewa an aiwatar da haramcin haɗa barasa mai ƙarfi a kwalabe ko leda daga watan Disamba 2025, ba tare da wani ƙarin lokaci ba. Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta ƙi amincewa da buƙatar wasu masana’antu na sake samun ƙarin shekara guda don ci gaba da samar da barasa a leda. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da Sanata Asuƙuo Ekpeyong ya gabatar, wanda ya buƙaci majalisar ta hana duk wani…
Read More
Majalisa ta gano ɓacewar Dala Biliyan 303 daga kuɗaɗen mai

Majalisa ta gano ɓacewar Dala Biliyan 303 daga kuɗaɗen mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dattawan Nijeriya ta gano gagarumin almundahana a harkar man fetur na ƙasa, inda ta bayyana cewa kusan Dala Biliyan 303 na iya ɓacewa daga cinikayyar man gida da ta ƙasashen waje. Wannan bincike na musamman wanda Sanata Ned Nwoko ke jagoranta ya nuna cewa sakamakon binciken ƙwararru ya gano bambance-bambance da rashin daidaituwa a kuɗaɗen da suka kai kusan dala biliyan 22. Binciken ya kuma gano giɓin dala biliyan 81 tsakanin bayanan da kamfanin NNPCL da Babban Bankin Nijeriya (CBN) suka bayar a shekarun 2016 da 2017 — abin da ya tayar da hankali a…
Read More
Gwajo Gwajo ya yaba da hangen nesa a kasafin kuɗi na 2026 da Gwamna Raɗɗa ya gabatar

Gwajo Gwajo ya yaba da hangen nesa a kasafin kuɗi na 2026 da Gwamna Raɗɗa ya gabatar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rt Hon Ya'u Umar Gwajo Gwajo wanda ya tattauna da manema labarai a Katsina a kan kasafin kudi da Gwamna Dikko Raɗɗa ya gabatar,ya nuna gamsuwa musamman inda aka ware kashi 80 bisa 100 domin gudanar da manyan ayyuk. Hon.Gwajo Gwajo wanda tsohon kakakin majalisar dokokin Katsina kuma a yanzu mai bai wa gwamna Shawara kan harkokin siyasa ya ce wannan tsari na nuna jajircewar Gwamna Raɗɗa wajen tabbatar da ci gaban jihar ta fuskar ababen more rayuwa da inganta tattalin arzikin jama’a. Ya kuma jinjinawa Gwamnan bisa ƙoƙarinsa na ci gaba da bunƙasa fannonin…
Read More
Zargin kashe Kiristoci: Ana ci gaba da yin tir da Trump

Zargin kashe Kiristoci: Ana ci gaba da yin tir da Trump

*Tinubu, ECOWAS, Chana, Gumi da rahoton BBC lauyan Amurka sun yi allawadai *An yi musayar yawu tsakanin Akpabio da Barau  Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayyar NIjeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da Gwamnatin ƙasar Amurka ta ɗauka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake ganin suna take ’yancin yin addini. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Mohammed Idris (FNIPR), ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Cibiyar ƙasa ta Yaɗa Labarai, Abuja, a ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025. Idris ya ce gwamnatin Nijeriya ta…
Read More
FCCPC ta rufe shagunan tufafi a Kano saboda yaudarar masu saye

FCCPC ta rufe shagunan tufafi a Kano saboda yaudarar masu saye

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar kare haƙƙin mai saye ta ƙasa wato Federal Competition and Consumer Protection Commission(FCCPC) ta gudanar da samame ranar Laraba a Kano, inda ta rufe wasu shagunan dillalan kayan ɗinki da ake zargin suna sayar da kayan da aka tauye mudun su. Binciken da hukumar ta yi ya gano cewa wasu ƴan kasuwa na sayar da kayan da aka rubuta “10 yards” yadi goma alhali ba su wuce idan ka duba ciki sai ka samu bai wuce yadi tara ba, “9 yards”, tare da karɓar cikakken kuɗi daga masu saye. Daraktar bincike da Sa-ido ta…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 31 wajen gina madatsar ruwa ta Zobe

Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 31 wajen gina madatsar ruwa ta Zobe

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da ci gaba da aikin madatsar ruwa ta Zobe a ƙaramar hukumar Ɗanmusa. Aikin wanda aka fara shi tun fiye da shekara 30 da suka gabata, za a kashe kuɗi naira biliyan 31 wajen kammala shi, kamar yadda hukumomi suka tabbatar, inda ake sa ran zai samar da ruwa mai tsafta ga ƙananan hukumomi bakwai ciki, har da Katsina babban birnin jihar. Gwamnan Katsina Dikko Umaru Raɗɗa ya ce, aikin wanda gwamnatocin baya suka gaza kammalawa ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen gwamnatinsa. "Daga sanya hannu a wannan kwangila,…
Read More
Gwamnan Katsina ya kafa kwamitin da zai sa ido kan almajirai

Gwamnan Katsina ya kafa kwamitin da zai sa ido kan almajirai

Sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari wanda ya ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnatin jihar ya ce zai gudanar da bincike da kuma kawo mafita kan matsalar mutane da ke yawon bacci a kan tituna da wuraren da ba su dace ba. Ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne domin ganin an rage yawan mutanen da ke kwana a waje saboda talauci, rashin gida, da kuma wasu matsalolin rayuwa. Barista Faskari ya bayyana cewar Kwamitin zai fara gudanar da bincike da tattara bayanai domin gano mutanen da ke yawo ko kwana a tituna a dukkan ƙananan hukumomi na jihar…
Read More
Muhallin darbejiya a gyaran jiki (3)

Muhallin darbejiya a gyaran jiki (3)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.  A makon baya, mun fara kawo maku bayanai kan amfanin darbejiya ga fata. Inda kuma sanar da ku cewa, wannan sati za mu cigaba. Kamar yadda muke faɗa tun a farkon darasin, iccen darbejiya ba sabon abu ba ne ga magungunan gargajiya. Amma yanzu, masana kimiyyar kula da fata sun tabbatar da amfaninsa cikin sahihancin bincike. A yau, yawancin cream, soap, da face wash na zamani suna ɗauke da sinadaran darbejiya saboda ƙarfinsa wajen gyara da kare fata. 3. Sabunta sabuwar…
Read More
Dandalin shawara: Ina neman dabarun da zai sa saurayi ya dinga ba ni kuɗi ko ba yawa

Dandalin shawara: Ina neman dabarun da zai sa saurayi ya dinga ba ni kuɗi ko ba yawa

Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Assalamu alaikum. Aunty Aysha ya ki ke? Ya yara? Dan Allah shawara nake so a bani. Ina da saurayi, yana sona, ni ma kuma Ina son shi, ga shi iyaye na sun matsa min akan na fito da miji nai aure. Ni kuma na kasa gaya mai yanzu haka wancan sati akai auren ƙanwata yanzu sun ce in ban fito da miji nan da wata ɗaya ba, duk wanda suka zaɓa min shi zan aura. Ni kuma Ina son wancan, amma na kasa gaya mai, kuma shi wanda nake so bai ban kosisin kuɗi, bai taɓa…
Read More
Maguzawa daban Muguzanci daban

Maguzawa daban Muguzanci daban

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa akwai jama’a da su ke zama lafiya a matsayin maguzawa a garuruwan Hausawa. Kama daga yankin Malumfashi a jihar Katsina, zuwa wajajen Sumaila a jihar Kano da ma yankunan jihar Jigawa har ma cikin ƙasar Gobir; a na samun maguzawa da ke zaune da iyalinsu lafiya kuma sun fi zama a ƙauyuka. A gefe guda yayin da maguzawa ke zama al’umma da ke rayuwa irin ta gargajiya da zabar rashin shin shiga Musulunci, akwai kuma wata ɗabi’a ta maguzanci da ba lallai sai a waɗannan yankuna da na lissafa ba. Za a iya samun maguzanci…
Read More