ukarofi

12715 Posts
An samu Musulmi na farko a Amurka da ya zama magajin garin New York

An samu Musulmi na farko a Amurka da ya zama magajin garin New York

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A karon farko a tarihin Amurka, Musulmi ya zama Shugaban Gwamnatin birnin New York (Mayor of New York). Mai suna Zohran Mahmood Mamdani, ɗan shekaru 34, wanda asalinsa daga ƙasar Uganda ne amma ya tashi kuma ya girma a Amurka. Zohran ya shiga siyasa ƙarƙashin jam’iyyar Democrat, inda ya tsaya takarar shugabancin birnin New York, ya kuma kayar da ɗan takarar da shugaban ƙasa Donald Trump ya goyi baya. Kazalika, rahotanni sun nuna cewa New York shi ne birni mafi girma da tasiri a Amurka, kuma yanzu Musulmi ne ke jan ragamar birnin — mai…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan aikin kwangilar samar da ruwan sha daga madatsar ruwa ta Zobe

Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan aikin kwangilar samar da ruwan sha daga madatsar ruwa ta Zobe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan aiki kashi na biyu idan an kammala zai ba garuruwan Rimi, Charanchi,kafinsoli,Tafashya, Raɗɗa, karofi da Dutsinma wadataccen ruwan sha. Haka kuma za a kafa bututun ruwan mai tsawon mita 88.74 da ƙarfafa cibiyar samar da ruwan sha na kafinsoli. Idan an kammala aikin madatsar ruwan za ta samar da lita miliyan 1.5 na ruwan sha ga alummomin yakin da haɓaka noman rani ga ƙananan sana'o'i a yankin. Gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya ƙaddamar da aikin a garin kafinsoli ya ce yau shekara 47 da fara aikin gina Zobe Dam tun lokacin mulkin marigayi shugaban…
Read More
Harin Shanono: Ku dage da addu’o’in samun zaman lafiya – Sarkin Kano

Harin Shanono: Ku dage da addu’o’in samun zaman lafiya – Sarkin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya umarci hakimai da dagatai, da kuma masu unguwanni, da ma limaman masallatan Juma’a, da su ƙara dagewa da addu’o’n samun zaman lafiya a jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya. ‎Sarkin ya bada wannan umarni ne a ranar Talata a bisa ganin yadda wasu mahara su ke shiga ƙaramar hukumar Shanono, inda kuma bisa yawan addu’ar har aka samu nasarar hallaka mutum 19 daga cikinsu. ‎Mai martaba sarkin ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa tura jami’an sojoji, da jami’an tsaro na farin kaya akan…
Read More
Majalisar Dokokin Kano za ta samar da dokar koyar da ɗalibai da harshen uwa

Majalisar Dokokin Kano za ta samar da dokar koyar da ɗalibai da harshen uwa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar dokokin kano ta fara yunƙurin samar da wata doka wadda za ta tilasta yin amfani da harshen uwa musamman harshen Hausa a matsayin hanyar koyarwa a makarantun jihar, domin bunƙasa fannin ilimi. Hakan ya biyo bayan kuɗurin da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Takai a zauren Dr. Musa Ali Kachako ya gabatar. Da yake ƙarin bayani a gaban majalisar, Dr. Kachako yace samar da dokar zai dace da yadda tsarin koyarwa yake a duniya kamar yadda ƙasashen da suka ci gaba irin su China, Japan da India suka samu babbar nasara ta hanyar…
Read More
Ƙaramar Hukumar Katsina za ta gina cibiyar koyon ƙirƙirar kimiyya da fasaha

Ƙaramar Hukumar Katsina za ta gina cibiyar koyon ƙirƙirar kimiyya da fasaha

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wani mataki na bunƙasa ilimi da cigaban fasahar zamani, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya bayyana shirin gina cibiyar koyon kimiyyar sadarwa ta zamani (Digital Learning Centre) a makarantar firamare ta Layout, Wakilin Kudu II. Da zarar an kammala aikin, cibiyar za ta kasance cikin na’urorin kwamfuta na zamani da kayan aikin ICT, wadda za ta zama cibiyar koyon fasahar kwamfuta da dabarun dijital da kuma koyo ta yanar gizo. Domin tabbatar da ci gaba da aiki ba tare da tangarɗa ba shugaban ƙaramar hukumar ya ce za a samar…
Read More
Ɓangaren ilimi ya fi samun kaso mai tsoka a kasafin kuɗin 2026 na gwamnatin Katsina

Ɓangaren ilimi ya fi samun kaso mai tsoka a kasafin kuɗin 2026 na gwamnatin Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An sami ƙarin Naira biliyan 66 a ɓangaren Ilimi a kasafin kuɗin 2026 idan an kwatanta da Naira biliyan 90 da aka ware wa ilimi a shekarar 2025. Ma'aikatan ayyuka,gidaje da sufuri ta sami Naira Biliyan 117 sai aikin gona da ya sami Naira biliyan 78. Kiwon lafiya kuwa ya sami biliyan 67.5,haka kuma fannin ruwan sha ya sami Naira biliyan 62.8. Sai ma'aikatar muhalli da ta sami Naira biliyan 53.8 sauran ma'aikatu da hukumomi suka sami Naira biliyan 536.384 dai dai da kashi 59.7 bisa ɗari na kasafin kuɗin. Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗin…
Read More
Soja ya kashe kansa bayan ya kashe matarsa a Neja

Soja ya kashe kansa bayan ya kashe matarsa a Neja

Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja. Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025. Ya ce, mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali…
Read More
Sauro ya ciji wani mutum a karon farko na tarihin ƙasar Iceland

Sauro ya ciji wani mutum a karon farko na tarihin ƙasar Iceland

A karon farko a tarihi, an gano sauro a ƙasar Iceland, tare da gano samfura guda uku a wannan watan a Kjos, wani yanki mai ƙwari a kusa da Hvalfjordur. Wani mai sha’awar ƙwari, Bjorn Hjaltason ne ya fara ba da rahoton ganowar a cikin wani zaure na Facebook mai suna Skordyr a Islandi (wato ƙwari a Iceland), kamar yadda Hukumar Watsa Labarai ta Iceland ta faɗa a ranar Litinin. An miƙa samfuran ga Cibiyar Tarihin Halittu ta Iceland domin bincike, inda masanin ilimin halitta Matthias Alfredsson ya tabbatar da cewa lalle sauro ne. An bayyana samfurin a matsayin Culiseta…
Read More
Kotu ta ɗaure direban jirgin ƙasa wata 18 a Legas saboda satar kuɗi

Kotu ta ɗaure direban jirgin ƙasa wata 18 a Legas saboda satar kuɗi

Wata kotu a jihar Legas da ke kudancin Nijeriya ta ɗaure wami direban jirgin ƙasa wata 18 a gidan yari saboda kama shi da laifin satar kuɗi. Mai Shari'a Rahman Osodi na kotun da ke Ikeja ta kama Christopher Ekene Ofielu mai shekara 39 da laifin satar naira miliyan 6.9 a ranar Litinin da ta gabata, kamar yadda hukumar EFCC ta ruwaito a ranar Asabar. ɗaya daga cikin laifuka uku da kotun ta kama shi da su na tuhumar sa da tura kuɗin zuwa asusun ajiyarsa na banki daga dandalin HabariPay Ltd ba bisa ƙa'ida ba. Lauyansa ya nemi alƙalin…
Read More
Kwalliya: Garin neman gira za a rasa ido 

Kwalliya: Garin neman gira za a rasa ido 

Tare da BILKISU YUSUF ALI A yau, batun kwalliya ya zama ɗaya daga cikin muhimman al’amura da suka shafi rayuwar mata, musamman matasa. Duk da cewa kwalliya wani nau’i ne na bayyana tsafta da ƙawata kai, an gano cewa akwai ƙaruwa mai yawa wajen amfani da kayan kwalliya masu haɗari, musamman na fata (skin lightening creams). Wannan lamari ya janyo damuwa a tsakanin masana lafiya da manazarta a fannin zamantakewa da lafiya. Wannan nazari za mu  tattauna matsalar amfani da kayan kwalliya masu haɗari, binciken masana, da kuma muhimmancin kwalliya ga mace idan an yi ta daidai. Matsalar kayan kwalliya…
Read More