31
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya tana tabbatar da ‘yancin addini ga kowa tare da kare ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da addininsu ba. Da yake magana a CNN a daren Talata, Idris ya ƙaryata zargin wasu jami’an Amurka da ke cewa ‘yan ta’adda a Nijeriya suna kai hare-hare ne kan Kiristoci kawai. Ya bayyana wannan iƙirari a matsayin rashin fahimtar gaskiyar yanayin tsaron ƙasar. A cewar ministan, masu yada irin waɗannan bayanai suna taimaka wa masu tada rikici da ke ƙoƙarin haifar da rikicin addini a Nijeriya. Ya ce,…
