ukarofi

12715 Posts
Yadda sojoji suka daƙile yi wa manyan gwamnatin Tinubu kisan kiyashi – Rahoto

Yadda sojoji suka daƙile yi wa manyan gwamnatin Tinubu kisan kiyashi – Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A cikin abin da jami'an tsaro suka bayyana a matsayin mafi hatsarin juyin mulki a tarihin Nijeriya kwanan nan, Hedikwatar Tsaro (DHQ), ƙarƙashin jagorancin tsohon Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa, da kuma sashin leƙen asirinta na ciki ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro (CDI) Manjo Janar Emmanuel Undiandeye, sun yi nasarar daƙile wani makirci mai tayar da hankali da nufin kifar da gwamnatin tarayya, kamar yadda PRNigeria ta ruwaito. An ruwaito cewa makircin da aka daƙile, wanda jami'an leƙen asirin tsaro suka gano makonni da suka gabata, ya ƙunshi shirye-shiryen kisan gillar manyan…
Read More
Tinubu ya rantsar da sababbin shugabannin tsaro

Tinubu ya rantsar da sababbin shugabannin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya ɗaura wa sabbin shugabannin sojoji sabbin muƙamansu. Manhaja ta ruwaito cewa an yi gajeren bikin ne a fadar shugaban ƙasa a Abuja. An yi wa sabon Babban Hafsan Tsaro, (tsohon Laftanar Janar) Olufemi Oluyede ado da sabon muƙamin Janar. An yi wa sabon Babban Hafsan Soja, (tsohon Manjo Janar) Wahidi Shaibu ado da kaya a matsayin Laftanar Janar, Babban Hafsan Sojan Ruwa, (tsohon Rear Admiral) Idi Abbas da adon kaya a matsayin Mataimakin Admiral, yayin da aka yi wa Babban Hafsan Sojan Sama, (tsohon Mataimakin Air Marshal) Kelvin Aneke ado…
Read More
Gwamnan Bauchi ya ƙirƙiri sababbin ƙananan hukumomi 29

Gwamnan Bauchi ya ƙirƙiri sababbin ƙananan hukumomi 29

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rattaɓa hannu kan sabuwar dokar da ta ƙirƙiri ƙarin ƙananan hukumomi 29 a jihar. Wata takarda da Manhaja ta samu ta nuna cewa Muƙaddashin Mataimakin Magatakarda na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Musa Yerima, ya tura wannan ƙuduri zuwa Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, yana neman amincewar Majalisar Tarayya domin tabbatar da dokar a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ake yi. A halin yanzu, Jihar Bauchi na da ƙananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya amince da su. Da ƙarin waɗannan 29 da ake…
Read More
Zugar Shaiɗan ce ta kama Maryam Sanda – Gumi

Zugar Shaiɗan ce ta kama Maryam Sanda – Gumi

*Ya yi maraba da rage ma ta hukunci Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shahararren malamin addinin Musulunci, Shaikh Ahmad Gumi, ya yi maraba da sauya wa Maryam Sanda hukunci daga kisa zuwa zaman shekaru 12 a gidan yari, yana mai cewa nadamar da ta nuna bayan kisan mijinta alama ce ta “aikin Shaiɗan”. Shaikh Gumi ya bayyana haka a wani saƙon da ya wallafa a Facebook, inda ya ce kisan mijin nata, Bilyaminu Bello, ya faru ne da tsananin fushi da tasirin Shaiɗan, sannan kuma ta fashe da kuka bayan ta gane abin da ta aikata — abin da ya kira…
Read More
An cafke wani mutum da ke bayyana kan sa a matsayin ɗan Majalisar Tarayya na Katsina

An cafke wani mutum da ke bayyana kan sa a matsayin ɗan Majalisar Tarayya na Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Jami’an tsaron farin kaya na humkuma NSCDC sun kama wani mutum wanda aka sakaya sunansa, ana zargin shi da yin sojan gona a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya a majalisar tarayya. Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun kama mutumin ne, bayan an same shi da katin shaidar bogi da wasu takardu da ke nuna cewa shi ne ɗan majalisar tarayya. Wasu rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin ganin shugaban hukumar tsaron farin kaya ne lokacin da jami’an suka gano cewa takardun nasa na bogi ne. Binciken…
Read More
Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ɗauki nauyin mata 200 don yi masu maganin cutar kansar mahaifa

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ɗauki nauyin mata 200 don yi masu maganin cutar kansar mahaifa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Matar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ɗauki nauyin mata 200 don yi masu aiki da basu magunguna kyauta masu ɗauke da cutar kansar mahaifa da ta mama a Jihar. Hajiya Huriyya ta bayyana hakan ne a wani taron wayar da kan jama'a kan ranar cutar kansa ta duniya ta 2025, wanda aka gudanar a makarantar sakandare ta 'yan mata ta gwamnati a Gusau yau Alhamis. A cewarta, za a tantance mata 200 a ƙarƙashin ofishinta domin a yi musu magani kyauta da ke ɗauke da cutar kansar nahaifa da ta mama. Hajiya…
Read More
Sheikh Yakubu Musa Hassan ya zama ɗan majalisar sarakuna a Katsina

Sheikh Yakubu Musa Hassan ya zama ɗan majalisar sarakuna a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda ya naɗa Shugaban ƙungiyar Izalah ta Jihar Katsina Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan (Sautus-Sunnah) a matsayin ɗan majalisar sarakunan jihar Katsina mai wakiltar malamai. Takardar naɗin wanda ke ɗauke da sa Aminu Tukur babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jihar ya ce wannan naɗin na bisa tanadin sashi na 21(1) na dokar sarakunan jihar Katsina. Haka kuma gwamnan ya amince da naɗin shugaban kamfanin continental Alhaji Salisu Mamman a matsayin ɗan majalisar masarautar Katsina da zai wakilci ƴan kasuwa. Harwala yau gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da naɗin Alhaji Muhammad Usman Sarki a matsayin…
Read More
Jami’ar British American University ta karrama shugabannin kamfanin ASIA a Kano

Jami’ar British American University ta karrama shugabannin kamfanin ASIA a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban kuma wanda ya assasa kamfanin ASIA Group of Companies wato Alhaji Sani Isah Abubakar (ASIA) ya samu Digirin Girmamawa na (Doctor of Excellence – Honoris Causa) daga British American University, a matsayin yabo bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasuwanci, jagoranci, da ayyukan jin ƙai. An gabatar da wannan taron lambar yabo ne a wani biki da kamfanin ASIA Group ya shirya a garin Kano ranar Alhamis, wanda ya ja hankalin manyan baki, sarakunan gargajiya, shugabannin kasuwanni da fitattun mutane daga sassan ƙasar nan. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa…
Read More
Shin waye Ouba Ali na Kamaru?

Shin waye Ouba Ali na Kamaru?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Kamar yadda na bayyana a rubuce-rubucena da suka gabata, ’yan kwangilar rusa Arewa da yaƙi ta hanyar kunna fitinar ƙabilanci, su na nan a ciki da wajen Nijeriya. Kama daga yara ‘yan soshiyal midiya zuwa gagga masu ɗaukar nauyin aikin. Ouba Ali Mohaman jigo ne ko uban gida ne ga ’yan kwangilar nan na Nijeriya. Dan Jamhuriyar Kamaru ne da bayanansa su ka nuna ya na zaune a babban birnin ƙasar Yaounde amma asalinsa daga Tibati ne a nan Kamaru. Ya yi tafiye-tafiye ƙasashe ciki kuwa da Amurka inda a 2018 ma ya shiga Washington…
Read More
Yadda falsafar Ibn Rushud ta canja duniya

Yadda falsafar Ibn Rushud ta canja duniya

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Wato ba a yi wani masani a cikin magabata wanda Allah ya albarkaci Musulunci da shi ba irin Ibn Rushud. Amma kash, akasarin Musulmi ba su ma san shi ba. Ibn Rushud ya yi shura a fanonin Ilimi irinsu philosophy, theology, medicine, astronomy, physics, psychology, mathematics, neurology, Islamic jurisprudence, law da linguistics. Kuma ya rubuta littafai sama da ɗari a waɗannan fannoni, wato guda 28 a falsafa, 20 a likitanci, 8 a fannin Shari'a, 5 a addinin Musulunci da guda 4 kan yaren Larabci. Cikin jerin abubuwa waɗanda shi ne ya fara gano su a likitance…
Read More