ukarofi

12715 Posts
Gwamnatin Kano ta ƙaryata rahoton cibiyar Wole Soyinka kan take haƙƙoƙin ’yan jarida

Gwamnatin Kano ta ƙaryata rahoton cibiyar Wole Soyinka kan take haƙƙoƙin ’yan jarida

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaryata ikirarin da Cibiyar Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism (WSCIJ) ta yi cewa jihar tana cikin jerin jihohin Najeriya da ke fiye da kowa take ’yancin kafafen yaɗa labarai. Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana rahoton a matsayin mai cike da ruɗani kuma ba shi da tushe daga gaskiyar da ke faruwa a jihar. Comrade Waiya ya nuna godiya ga kafafen yaɗa labarai bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban siyasa, zamantakewa…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta nemi a soke ɗaukar ma’aikata na hukumar Kwastam gaba ɗaya

Majalisar Dokokin Kano ta nemi a soke ɗaukar ma’aikata na hukumar Kwastam gaba ɗaya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta buƙaci dukkan ‘yan majalisa da ke wakiltar Arewa a majalisar tarayya da su ɗauki mataki mai ƙarfi domin a soke gaba ɗaya jerin sunayen sabbin jami’an da hukumar kwastam ta ƙasa ta fitar kwanan nan. Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Laraba. A ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, majalisar ta bayyana ɓacin ran ta kan tsarin ɗaukar ma’aikatan, inda ta siffanta shi da cewa cike ya ke da son kai, nuna bambanci da rashin…
Read More
Ƙaramar Hukumar Bichi ta ɗauki nauyin karatun matasa 40 a fannin lafiya

Ƙaramar Hukumar Bichi ta ɗauki nauyin karatun matasa 40 a fannin lafiya

Daga USMAN KAROFI a Abuja Shugaban fadar ƙaramar hukumar Bichi, Sani Ahmad Bello wanda ya bayyana haka, yayin tattaunawarsu da jami'ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi R/Lemo, ya ce, ƙaramar hukumar Bichi ta ɗauki nauyin ɗaliban tun daga matakin farawa zuwa gama karatun; kama daga kuɗin makaranta, unifom gami da abinci, a makarantun Kazaure, (Collage Of Nursing) da (Dambo College Of Health Science And Innovation Kazaure), inda wasu za su ɗauki tsawon shekaru uku wasu kuma shekaru huɗu kafin su kammala. Sani Ahmad ya ci gaba da cewa, ɗaliban sun rabauta da wannan tagomashi ne sakamakon bita…
Read More
Ƙaramar Hukumar Katsina za ta gina cibiyar kula da lafiyar mata masu juna biyu

Ƙaramar Hukumar Katsina za ta gina cibiyar kula da lafiyar mata masu juna biyu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan cibiya idan an kammala ginawa za ta zama na farko a ƙaramar hukumar kuma ana sa ran za ta magance matsalar ƙarancin cibiyoyin kiwon lafiya a yankin. Haka kuma zai inganta samun damar yin amfani da cibiyoyin ga mata da yara ƙanana. A cewar shugaban karamar hukumar, Alhaji Ishaq Miƙidad cibiyar za ta riƙa samar da cikakkiyar kulawa ga mata tun kafin su haihu da kuma bayan sun haihu, domin tabbatar da cewa suna samun tallafi yadda ya kamata a dukkan matakan haihuwa. "Haka kuma, za a riƙa gudanar da shirin rigakafi da tarurrukan…
Read More
Kare martabar mata da yaƙi da fyaɗe ya sa na fara rubutu – Jidda Washa

Kare martabar mata da yaƙi da fyaɗe ya sa na fara rubutu – Jidda Washa

"Shirya gasar marubuta babban cigaba ne ga marubuci" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Daya daga cikin matasan marubuta da tauraruwar su ke haske cikin jerin marubuta mata da ke sakin rubuce-rubucen su a kafafen sada zumunta na 'online', Malama Jidda Washa, wacce ta rubuta littattafai da gajerun labarai da dama da ke ɗauke da darussa daban daban na kyautata rayuwa.  A tattaunawar ta da Blueprint Manhaja, marubuciyar ta bayyana abin da ya fara zaburar da ita ta fara rubutu, da burin ta a harkar adabi. MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki? JIDDA: Sunana Hauwa'u Adam Suleiman wacce aka fi…
Read More
Magance ƙwari a gida ta bin hanyoyin gargajiya

Magance ƙwari a gida ta bin hanyoyin gargajiya

Tare da BILKISU YUSUF ALI Gabatarwa: ƙwari (pests) na ɗaya daga cikin manyan matsaloli da su ke addabar gidaje a duniya baki ɗaya, musamman a yankunan da ke da ɗumi, kamar ƙasashennmu na Afrika. Su kan haifar da babbar illa ga lafiyar ɗan Adam da tsaftar abinci da zaman lafiya a gida. Wannan bincike yana duba hanyoyin da za a bi don magance ƙwari cikin sauƙi ta hanyar haɗa hanyoyin zamani da na gargajiya. Ma’anar ƙwari: ƙwari na nufin kowanne irin dabbobi ko kwari da ke tsoma baki ko cutar da rayuwar ɗan Adam  abinci, muhalli ko lafiyar jiki. Su…
Read More
Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin duba yarjejeniyar zaman lafiya a wasu ƙananan hukumomin jihar

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin duba yarjejeniyar zaman lafiya a wasu ƙananan hukumomin jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa wani kwamiti da zai duba yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla tsakanin ɓarayin daji da al’ummomin yankunan da ke fama da matsalolin tsaro a faɗin jihar. An kafa kwamitin ne ƙarkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya jagoranci taron kafa kwamitin tare da ƙaddamar da ayyukansa. Kwamitin, wanda Kwamishinan ‘yan Sanda na Jihar Katsina zai jagoranta, ya ƙunshi wakilai daga hukumomin tsaro da sassan gwamnati. Ciki har da Kwamishinanharkokin cikin gida da tsaro wanda zai kasance sakataren kwamitin, da kuma wakilai daga rundunar Sojoji ta…
Read More
Ilimi da gaskiya ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma – Sarki Sunusi II

Ilimi da gaskiya ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma – Sarki Sunusi II

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa, yin gaskiya da amana shi ne ginshiƙin na cigaban kowace al'umma. Sarki Sunusi II ya bayyana haka ne a taron ƙaddamar da littafin (All Hands on Deck) na Ms. Arunma Oteh, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Transcorp Hilton da ke Abuja, a ranar Talata. Littafin All Hands on Deck wacce tsohuwar babbar darakta a bankin duniya Ms. Oteh ta rubuta, ya maida hankali ne kan hanyoyin bunƙasa shugabanci mai nagarta, da gaskiya da amana a harkokin tattalin arziki da mulki. Sarkin…
Read More
Hadi Sirika ya zama sabon shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina

Hadi Sirika ya zama sabon shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya amince da naɗa tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya kuma Marusan Katsina, Sanata Hadi Sirika a matsayin sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina. Sakataren gwamnatin jihar Katsina Barista Abdullahi Garba Faskari wanda ya sanya hannu a takardar ya bayyana Hadi Sirika a matsayin mutum mai ƙwarewa da jajircewar a duk muƙaman da ya rike a gwamnati wanda hakan gwamna Dikko Raɗɗa ya ga dacewar sa da muƙamin. Barista Abdullahi Faskari yayi fatan tsohon Ministan zai yi amfani da ƙwarewar sa wajen ciyar…
Read More
KANFEST: Buƙatar mu ƙasashen ƙetare su zuba jari a Jihar Kano — Gwamna Abba

KANFEST: Buƙatar mu ƙasashen ƙetare su zuba jari a Jihar Kano — Gwamna Abba

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa babban burin gudanar da bikin Kano Festival of Arts and Culture (KANFEST) shi ne jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje domin bunƙasa tattalin arzikin jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin rufe shagulgulan KANFEST na tsawon kwanaki uku, a yayin liyafar karramawa da aka shirya wa mahalarta a Fadar Gwamnatin Jihar Kano da yammacin Litinin. Gwamna Yusuf ya buƙaci mahalarta daga ƙasashen waje da su kasance jakadun jihar Kano ta hanyar yaɗa dimbin damar saka hannun jari da jihar ke da su a…
Read More